24-30 ga Maris
KARIN MAGANA 6
Waƙa ta 11 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Wane Darasi Za Mu Koya Daga Cinnaka?
(minti 10)
Za mu iya koyan darussa masu kyau idan muka lura da cinnaku ko kyashi (K. Ma 6:6)
Ko da yake cinnaku ba su da shugaba, duk da haka suna amfani da hikimarsu don su yi aiki tuƙuru, su haɗa kai kuma su yi shiri don nan gaba (K. Ma 6:7, 8; it-1-E 115 sakin layi na 1-2)
Idan kuka yi koyi da cinnaku, za ku amfana (K. Ma 6:9-11; w09 4/15 16 sakin layi na 9-10)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
K. Ma 6:16-19—Shin, abubuwan da aka ambata a waɗannan ayoyin su ne duka zunuban da Jehobah ya tsana ne? (w00-E 9/15 27 sakin layi na 3)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 6:1-26 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci wani danginka da ya daɗe bai zo taro ba don ya zo ya saurari jawabi na musamman da kuma jawabin da za a yi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 4 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nemi dama daga shugaban aikinku don ka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 3 batu na 3)
6. Fara Magana da Mutane
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci mutumin ya zo ya saurari jawabi na musamman da jawabin da za a yi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu. (lmd darasi na 5 batu na 3)
Waƙa ta 2
7. Halittu Suna Nuna Cewa Jehobah Yana So Mu Yi Farin Ciki—Dabbobi Masu Ban Sha’awa
(minti 5) Tattaunawa.
Ku kalli BIDIYON. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Mene ne dabbobi suke koya mana game da Jehobah?
8. Bukatun Ikilisiya
(minti 10)
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) w23.3 4-7 sakin layi na 11-20