28 ga Yuni–4 ga Yuli
MAIMAITAWAR SHARI’A 9-10
Waƙa ta 49 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Mene ne Yahweh Allahnku Yake So a Gare Ku?”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
M.Sh 9:1-3—Me ya sa Isra’ilawa ba sa bukatar su ji tsoron ’ya’yan Anak duk da cewa su “masu tsayi ne ga ƙarfi kuma”? (mwbr21.05-HA an ɗauko daga it-1 103)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) M.Sh 10:1-22 (th darasi na 10)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka ba da ɗaya daga cikin littattafan da muke wa’azi da su. (th darasi na 3)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Ka gabatar da tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? (th darasi na 9)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) fg darasi na 12 sakin layi na 4-5 (th darasi na 18)
RAYUWAR KIRISTA
Kana Amfana Daga Wasannin Bidiyon da Kake Yi?: (minti 7) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Sai ka tambayi masu sauraro: Ta yaya wasannin bidiyo zai iya cutar da kai? Waɗanne abubuwa ne suka fi wasannin bidiyo muhimmanci? (Afi 5:15, 16) Ta yaya wasannin bidiyon da ka zaɓa za su nuna irin halinka? Ta yaya za ka yi nasara ta gaske?
“Ka Mai da Hankali Sa’ad da Kake Zaɓan ko Za Ka Sha Giya ko A’a”: (minti 8) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Ka Yi Tunani da Kyau Kafin Ka Sha Giya.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lfb darasi na 37
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 3 da Addu’a