Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Mai da Hankali Sa’ad da Kake Zaɓan ko Za Ka Sha Giya ko A’a

Ka Mai da Hankali Sa’ad da Kake Zaɓan ko Za Ka Sha Giya ko A’a

Dukan Kiristoci suna bukatar kamun kai idan ya zo ga shan giya. (K. Ma 23:​20, 29-35; 1Ko 6:​9, 10) Idan Kirista yana so ya sha giya, ya sha daidai yadda ba zai bugu ba. Ban da haka, bai kamata ya dogara ga giya kafin ya yi wani abu ba kuma ya guji sa wasu tuntuɓe. (1Ko 10:​23, 24; 1Ti 5:23) Hakika, bai kamata a tilasta wa kowa musamman ma matasa su sha giya ba.

KU KALLI BIDIYON NAN KA YI TUNANI DA KYAU KAFIN KA SHA GIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa dole ne Kiristoci su bi dokar da aka kafa game da shan giya?​—Ro 13:​1-4

  • Me ya sa bai kamata mu bar wasu su tilasta mana mu sha giya ba?​—Ro 6:16

  • Ta yaya za mu guji haɗarin da shan giya ke jawowa?