RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance a Shirye a Ƙarshen “Kwanakin Ƙarshe”
Abubuwa za su yi muni sosai yayin da muke rayuwa a ƙarshen “kwanakin ƙarshe.” (2Ti 3:1; Mt 24:8) A lokacin da bala’i ya abko, bayin Jehobah suna samun umurnin da zai ceci rayukansu a kan lokaci. Za mu iya ceton rayukanmu idan mun kasance da shiri tun yanzu.—Lu 16:10.
-
Ka yi kusa da Allah: Ka riƙa karanta da kuma nazarin Littafin Mai Tsarki. Ka koyi hanyoyin yin wa’azi dabam-dabam. Kada ka ji tsoro idan an ware ka na ɗan lokaci daga ’yan ikilisiyarku. (Ish 30:15) Ka tuna cewa ba za a iya ware ka daga Jehobah da kuma Yesu ba.—od-E 176 sakin layi na 15-17
-
Ka shirya kanka: Ban da jaka ko akwatin gaggawa, kowannenmu zai iya ajiye abinci da ruwa da magani da dai sauransu saboda yanayin gaggawa da zai iya bukaci mutum ya yi zama a wani wuri na ɗan lokaci.—K. Ma 22:3; g17.5-E 4, 6
KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALA’I TA AUKU? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya dangantaka mai kyau da Jehobah za ta taimaka mana sa’ad da bala’i ya abku?
-
Me ya sa yake da muhimmanci mu . . .
-
ba dattawa lambar wayarmu da adireshinmu?
-
kasance da jaka ko akwatin gaggawa?
-
bincika irin bala’in da za su iya aukuwa a yankinmu da matakan da ya kamata mu ɗauka?
-
-
A waɗanne hanyoyi uku ne za mu taimaka ma waɗanda bala’i ya abka musu?
KA TAMBAYI KANKA, ‘Waɗanne darussa ne annobar korona bairus ta koya mana game da kasancewa da shiri?’