RAYUWAR KIRISTA
Muna Gode wa Jehobah don Ƙaunarku
Ikilisiyar da ke Tasalonika sun nuna wa ’yan’uwansu ƙauna duk da cewa suna cikin yanayi mai wuya. (2Ta 1:3, 4) Bayin Jehobah a yau suna nuna wa juna irin wannan ƙaunar a faɗin duniya. Talifofin jw.org masu jigo “Yadda Ake Amfani da Gudummawarka” sun nuna hanyoyin da gudummawarka take taimaka wa ’yan’uwa a mawuyacin yanayi. Muna yaba muku don ƙaunarku da kuma gudummawarku.
KU KALLI BIDIYON NAN MUNA “GODE WA ALLAH SABODA KU,” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
• Me da me ake yi da gudummawarmu?
• A wace hanya mafi kyau ce za mu taimaka wa ’yan’uwanmu da suke bukatar taimako?—Ku kuma duba talifin jw.org mai jigo “Yadda Ake Taimaka wa Masu Bukata”