KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI
Ka Amince da Taimakon Jehobah ta Wurin Yin Addu’a
Jehobah ne yake sa gaskiyar da muke gaya wa mutane ta ratsa zuciyarsu. (1Ko 3:6-9) Don haka, idan muna so mu yi nasara a hidimarmu, wajibi ne mu dogara ga Jehobah ya taimaka mana da kuma ɗalibanmu.
Ka roƙi Jehobah ya taimaka wa ɗalibanka su jimre da matsalolin da suke fuskanta. (Fib 1:9, 10) Ka gaya wa Jehobah ainihin abin da kake so ya yi maka. Ka roƙe shi ya sa ruhu mai tsarki ya ja-goranci tunaninka da ayyukanka. (Lu 11:13) Ka koya wa ɗalibanka yadda za su yi addu’a kuma ka ƙarfafa su su riƙa yin hakan. Ka ambata sunan ɗalibinka yayin da kuke addu’a tare, ko sa’ad da kake addu’a a madadinsa.
KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN AMINCE DA TAIMAKON JEHOBAH—ADDU’A, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Wace matsala ce Anita ta fuskanta sa’ad da take nazari da Rose?
-
Ta yaya 1 Korintiyawa 3:6 ya taimaka wa Anita?
-
Me ya taimaka wa Anita ta warware matsalar da ta fuskanta?