SASHE NA 8
Mece Ce Ma’anar Mutuwar Yesu a Gare Ka?
Yesu ya mutu domin mu rayu. Yohanna 3:16
Kwanaki uku bayan mutuwar Yesu, wasu mata sun ziyarci kabarinsa kuma suka tarar da cewa babu kome a cikinsa. Jehobah ya riga ya ta da Yesu daga matattu.
Daga baya, Yesu ya bayyana ga manzanninsa.
Hakika, Jehobah ya ta da Yesu a matsayin ruhu mai iko, marar mutuwa. Almajiran Yesu sun gan shi sa’ad da yake komawa sama.
Daniyel 7:13, 14
Allah ya ta da Yesu daga matattu kuma ya naɗa shi Sarkin Mulkin Allah.Yesu ya ba da ransa don ya fanshi ’yan Adam. (Matta 20:28) Ta hanyar fansar nan, Allah ya buɗe mana hanyar yin rayuwa har abada.
Jehobah ya naɗa Yesu ya zama Sarki don ya yi mulki bisa duniya. Mutane 144,000 masu aminci da aka ta da daga matattu a duniya ne za su kasance tare da shi a sama. Yesu da mutane 144,000 ne za su zama sarakuna a wannan gwamnati mai adalci na samaniya, wato Mulkin Allah.—Ru’ya ta Yohanna 14:1-3.
Mulkin Allah zai mai da duniya aljanna. Yaƙi, laifi, talauci, da yunwa za su zama labari. Mutane za su kasance da farin ciki sosai.—Zabura 145:16.