Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 55

Ɗan Yaro Ya Bauta Wa Allah

Ɗan Yaro Ya Bauta Wa Allah

SHIN wannan ba kyakkyawan yaro ba ne? Sunansa Sama’ila. Kuma mutumin da ya ɗora masa hannu a kai babban firist ne na Isra’ila, Eli. Wannan kuma baban Sama’ila ne Elkanah da kuma mamarsa Hannatu sun kawo Sama’ila wurin Eli.

Sama’ila yana ɗan shekara huɗu ne ko biyar. Amma zai zauna a nan mazaunin Jehobah da Eli da kuma wasu firistoci. Me ya sa Elkanah da Hannatu za su ba da yaro ƙarami haka kamar Sama’ila ya bauta wa Jehobah a mazauni? Bari mu gani.

Wasu ’yan shekaru kafin wannan Hannatu tana baƙin ciki ƙwarai. Dalili kuwa shi ne ba ta da ɗa, kuma tana bukatar ta sami ɗa sosai. Saboda haka wata rana da Hannatu ta ziyarci mazaunin Jehobah, ta yi addu’a: ‘Ya, Jehobah, kada ka manta da ni! Idan ka ba ni ɗa, na yi alkawari zan ba ka shi ya bauta maka dukan rayuwarsa.’

Jehobah ya yi wa Hannatu alkawari, kuma bayan wasu watanni ta haifi Sama’ila. Hannatu tana ƙaunar ɗanta sosai, kuma ta fara koya masa game da Jehobah sa’ad da yake ƙarami. Ta gaya wa mijinta: ‘Da zarar Sama’ila ya yi ɗan girma da ba zai bukaci a shayar da shi ba, zan kai shi mazauni ya bauta wa Jehobah a can.’

Abin da muka ga Hannatu da Elkanah suke yi ke nan a wannan hoto. Kuma domin iyayen Sama’ila sun koyar da shi da kyau, ya yi farin ciki ya bauta wa Jehobah a tantin Jehobah. Kowace shekara Hannatu da Elkanah suna zuwa bauta a wannan tanti na musamman, kuma su ziyarci ɗansu. Kuma kowace shekara Hannatu tana kawo wa Sama’ila sabuwar riga da ta ɗinka masa.

Da shigewar shekaru, Sama’ila ya ci gaba da bauta wa Jehobah a mazauninsa, kuma Jehobah da mutanen suna ƙaunarsa. Amma ’ya’yan Eli babban firist Hophni da Phinehas ba su da kirki. Suna yin miyagun abubuwa kuma suna sa wasu su yi wa Jehobah rashin biyayya. Ya kamata Eli ya cire su daga aikin firistanci amma bai yi haka ba.

Sama’ila bai ƙyale miyagun abubuwa da suke faruwa a mazauni ya sa ya daina bauta wa Jehobah ba. Amma domin mutanen da suke ƙaunar Jehobah kaɗan ne, ya daɗe Jehobah bai yi magana da kowane mutum ba. Ga abin da ya faru sa’ad da Sama’ila ya yi ɗan girma:

Sama’ila yana cikin barci a mazauni sa’ad da wata murya ta tashe shi. Ya amsa: ‘Ga ni nan.’ Ya tashi ya ruga wurin Eli, ya ce:’Ka kira ni, ga ni nan.’

Amma Eli ya amsa ya ce: ‘Ban kira ka ba; ka koma ka kwanta.’ Sama’ila ya koma ya kwanta.

Sai kuma aka sake kiransa: ‘Sama’ila!’ Sama’ila ya sake rugawa zuwa wurin Eli. ‘Ka kira ni gani nan,’ in ji shi. Amma Eli ya ce: ‘Ban kira ka ba, ɗana. Ka je ka yi kwanciyarka.’ Saboda haka Sama’ila ya koma ya kwanta.

‘Sama’ila!’ muryar ta sake kira na sau uku. Sama’ila ya ruga zuwa wurin Eli. ‘Ga ni nan, hakika ka kira ni wannan karon,’ in ji shi. A yanzu Eli ya sani cewa Jehobah ne yake kiransa. Saboda haka ya gaya wa Sama’ila: ‘Ka koma ka yi kwanciyarka, idan ya sake kiranka, ka ce: “Jehobah, ka yi magana, bawanka yana sauraronka.”’

Abin da Sama’ila ya faɗa ke nan sa’ad da Jehobah ya sake kiransa. Jehobah ya gaya wa Sama’ila cewa zai yi wa Eli da ’ya’yansa horo. Daga baya Hophni da Phinehas suka mutu a yaƙi da Filistiyawa, da Eli ya sami labarin abin da ya faru, sai ya faɗi wuyarsa ta karye shi ma ya mutu. Saboda haka maganar Jehobah ta zama gaskiya.

Sama’ila ya girma ya zama alƙali na ƙarshe a Isra’ila. Sa’ad da ya tsufa, mutanen suka ce masa: ‘Ka zaɓa mana sarki da zai yi sarauta bisanmu.’ Amma Sama’ila ba ya son ya yi haka, domin ainihi Jehobah ne sarkinsu. Amma Jehobah ya gaya masa ya saurari maganarsu.

1 Samuila 1:1-28; 2:11-36; 4:16-18; 8:4-9.