LABARI NA 46
Ganuwar Jericho
ME YA SA ganuwar Jericho take rushewa haka? Kamar wani babban bam ya tashi da su. Amma a wannan zamanin ba su da bam; ba su ma da bindigogi. Wata mu’ujiza ce ta Jehobah! Bari mu ga yadda hakan ya faru.
Ka saurari abin da Jehobah ya gaya wa Joshua: ‘Kai da mayaƙanka za ku zagaya birnin. Ku zagaya birnin sau ɗaya a rana har kwana shida. Ku ɗauki akwatin alkawarin. Firistoci bakwai su shige gabansa kuma su riƙa busa ƙaho.
‘A rana ta bakwai ku zagaya birnin sau bakwai. Sa’an nan sai ku yi busa mai ƙarfi da ƙaho, kuma kowa ya yi kururuwa mai ƙarfi irin na yaƙi. Ganuwar za ta rurrushe!’
Joshua da mutanen suka yi abin da Jehobah ya faɗa. Sa’ad da suke zagayawa, kowa ya yi shiru. Babu wanda ya ce ko uffan ba. Abin da ake ji kawai shi ne ƙarar ƙaho da kuma tafiyar ƙafafuwan mutane. Abokan gaban mutanen Allah a Jericho babu shakka sun tsorata. Ka ga wannan jan igiyar a kan taga? Tagar wacece wannan? Hakika, Rahab ta yi abin da ’yan leƙen asiri biyu suka gaya mata ta yi. Dukan iyalinta suna tare da ita a ciki.
A ƙarshe, a kwana na bakwai, bayan sun zagaya birnin sau bakwai, ƙahuna suka yi ƙara, kuma mayaƙan suka yi kururuwar yaƙi, kuma ganuwar ta faɗi. Sai Joshua ya ce: ‘Ku kashe kowa a cikin birnin kuma ku ƙona shi. Ku ƙone kome. Ku kwashi azurfa, zinariya, tagulla da kuma ƙarfe ku zuba cikin tantin Jehobah.’
Ga ’yan leƙen asiri biyun, Joshua ya ce: ‘Ku shiga cikin gidan Rahab, ku fito da ita da iyalanta waje.’ Rahab da iyalinta sun tsira, kamar yadda ’yan leƙen asirin suka yi mata alkawari.
Joshua 6:1-25.