Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 4

Daga Sarkin Isra’ila na Farko Zuwa Bauta a Babila

Daga Sarkin Isra’ila na Farko Zuwa Bauta a Babila

Saul ya zama sarkin farko na Isra’ila. Amma Jehobah ya ƙi shi, kuma ya zaɓi Dauda ya zama sarki a maimakonsa. Za mu fahimci abubuwa masu yawa game da Dauda. Sa’ad da yake saurayi ya yaƙi ƙaton nan Goliath. Daga baya ya guje wa Sarki Saul da ya cika da kishi. Sai kuma Abigail ta hana shi yin wauta.

A gaba kuma, za mu koyi abubuwa da yawa game da Sulemanu ɗan Dauda, wanda ya gaji sarautar Isra’ila daga hannun Dauda. Sarakuna uku na farko na Isra’ila kowannen su ya yi sarauta na shekaru 40. Bayan mutuwar Sulemanu, aka raba masarautar Isra’ila gida biyu, masarautar arewa da ta kudu.

Masarautar arewa mai ƙabilu 10 ta yi shekara 257 kafin Assuriyawa suka halakata. Bayan shekara 133 kuma, aka halaka masarautar kudu mai ƙabilu biyu. A wannan lokacin aka kwashi Isra’ilawa zuwa bauta a Babila. Saboda haka Sashe na HUƊU ya ba da tarihin shekaru 510, a wannan lokacin abubuwa masu muhimmanci sun faru.