LABARI NA 26
Ayuba Mai Aminci Ne Ga Allah
KANA tausayin wannan mutumin majiyyaci? Wannan mutumin Ayuba ne, da kuma matarsa. Ka san abin da take gaya wa Ayuba? ‘Ka la’anci Allah ka mutu.’ Bari mu ga abin da ya sa ta faɗi irin wannan maganar, da abin da ya sa kuma Ayuba yake wahala haka.
Ayuba mutum ne mai aminci da yake yi wa Jehobah biyayya. Yana da zama a ƙasar Uz, ba ta da nisa da ƙasar Kan’ana. Jehobah yana ƙaunar Ayuba ƙwarai, amma da akwai wanda ba ya sonsa. Ka san ko wanene ne wannan?
Shaiɗan ne Iblis. Ka tuna cewa Shaiɗan mugun mala’ikan nan ne da ya ƙi Jehobah. Ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi wa Jehobah rashin biyayya, kuma yana tunanin cewa zai iya sa kowa ya yi wa Jehobah rashin biyayya. Amma ya iya yin haka ne? A’a. Ka yi tunanin mutane da yawa maza da mata masu aminci da muka koya game da su. Guda nawa za ka iya kiran sunansu?
Bayan mutuwar Yakubu da Yusufu a ƙasar Masar, Ayuba ne mutumin da ya fi kowa aminci ga Jehobah a lokacin a dukan duniya. Jehobah yana so ya sanar da Shaiɗan cewa ba zai iya sa kowa ya zama mugu ba, saboda haka ya ce: ‘Ga Ayuba. Ka ga yadda yake da aminci a gare ni.’
Shaiɗan ya ce: ‘Yana da aminci a gare ka domin ka yi masa albarka yana da abubuwa masu kyau da yawa. Amma, idan ka kawar da waɗannan zai la’ance ka.’
Saboda haka Jehobah ya ce: ‘Je ka, ka ɗauke masa dukan abubuwan da yake da su. Ka yi wa Ayuba dukan mugunta da ka ga dama. Za mu gani ko zai la’ance ni. Amma ka tabbata ba ka kashe shi ba.’
Da farko Shaiɗan ya sa mutane suka sace shanu da raƙuman Ayuba, kuma suka kashe tumakinsa. Sai kuma ya kashe ’ya’yan Ayuba maza da mata 10 a cikin hadari. Sai kuma ya harbe shi da wata irin cuta mai tsanani. Ayuba ya sha wuya ƙwarai. Abin da ya sa ke nan matar Ayuba ta gaya masa: ‘Ka la’anci Allah ka mutu.’ Amma Ayuba ya ƙi ya yi haka. Kuma abokansa uku na ƙarya suka gaya masa cewa ya yi muguwar rayuwa. Amma Ayuba ya kasance da aminci.
Wannan ya sa Jehobah ya yi farin ciki ƙwarai, kuma daga baya ya albarkaci Ayuba, kamar yadda kake gani a wannan hoton. Ya warkar masa da cutarsa. Kuma Ayuba ya sake haifan ’ya’ya kyawawa 10, ya sami shanu ninki biyu, da tumaki da raƙuma.
Za ka so ka kasance da aminci ga Jehobah kamar yadda Ayuba ya yi? Idan ka yi haka Allah zai yi maka albarka kai ma. Za ka iya rayuwa har abada sa’ad da aka mai da dukan duniya ta yi kyau kamar lambun Aidan.
Ayuba 1:1-22; 2:1-13; 42:10-17.