LABARI NA 93
Yesu Ya Ciyar Da Mutane Masu Yawa
WANI mummunan abu ya faru. An kashe Yohanna mai Baftisma. Hirudiya matar sarki, ba ta ƙaunarsa. Sai ta sa sarkin ya fille kan Yohanna.
Sa’ad da Yesu ya sami labari, ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ya tafi wajen da ba kowa shi kaɗai. Amma mutanen suka bi shi. Sa’ad da Yesu ya ga jama’ar, ya ji tausayinsu. Saboda haka ya koyar da su game da mulkin Allah, kuma ya warkar da marasa lafiya.
Da maraice almajiransa suka zo wurinsa suka ce: ‘Yamma ta riga ta yi, kuma wannan wajen babu kowa. Ka sallami mutanen nan saboda su je su saya wa kansu abinci a ƙauyuka na kusa.’
‘Ba za su ko’ina ba,’ in ji Yesu. ‘Ku ba su abin da za su ci.’ Yesu ya juya ga Filibbus ya tambaya: ‘A ina ne za mu sayi isashen abin da zai ishe dukan waɗannan mutane?’
‘Sai da kuɗi mai yawa za a sayi abinci da kowa a nan zai sami ɗan kaɗan,’ in ji Filibbus. Andarawus ya ce: ‘Wannan yaron da yake ɗauke da abincinmu, yana da burodi biyar da kifi guda biyu. Amma ba zai ishe dukan waɗannan mutane ba.’
‘Ku gaya wa dukan mutanen su zauna a kan ciyawa,’ in ji Yesu. Sai ya yi wa Allah godiya domin abincin, kuma ya fara rarraba su ƙanana ƙanana. Sai almajiran suka ba mutanen dukan burodin da kifin. Wajen maza 5,000 ne, da kuma wasu mata da yara dubbai. Dukansu suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka tattara abin da aka ci aka bari, kuma suka cika kwanduna 12!
Yesu ya sa almajiransa suka shiga cikin kwalekwale domin su haye Tekun Galili. A cikin dare aka yi wani hadari mai ƙarfi, igiyar ruwa tana ta jijjiga jirgin. Almajiran suka tsorata. Sai da tsakar dare, suka ga wani yana zuwa wurinsu a kan ruwa. Suka yi kuka don tsoro, ba su san abin da suke gani ba.
‘Kada ku ji tsoro,’ in ji Yesu. ‘Ni ne!’ Duk da haka ba su yarda ba. Saboda haka Bitrus ya ce: ‘Idan kai ne da gaske, Ubangiji, ka gaya mini in yi tafiya a kan ruwa in zo gare ka.’ Yesu ya amsa: ‘Ka zo!’ Sai Bitrus ya fita ya fara tafiya a kan ruwa! Sai ya tsorata ya fara nitsewa, amma Yesu ya cece shi.
Daga baya Yesu ya sake ciyar da dubban mutane. A wannan lokaci ya yi haka ne da burodi bakwai da kuma ’yan ƙananan kifi kaɗan. Amma kuma kowa ya ci ya ƙoshi. Ba abin farin ciki ba ne yadda Yesu yake kula da mutane? Sa’ad da ya fara mulki a mulkin Allah ba za mu sake damuwa ba domin muna bukatar wani abu!
Matta 14:1-32; 15:29-38; Yohanna 6:1-21.