DARASI NA 17
Ka Zama Aboki na Kwarai Idan Kana So Ka Sami Abokai na Kwarai
Abota ta dangana bisa ƙauna. Idan ka ci gaba da koya game da Jehobah, za ka daɗa ƙaunar sa. Kuma idan kana ƙaunar Allah sosai, za ka daɗa sha’awar bauta masa. Wannan zai motsa ka ka zama almajirin Yesu Kristi. (Matta 28:19) Idan ka zama Mashaidin Jehobah, za ka iya zama aminin Allah har abada. Mene ya zama dole ka yi?
Dole ka nuna cewa kana ƙaunar Allah ta wajen bin dokokinsa. “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 Yohanna 5:3.
Ka yi amfani da abin da ka koya. Yesu ya ba da labari wanda ya nuna wannan. Mutum mai hikima ya gina gidansa a kan dutse. Wawan mutum ya gina gidansa a kan yashi. Da aka yi guguwa, gidan da aka gina a kan dutse bai faɗi ba, amma gidan da aka gina a kan yashi ya rushe. Yesu ya ce waɗanda suka saurari koyarwarsa kuma suka bi abin da suka ji, suna kama da mutumin nan mai hikima da ya gina gida a kan dutse. Amma waɗanda suka saurari koyarwarsa kuma ba su yi su ba, suna kama da wawan mutumin nan da ya gina gida a kan yashi. Wane irin mutum kake so ka zama?—Matta 7:24-27.
Matta 11:29.
Keɓe kai. Wannan yana nufin cewa za ka gaya wa Jehobah a cikin addu’a cewa kana so ka yi nufinsa har abada. Yin nufin Allah zai nuna cewa kai almajirin Yesu Kristi ne.—Baftisma. “Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.”—Ayyukan Manzanni 22:16.
Ka yi wa Allah hidima da dukan zuciyarka. “Iyakar abin da kuke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji, ba ga mutane ba.”—Kolosiyawa 3:23.