Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 14

Aminan Allah Suna Guje Ma Abin da Ba Shi da Kyau

Aminan Allah Suna Guje Ma Abin da Ba Shi da Kyau

Shaiɗan yana jarabtar mutane su yi abubuwan da ba su da kyau. Mutumin da yake son ya zama aminin Allah yana bukatar ya tsane abin da Jehobah ya tsana. (Zabura 97:10) Ga wasu abubuwa da aminan Allah suka tsana:

Lalata da zina. “Ba za ka yi zina ba.” (Fitowa 20:14) Ƙari ga haka, yin jima’i kafin aure zunubi ne.—1 Korintiyawa 6:18.

Yin maye. “Masu-maye . . . ba za su gāji mulkin Allah ba.”—1 Korintiyawa 6:10.

Kisan kai, zubar da ciki. “Ba za ka yi kisan kai ba.”—Fitowa 20:13.

Sata. “Ba za ka yi sata ba.”—Fitowa 20:15.

Ƙarya. Jehobah ba ya son “harshe mai-ƙarya.”—Misalai 6:17.

Yawan fushi da kuma mugunta. “Mai-mugunta da mai-son zalunci ransa [Jehobah] yana ƙinsu.” (Zabura 11:5) “Ayyukan jiki [sun haɗa da] . . . hasala.”—Galatiyawa 5:19, 20.

Caca. ‘Kada ku yi tarayya da mutum . . . mai-kwaɗayi.’—1 Korintiyawa 5:11.

Ƙiyayya saboda launin fata ko ƙabila. “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta maku, ku yi masu addu’a.”—Matta 5:43, 44.

Abubuwan da Allah ya gaya mana don amfanin kanmu ne. Ba kowane lokaci ba ne yake da sauƙi mu ƙi abubuwan da ba su da kyau. Da taimakon Jehobah da kuma na Shaidunsa, za mu iya ƙin abubuwan da suke ɓata wa Allah rai.—Ishaya 48:17; Filibiyawa 4:13; Ibraniyawa 10:24, 25.