Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 18

Ka Zama Aminin Allah Har Abada!

Ka Zama Aminin Allah Har Abada!

Bai da sauƙi a sami abokin ƙwarai; kuma bai da sauƙi a ci gaba da abokantaka bayan an ƙulla ta. Idan kana ƙoƙartawa ka zama aminin Allah, za ka sami albarka sosai. Yesu ya ce game da waɗanda suke gaskata shi: “Gaskiya kuwa za ta ’yantar da ku.” (Yohanna 8:32) Mene ne wannan yake nufi?

Za ka more ’yanci yanzu. Za ka ’yantu daga koyarwan ƙarya da kuma ƙaryace-ƙaryace da Shaiɗan yake yaɗawa. Rayuwarka za ta kasance da ma’ana kuma za ka fita dabam da sauran mutane da ba su san Jehobah ba. (Romawa 8:22) Ba za ka ji tsoron matattu ba domin aminan Allah ba sa “tsoron matattu.”—Ibraniyawa 2:14, 15.

Za ka more ’yanci a sabuwar duniya ta Allah. Za ka more kyakkyawan ’yanci kuwa a nan gaba! A cikin Aljanna, ba za a yi yaƙi ko ciwo ko aikata laifi ba. Babu talauci da kuma yunwa. Babu tsufa da kuma mutuwa. Babu tsoro, zalunci, da kuma rashin adalci. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Allah: “Kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai rai muradinsa.”—Zabura 145:16.

Aminan Allah za su rayu har abada. Madawwamin rai kyauta ce da Allah zai ba wa dukan waɗanda suka zama aminansa. (Romawa 6:23) Ka yi tunanin yadda rayuwa har abada za ta kasance!

Za ka sami lokacin yin abubuwa da yawa. Wataƙila kana so ka koyi yin kiɗa ko zane-zane ko saƙa ko kana so ka koyi wasu abubuwa game da dabbobi ko itatuwa. Idan yin tafiya zuwa wurare dabam-dabam ne kake so ka yi ma za ka iya yin hakan. Yin rayuwa har abada zai ba ka damar yin dukan waɗannan abubuwan!

Za ka sami lokacin yin abokane da yawa. Rayuwa har abada za ta sa ka san mutane da yawa waɗanda suka zama aminan Allah. Za ka zo ga fahimtar iyawarsu da kuma halayensu masu kyau, su ma za su zama aminanka. Za ka ƙaunace su, su ma za su ƙaunace ka. (1 Korintiyawa 13:8) Samun rai na har abada zai ba ka damar yin abokantaka da kowa da ke raye! Amma abu mafi muhimmanci shi ne, dangantakarka da Allah za ta daɗa danƙo yayin da lokaci yake shigewa. Bari ka zama aminin Allah har abada!