SASHE NA 3
Shawara Mai Amfani da ke Kyautata Rayuka
A CE wani sabon likita ya tare a unguwarku. Wataƙila da farko kana ɗan yin shakkar ko shi ƙwararren likita ne. Amma idan wasu daga cikin abokanka suka nemi taimakonsa kuma suka samu lafiya nan da nan fa? Ba za ka yi tunanin ganin likitan ba?
A wasu hanyoyi, Nassosi Masu Tsarki suna kama ne da wannan likitan. Wasu mutane suna shakkar bincika su. Amma sa’ad da suka yi amfani da shawara mai kyau da ke cikinsu, hakan yana sa rayuwarsu ta kasance da ma’ana. Ga wasu misalai.
Magance Matsalolin Aure
“A farkon aurenmu, na yi tunanin cewa maigidana, Dumas, ba ya kula da ni,” in ji Sumiatun. “Ina yawan yi masa ruwan zagi saboda taƙaici, in jefe shi da abubuwa, har da bugu. Akwai lokatan da na yi fushi sosai, har na suma.
“Sa’ad da Dumas ya soma nazarin Nassosi Masu Tsarki, na yi masa ba’a. Amma a ɓoye, nakan saurari nazarin da yake yi daga ɗakin da nike. Wata rana, na ji yana karanta wasu ayoyi: ‘Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji . . . Mata kuma ta ga ƙwarjinin Mijinta.’ (Afisawa 5:22, 23) Waɗannan kalaman sun taɓa zuciyata. Na roƙi Allah ya gafarta mini domin zagin da nake yi wa mijina, kuma na roƙe Shi ya taimake ni in zama matar kirki. Ba da daɗewa ba, ni da Dumas muka soma nazarin Nassosi tare.”
Nassosi Masu Tsarki sun ce: “Haka nan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu.” (Afisawa 5:28) Sumiatun ta ce: “Waɗannan abubuwan da muka koya ya taɓa mu. Sai na soma ba Dumas kofin shayi idan ya dawo gida daga wurin aiki kuma na soma yi masa magana yadda ya kamata. Saboda haka, Dumas ya ƙara nuna mini ƙauna kuma ya taimaka mini a aikace-aikace na gida. Mu biyun mun yi ƙoƙarin ‘kasancewa da nasiha zuwa ga junanmu, masu taushin zuciya, muna yi wa junanmu gafara.’ (Afisawa 4:32) Hakan ya zurfafa ƙauna da darajar da muke nuna wa juna sosai. A yanzu mun yi shekaru fiye 40 da yin aure kuma muna cike da farin ciki. Shawara mai kyau da ke cikin Kalmar Allah ce ta ceci aurenmu!”
Kame Fushi
“Ni mutumi ne mai zafin rai a dā,” in ji Tayib. “Ina yawan yin faɗa kuma na sha tsorata mutane da bindiga. Ina bugun matata, Kustriyah, kuma in buga ta da ƙasa cikin fushi. Mutane da yawa suna jin tsoro na.
“Akwai ranar da na karanta kalmomin Yesu: ‘Sabuwar doka na ke baku, ku yi ƙaunar juna, kamar yadda ni na ƙaunace ku.’ (Yohanna 13:34) Hakan ya taɓa ni sosai, kuma na ƙudurta cewa zan canja halina. Idan na soma fushi, ina roƙon Allah ya taimake ni in kame kaina. Ba da jimawa ba na rage zafin rai. Ni da matata mun yi amfani da shawarar da ke Afisawa 4:26, 27: ‘Kada rana ta faɗi kuna kan fushinku, kada kuwa ku ba Shaitan dama.’ A kowane dare, muna karanta Nassosi kuma mu yi addu’a tare. Hakan yana kawar da dukan matsalolin da muka fuskanta a ranar kuma yana jawo mu kusa da juna.
“A yanzu an san ni a matsayin mutum mai son zaman lafiya. Matata da yarana suna ƙaunata kuma suna daraja ni. Ina da abokai da dama, kuma na kusaci Allah sosai. Ni mutumi ne mai farin ciki sosai.”
Daina Shan Ƙwayoyi Masu sa Maye
“Na yi tarayya da matasa ’yan daba, a dā ni mugun mashayin taba ne, kuma ina yawan buguwa da giya, in faɗi, kuma in kwana a kan titi,” in ji Goin. “Ina sha da kuma sayar da ƙwayoyi masu sa maye, kamar su taba wi-wi da hodar Iblis, waɗanda nake ɓoye wa a ƙarƙashin rigar kāre harsashi. Ko da yake da ka gan ni ka ga abin tsoro kuma ba na rage wa kowa, a kullum ina cikin fargaba.
“Sai wani ya nuna mini wannan nassin: ‘Ɗana kada ka manta da koyarwata . . . gama za su ƙara maka tsawon kwanaki, da shekaru na rai, da salama kuma.’ (Misalai 3:1, 2) Ina begen samun dogon rai da ke cike da kwanciyar hankali! Kuma na karanta: ‘Da yake fa, ƙaunatattu, muna da waɗannan alƙawarai, bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazantar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.’ (2 Korintiyawa 7:1) Sai na daina shan ƙwaya, na daina tarayya da ’yan daba, kuma na fara bauta wa Allah.
“A yanzu na yi shekaru fiye da 17 da daina shan duk wata muguwar ƙwaya. Ina more ƙoshin lafiya, iyali mai farin ciki, abokan kirki, da lamiri mai kyau. Maimakon in riƙa kwana a buge a kan titi, ina barci a kan gadona cike da kwanciyar hankali a kowace rana.”
Cin Nasara a Kan Nuna Bambancin Launin Fata
“Ni mai aikata laifi ne sa’ad da nake matashi,” in ji Bambang, “kuma yawancin mutanen da suka faɗa tarkona wasu ’yan ƙabila ce da na ƙi jinin su.
“Da shigewar lokaci, sai na fara biɗan Allah. Yin haka ya sa na sadu da wani rukuni da ke nazarin Nassosi Masu Tsarki. A nan ne mutanen ƙabilar nan da na ƙi jininsu suka gai da ni sosai! Na kuma lura cewa a tsakanin wannan rukunin nazarin, ƙabilu dabam-dabam suna yin cuɗanya da juna a sake kuma da farin ciki. Hakan ya ba ni mamaki! A lokacin ne na fahimci nassin nan da ya ce: ‘Allah ba mai tara ba ne, amma a cikin kowace al’umma wanda yake tsoron sa, yana aika adalci kuma, abin karɓe ne a gare shi.’—Ayyukan Manzanni 10:34-35.
“A yau, na daina nuna wariya. Wasu daga cikin abokai na na kud da kud ’yan ƙabilar nan ne da na ƙi jininsu a dā. Allah ya koya mini ƙauna ta hanyar Nassosi Masu Tsarki.”
Yin Watsi da Halin Nuna Ƙarfi
“Sa’ad da nake matashi, an ɗaure ni a kurkuku sau uku—sau biyu don na yi sata kuma ɗayan domin na soki wani mutum ne da wuƙa,” in ji Garoga. “Daga baya, na shiga ƙungiyar ’yan tawaye kuma na kashe mutane da yawa. Bayan an daina tarzomar, sai na zama shugaban wasu ’yan daba da suke ƙwace kuɗi daga hannun mutane kuma su nemi bayani daga wurinsu
ta wajen razanar da su. Ina da ’yan tsaro da ke bi na zuwa duk inda za ni. Kuma na zama abin tsoro ga mutane.“Wata rana, na karanta wannan nassin: ‘Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura.’ (1 Korintiyawa 13:4, 5) Waɗannan kalaman sun taɓa zuciya ta. Na ƙaura zuwa wani wuri dabam, na yi nazarin nassosi, kuma na yi amfani da shawarar da ke cikinsu a rayuwata.
“A yanzu dai na daina nuna ƙarfi. Akasin haka, mutane suna daraja ni a matsayin mai koyar da Kalmar Allah. Rayuwata ta sami manufa da ma’ana mai kyau.”
Kalmar Allah Tana da Iko
Waɗannan labaran da wasu masu yawa sun tabbatar da cewa “maganar Allah mai-rai ce, mai aikatawa.” (Ibraniyawa 4:12) Shawararta tana da sauƙi, tana da amfani, kuma tana ban ƙarfafa.
Nassosi Masu Tsarki za su iya taimaka maka kuwa? Ƙwarai kuwa, za su iya taimaka maka, ko da wace irin matsala ce kake fuskanta. “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.”—2 Timothawus 3:16, 17.
Saboda haka, bari mu bincika wasu muhimman koyarwa da ke cikin Nassiso Masu Tsarki.