BABI NA 15
Ka Ji Dadin Aikin da Kake Yi
“Kowane mutum . . . ya ji wa ransa daɗi cikin dukan aikinsa.”—MAI-WA’AZI 3:13.
1-3. (a) Yaya mutane da yawa suke ji game da aikinsu? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a babin nan?
MUTANE a faɗin duniya suna aiki sosai don su sami abin biyan bukatarsu da na iyalansu. Da yawa a cikinsu ba sa son aikinsu, wasu kuma gabansu yana faɗuwa a duk lokacin da suke zuwa aiki. Idan haka yanayinka yake, me za ka yi don ka ji daɗin aikinka? Ta yaya za ka ji daɗin aikin da kake yi?
2 Jehobah ya ce: “Kowane mutum ya ci ya sha, ya ji wa ransa daɗi cikin dukan aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.” (Mai-Wa’azi 3:13) Jehobah ya halicce mu da sha’awar yin aiki. Yana so mu ji daɗin aikin da muke yi.—Karanta Mai-Wa’azi 2:24; 5:18.
3 Saboda haka, me zai taimaka mana mu ji daɗin aikin da muke yi? Waɗanne irin ayyuka ne bai kamata Kirista ya yi ba? Ta yaya za mu daidaita yadda muke aiki don mu sami lokacin bauta ma Jehobah? Wane aiki mai muhimmanci ne za mu yi?
MA’AIKATA BIYU DA SUKA FI KOWA AIKI
4, 5. Wane ra’ayi ne Jehobah yake da shi game da aiki?
4 Jehobah da kansa yana jin daɗin yin aiki. Farawa 1:1 ta ce: “Da farko Allah ya halicci sammai da kuma duniya.” (New World Translation) Bayan da Allah ya gama halittar duniya da kome da ke cikinta, sai ya ce duk abin ya yi na da “kyau sosai.” (Farawa 1:31) Mahaliccinmu ya so abubuwan da ya halitta.—1 Timoti 1:11.
5 Jehobah bai daina aiki ba. Yesu ya ce: “Ubana yana aiki har yanzu.” (Yohanna 5:17) Ko da yake ba mu san dukan ayyukan da Jehobah yake yi ba, amma mun san wasu daga cikinsu. Yana zaɓan waɗanda za su yi sarauta tare da Ɗansa Yesu Kristi a sama. (2 Korintiyawa 5:17) Har ila yana ja-gorar ’yan Adam da kuma kula da su. A sakamakon wa’azi da ake yi, miliyoyin mutane suna sanin gaskiya game da Jehobah kuma suna begen yin rayuwa a aljanna.—Yohanna 6:44; Romawa 6:23.
6, 7. Wane irin ma’aikaci ne Yesu?
6 Yesu yana son yin aiki kamar Ubansa Jehobah. Kafin Yesu ya zo duniya, shi “gwanin” mai aiki ne da ya yi aiki tare da Allah wajen halittar abubuwan da ke sama da kuma duniya. (Misalai 8:22-31; Kolosiyawa 1:15-17) A lokacin da Yesu yake duniya, ya yi aiki sosai. A lokacin da yake matashi, ya ƙware a aikin kafinta, mai yiwuwa ya yi aiki sosai wajen yin rufin ɗaki da gyara kofofi da yin kujeru da kuma tebura. Ya iya aikinsa sosai shi ya sa mutane suke kiransa ‘kafinta.’—Markus 6:3.
7 Duk da haka, aikin da ya fi muhimmanci a wurin Yesu shi ne wa’azi da koyar da mutane game da Jehobah. Da yake ya so ya gama wa’azinsa a cikin shekaru uku da rabi, ya yi aiki sosai daga safe har dare. (Luka 21:37, 38; Yohanna 3:2) Yesu ya je wurare masu nisa kuma ya bi hanyoyi marasa kyau don ya yi wa mutane da yawa wa’azin bishara.—Luka 8:1.
8, 9. Me ya sa Yesu ya ji daɗin aikinsa?
Yohanna 4:31-38) Ya yi amfani da duk damar da ya samu don ya koyar da mutane game da Ubansa. Shi ya sa ya gaya ma Jehobah cewa: “Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin cika dukan aikin da ka ba ni in yi.”—Yohanna 17:4.
8 Yesu ya ɗauki yin aikin Allah kamar abinci. Wannan aikin ya ba shi ƙarfi da kuzari. Akwai lokutan da Yesu ya yi aiki sosai har ma bai ci abinci ba don aikin. (9 A bayyane yake cewa Jehobah da Yesu sun yi aiki sosai kuma sun ji daɗin aikin da suka yi. Mu ma muna so mu bi ‘misalin’ Allah kuma mu bi ‘gurbin’ Yesu da kyau. (Afisawa 5:1; 1 Bitrus 2:21) Shi ya sa muke aiki sosai kuma muke iya ƙoƙarinmu a duk wani abin da muke yi.
YAYA YA KAMATA MU ƊAUKI AIKIN DA MUKE YI?
10, 11. Me zai taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau game da aikin da muke yi?
10 Mu bayin Jehobah muna aiki sosai don mu biya bukatunmu da na iyalinmu. Ya kamata mu riƙa son aikin da muke yi, amma hakan bai da sauƙi a wasu lokuta. Saboda haka, me za mu yi don mu ji daɗin aikin da muke yi?
11 Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Mai yiwuwa ba za mu iya canja inda muke aiki ko yawan aikin da muke yi ba, amma za mu iya canja ra’ayinmu. Idan muka fahimci abin da Jehobah yake bukata a gare mu, zai taimaka mana. Alal misali: Jehobah yana bukatar maigida ya yi iya ƙoƙarinsa wajen biyan bukatun iyalinsa. Littafi Mai Tsarki ya ce wanda ya kasa kula da 1 Timoti 5:8) Idan kai magidanci ne, ka yi ƙoƙari ka kula da iyalinka. Ko da kana son aikinka ko a’a, ka san cewa idan ka biya bukatun iyalinka, kana faranta ran Jehobah.
iyalinsa ya fi “marar ba da gaskiya muni.” (12. Ta yaya za mu amfana idan muna aiki sosai kuma muna faɗin gaskiya?
12 Ka zama mai ƙwazo a aiki kuma ka yi gaskiya. Hakan zai sa ka ji daɗin aikin da kake yi. (Karin Magana 12:24; 22:29) Ban da haka ma, wanda ya ɗauke ka aiki zai yarda da kai. Masu ɗaukan mutane a aiki suna yarda da ma’aikatan da suke gaskiya, waɗanda ba sa sata kuɗi ko kayayyaki ko kuma lokacin maigidansu. (Afisawa 4:28) Abu mafi muhimmanci kuma shi ne Jehobah zai sani in kana aiki sosai kuma kana faɗin gaskiya. Ƙari ga haka, ‘tunanin zuciyarmu ba za ta dame mu game da wani laifi’ ba.—Ibraniyawa 13:18; Kolosiyawa 3:22-23.
13. Wane amfani kuma za mu samu idan muka yi gaskiya a wurin aiki?
13 Ka san cewa halinka a wurin aiki zai iya sa a ɗaukaka Jehobah. Hakan zai iya sa mu ji daɗin aikin da muke yi. (Titus 2:9, 10) Wani da kuke aiki tare zai iya ce a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi domin halinka mai kyau.—Karanta Karin Magana 27:11; 1 Bitrus 2:12.
WANE IRIN AIKI ZAN YI?
14-16. Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke zaɓan aikin da za mu yi?
14 Littafi Mai Tsarki bai ba mu jerin ayyukan da Kirista zai yi da waɗanda bai kamata ya yi ba. Amma yana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka mana mu Karin Magana 2:6) Mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki mu yi ma kanmu tambayoyi na gaba.
yanke shawara mai kyau sa’ad da muke zaɓan aiki. (15 Wannan aikin zai sa in yi wani abu da Jehobah ya tsana? Mun koyi wasu abubuwan da Jehobah ba ya so kamar su sata da kuma ƙarya. (Fitowa 20:4; Ayyukan Manzanni 15:29; Afisawa 4:28; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:8) Saboda haka, zai dace mu guji duk wani aikin da zai sa mu kasa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.—Karanta 1 Yohanna 5:3.
Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:4.
16 Shin wannan aikin yana goyon bayan wani abu da Jehobah ba ya so? Alal misali, za ka amince ka yi aiki a kamfanin gini da suke gina coci? Yin aikin gini ba laifi ba ne. Amma ka san cewa Allah ya tsani koyarwar ƙarya da ake yi a coci. Saboda haka, ko da yake ba kai ne mai koyar da ƙaryar ba, amma ba ka ganin Jehobah zai yi fushi in ka sa hannu a gina cocin?—17. Me zai taimaka mana mu yanke shawarar da za ta faranta ran Jehobah?
17 Idan muna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, za mu zama kamar mutanen da aka kwatanta a Ibraniyawa 5:14, cewa suna “ƙoƙarin yin amfani da hankalinsu kullum, har ma suna iya bambanta nagarta da mugunta.” Saboda haka, za mu iya tambayar kanmu: ‘Idan na karɓi aikin nan, hakan zai iya sa wasu su yi tuntuɓe? Shin wannan aikin zai sa in bar iyalina kuma in yi nesa da su ko ma in je wata ƙasa? Ta yaya hakan zai shafe su?’
KU ZAƁI “ABIN DA YA FI KYAU”
18. Me ya sa zai iya mana wuya mu ɗauki ayyukan ibada da muhimmanci fiye da kome?
18 Zai iya mana wuya mu sa ayyukan ibada farko a rayuwarmu domin Littafi Mai Tsarki ya ce “a kwanakin ƙarshe za a sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Samun aikin da za mu ci gaba da yi ba abu mai sauƙi ba ne. Muna so mu kula da iyalinmu, amma mun san cewa abu mafi muhimmanci shi ne bautarmu ga Jehobah. Bai kamata mu riƙa yawan son abin duniya ba. (1 Timoti 6:9, 10) To me zai taimaka mana mu “iya zaɓar abin da ya fi kyau” kuma mu biya bukatun iyalinmu?—Filibiyawa 1:10.
19. Ta yaya dogara ga Jehobah zai sa mu kasance da ra’ayin da ya dace game da aikinmu?
Karin Magana 3:5, 6.) Mun san cewa Allah ya san duk bukatunmu kuma yana ƙaunar mu. (Zabura 37:25; 1 Bitrus 5:7) Kalmarsa ta ce: “Ku yi nesa da halin son kuɗi, ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi. Ga shi kuwa Allah ya ce, ‘Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.’ ” (Ibraniyawa 13:5) Jehobah ba ya so mu riƙa yawan damuwa a kan biyan bukatun iyalinmu. Sau da dama, ya nuna cewa zai iya biyan bukatun bayinsa. (Matiyu 6:25-32) Ko da wane irin aiki muke yi, za mu ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah a kullum da yin wa’azi da kuma halartar taro.—Matiyu 24:14; Ibraniyawa 10:24, 25.
19 Ka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka. (Karanta20. Ta yaya za mu sauƙaƙa rayuwarmu?
20 Kada ka zama mai rawan ido. (Karanta Matiyu 6:22, 23.) Hakan yana nufin cewa mu sauƙaƙa rayuwarmu don mu mai da hankali ga bauta wa Jehobah. Mun san cewa wauta ce mu so kuɗi ko jin daɗin rayuwa ko kuma kayan zamani fiye da dangantakarmu da Jehobah. Amma me zai taimaka mana mu mai da hankali ga abin da ya fi kyau? Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji cin bashi. Idan kuma ana bin ka bashi, ka shirya yadda za ka rage yawan bashin ko kuma ka biya gabaki ɗaya. Idan ba mu yi hankali ba, abubuwan duniya za su ɗauke hankalinmu gabaki ɗaya kuma ba za mu samu lokacin yin addu’a ko nazarin Littafi Mai Tsarki ko kuma wa’azi ba. A maimakon barin abubuwan duniya su sa mu cikin damuwa, ya dace mu haƙura da abubuwan da muke bukata kamar “abinci da rigunan sawa.” (1 Timoti 6:8) Ko da yaya yanayinmu yake, yana da kyau a wasu lokuta mu bincika yanayinmu don mu ga yadda za mu ƙara ƙwazo a bautar Jehobah.
21. Me ya sa muke bukatar mu yanke shawara a kan abin da ya kamata mu saka farko a rayuwarmu?
21 Ka sa abubuwan da suka fi muhimmanci farko a rayuwarka. Muna bukatar mu yi amfani da lokacinmu da ƙarfinmu da kuma abubuwan da muka mallaka a hanyar da ta dace. Idan ba mu mai da hankali ba, abubuwa marasa muhimmanci kamar neman ilimi ko Matiyu 6:33) Shawarar da muke yankewa da halinmu da abubuwan da muka saba yi da kuma makasudanmu za su nuna abin da muka sa a gaba.
kuɗi za su iya cin lokacin da za mu yi amfani da shi don yin abubuwa masu muhimmanci. Yesu ya ce: “Muhimmin abu na farko shi ne ku miƙa kanku ga al’amuran mulkinsa.” (AIKI MAFI MUHIMMANCI DA ZA MU YI
22, 23. (a) Wane aiki mafi muhimmanci ne Kiristoci suke da shi? (b) Me zai taimaka mana mu ji daɗin aikin da muke yi?
22 Aiki mafi muhimmanci da za mu yi shi ne bauta wa Jehobah kuma mu riƙa yin wa’azi. (Matiyu 24:14; 28:19, 20) Mu ma muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yin wannan aikin kamar yadda Yesu ya yi. Wasu sun ƙaura don su yi wa’azi a wuraren da ake bukatar masu wa’azi. Wasu kuma suna koyan sabon yare don su yi wa mutanen da suke jin yaren wa’azi. Ka nemi waɗanda suka yi hakan don ka yi musu tambaya game da shawarar da suka yanke. Za su gaya maka cewa suna jin daɗin hidimar kuma suna farin ciki.—Karanta Karin Magana 10:22.
23 A yau, mutane da yawa na yin aiki na sa’o’i da yawa, wasu kuma suna yin ayyuka dabam-dabam don su iya biyan bukatun iyalinsu. Jehobah ya san da hakan kuma duk wani ƙoƙari da muke yi don mu ciyar da iyalinmu yana faranta masa rai. Saboda haka, bari dukanmu mu ci gaba da yin koyi da Jehobah da kuma Yesu ta yin duk wani aiki da muke yi da himma. Kuma bari mu riƙa tunawa cewa aiki mafi muhimmanci da muke da shi, shi ne bauta wa Jehobah da kuma wa’azin Mulkinsa. Hakan zai sa mu yi farin ciki a rayuwa.