Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 66

Ezra ya koyar da Dokar Allah

Ezra ya koyar da Dokar Allah

Yanzu kusan shekara 70 ke nan da Isra’ilawa suka koma Urushalima, amma da akwai wasu da suka ci gaba da zama a yankuna dabam-dabam na Fasiya. Ɗaya daga cikinsu wani firist ne mai suna Ezra kuma yana koya wa mutane Dokar Jehobah. Ezra ya ji cewa mutanen da ke zama a Urushalima ba sa bin Dokar Allah kuma yana so ya je ya taimake su. Sai Sarkin Fasiya mai suna Artaxerxes ya ce masa: ‘Allah ya ba ka hikima don ka koya wa mutane Dokarsa. Ka tafi, kuma ka je da duk wanda yake so ya bi ka.’ Sai Ezra ya je ya sami dukan waɗanda suke so su koma Urushalima. Suka yi addu’a ga Jehobah domin ya kiyaye su a tafiya mai nisan da za su yi, kuma suka kama hanya.

Bayan wata huɗu, sai suka iso Urushalima. Hakiman da suke wurin sun gaya wa Ezra cewa: ‘Isra’ilawa sun yi wa Jehobah rashin biyayya kuma sun auri matan da suke bauta wa allolin ƙarya.’ Mene ne Ezra ya yi? Ezra ya durƙusa a ƙasa a gaban mutanen kuma ya yi addu’a, ya ce: ‘Jehobah, ka yi mana abubuwa da yawa sosai, amma mun yi maka zunubi.’ Duk da cewa mutanen sun tuba, sun ci gaba da yin abubuwa marasa kyau. Sai Ezra ya zaɓi dattawa da alƙalai don su bincika batun. A cikin watanni uku, an kori waɗanda ba sa bauta wa Jehobah.

An gama gina ganuwar Urushalima bayan shekara goma sha biyu. Sai Ezra ya tara mutanen don ya karanta masu Dokar Allah. Da Ezra ya buɗe littafin, sai mutanen suka tashi tsaye. Ya yabi Jehobah, kuma dukansu suka ɗaga hannuwansu sama. Sai Ezra ya karanta musu Dokar Allah, ya bayyana ta kuma mutanen sun saurara da kyau. Sun amince cewa sun sake bijire wa Jehobah kuma suka yi kuka. Washegari, Ezra ya ƙara karanta masu Dokar. Sai suka fahimci cewa ya kamata su yi Idin Bukkoki. Nan da nan suka soma shiri.

Mutanen sun yi kwana bakwai suna farin ciki da kuma godiya domin Jehobah ya albarkaci amfanin gonarsu. Ba a taɓa yin irin wannan Idin Bukkoki ba tun daga lokacin Joshua. Bayan sun gama bikin, sai mutanen suka taru suka yi addu’a cewa: ‘Ya Jehobah, ka cece mu daga zaman bauta, ka ciyar da mu sa’ad da muke daji kuma ka ba mu ƙasa mai kyau. Amma mun ci gaba da yi maka rashin biyayya. Ka tura annabawa don su gargaɗe mu amma mun ƙi saurara. Duk da haka, ka yi haƙuri da mu. Ka cika alkawarin da ka yi wa Ibrahim. Yanzu mun yi alkawari cewa za mu riƙa yi maka biyayya.’ Sun rubuta alkawarin da suka yi, sai hakimai da Lawiyawa da kuma firistoci suka sa hannu a alkawarin.

“Albarka tā fi tabbata ga waɗanda ke jin maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”​—Luka 11:​28, Littafi Mai Tsarki