DARASI NA 77
Yesu da Wata Mata a Bakin Rijiya
Bayan Idin Ƙetarewa, Yesu da almajiransa sun bi Samariya a hanyarsu zuwa Galili. Yesu ya tsaya a wani wuri da ake kira rijiyar Yakubu a kusa da birnin Sukar. Yayin da yake hutawa, sai almajiransa suka je cikin gari don su sayi abinci.
Sai wata mata ta zo ɗiban ruwa. Yesu ya ce mata: “Ki ba ni in sha.” Ta ce: ‘Me ya sa kake magana da ni? Ni Basamariya ce. Yahudawa ba sa magana da Samariyawa.’ Sai Yesu ya ce mata: ‘Da kin san ko waye ne ni, da kin roƙe ni in ba ki ruwa, ni kuwa zan ba ki ruwa mai ba da rai.’ Matar ta ce: ‘Me kake nufi? Ba ka ma da bokitin ɗiban ruwa.’ Sai Yesu ya ce: ‘Duk wanda ya sha ruwan da na ba shi, ba zai sake jin ƙishi ba.’ Matar ta ce: “Ubangiji, ka ba ni wannan ruwan.”
Sai Yesu ya ce mata: ‘Ki je ki kawo mijinki.’ Ta ce: ‘Ba ni da miji.’ Ya ce: ‘Gaskiya kika faɗa. Kin yi aure sau biyar amma yanzu kina zama da mutumin da ba mijinki ba ne.’ Ta ce: ‘Ina ganin kai annabi ne. Mutanenmu sun yi imani cewa a kan wannan dutse ne ya kamata mu bauta wa Allah, amma Yahudawa sun ce a Urushalima ne kaɗai za mu bauta wa Allah. Na yi imani cewa idan Almasihu ya zo, zai koya mana yadda za mu bauta wa Allah.’ Sai Yesu ya gaya mata wani abin da bai taɓa gaya wa kowa ba, ‘Ni ne Almasihu.’
Matan ta je cikin birnin da sauri ta gaya wa Samariyawa cewa: ‘Na ga Almasihu. Ya san kome game da ni. Ku zo ku gan shi!’ Sai suka bi ta zuwa rijiyar kuma suka saurari koyarwar Yesu.
Samariyawan sun gayyace Yesu ya zo cikin birnin. Ya yi kwana biyu a wajen yana koyar da su kuma mutanen suka yi imani da shi. Sun gaya wa Basamariyar cewa: ‘Da muka saurari wannan mutumin, sai muka gane cewa shi ne mai ceto.’
“Zo! Mai jin ƙishi kuma, bari ya zo: wanda yake so, bari ya ɗiba ruwa na rai kyauta.”—Ru’ya ta Yohanna 22:17