Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 95

Sun Ki Su Daina Wa’azi

Sun Ki Su Daina Wa’azi

Akwai wani gurgu da ke zama a ƙofar haikali yana bara. Wata rana, Bitrus da Yohanna sun je haikalin. Sai mutumin ya ce musu: ‘Don Allah ku ba ni kuɗi.’ Bitrus ya ce: ‘Zan ba ka abin da ya fi kuɗi. A cikin sunan Yesu, ka tashi ka yi tafiya!’ Sai Bitrus ya ɗaga shi kuma mutumin ya soma tafiya! Mutane da suka ga abin da ya faru sun yi murna sosai kuma suka zama mabiyan Yesu.

Amma hakan ya sa malaman addinan fushi sosai. Sun kama manzannin kuma suka kai su kotu suna cewa: ‘Wane ne ya ba ku ikon warkar da wannan mutumin?’ Bitrus ya ce: ‘Yesu Kristi, wanda kuka kashe ne ya ba mu ikon yin hakan.’ Sai malaman suka yi ihu suka ce: ‘Ku daina yin magana game da Yesu!’ Amma manzannin sun ce: ‘Dole ne mu yi magana game da shi. Ba za mu daina ba.’

Bayan an saki Bitrus da Yohanna, sai suka je suka gaya wa sauran almajiran abin da ya faru. Sun yi addu’a tare kuma suka roƙi Jehobah cewa: ‘Ka taimake mu mu yi ƙarfin hali don kada mu daina yin aikinka.’ Jehobah ya ba su ruhu mai tsarki kuma suka ci gaba da yin wa’azi da kuma warkarwa. Mutane da yawa sun zama mabiyan Yesu. Hakan ya sa Malaman kishi sosai kuma suka kama almajiran suka saka su a kurkuku. Amma Jehobah ya tura wani mala’ika da daddare don ya buɗe ƙofar kurkukun. Mala’ikan ya ce wa manzannin: ‘Ku koma haikalin don ku ci gaba da wa’azi.’

Washegari, sai ’yan Majalisa da malaman suka ji cewa: ‘Har yanzu kurkukun a rufe yake amma mutanen ba sa nan! Suna cikin haikali suna wa mutane wa’azi.’ Sai aka sake kama manzannin kuma aka kawo su Majalisar Yahudawa. Babban firist ya ce: ‘Ba mun gaya muku cewa kada ku yi wa’azi game da Yesu ba?’ Amma Bitrus ya ce: ‘Dole mu yi biyayya ga Allah fiye da mutane.ʼ

Malaman sun yi fushi sosai har suka so su kashe manzannin. Amma wani Bafarisi mai suna Gamaliel ya ce musu: ‘Ku bi a hankali! Wataƙila Allah yana tare da waɗannan mutanen. Kuna so ku yi yaƙi da Allah ne?’ Sai suka bi shawararsa. Sun sa an yi wa manzannin dūka kuma suka umurce su cewa kada su sake yin wa’azi. Bayan haka, sai suka ƙyale su. Duk da haka, manzannin ba su daina ba. Sun ci gaba da yin wa’azi a cikin haikali da kuma gida-gida ba tare da jin tsoro ba.

“Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”​—Ayyukan Manzanni 5:​29, Littafi Mai Tsarki