Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 96

Yesu Ya Zabi Shawulu

Yesu Ya Zabi Shawulu

An haifi Shawulu a birnin Tarsus amma daga baya, ya zama ɗan ƙasar Roma. Shi Bafarisi ne da ya san Doka sosai kuma ba ya son Kiristoci. Yana kama Kiristoci maza da mata daga gidajensu kuma ya jefa su cikin kurkuku. Sa’ad da ʼyan tawaye suka jefi wani almajirin Yesu mai suna Istifanus har ya mutu, Shawulu yana wurin yana kallo.

Amma ba Kiristoci da ke Urushalima ne kaɗai Shawulu yake so ya kama ba. Ya nemi izini daga wajen babban firist don ya kama Kiristocin da ke birnin Dimashƙa. Sa’ad da Shawulu ya kusa da birnin, wuta mai haske ta shiga idanunsa, sai ya faɗi a ƙasa. Sai ya ji wata murya ta ce: ‘Shawulu, me ya sa kake tsananta mini?’ Shawulu ya ce: ‘Wane ne kai?’ Muryar ta ce: ‘Ni Yesu ne. Ka je Dimashƙa, kuma za ka ji abin da za ka yi.’ Nan da nan Shawulu ya makance, sai aka ja-gorance shi zuwa birnin.

Akwai wani mabiyin Yesu a birnin Dimashƙa mai suna Hananiya. Yesu ya gaya masa a cikin wahayi cewa: ‘Ka je gidan Yahuda a wani unguwa da ake kira Miƙaƙƙiya kuma ka nemi Shawulu.’ Hananiya ya ce: ‘Ubangiji na san wannan mutumin sosai! Shi ne yake jefa mabiyanka a cikin kurkuku!’ Amma Yesu ya ce masa: ‘Ka je wurin sa don na zaɓe shi ya yi wa’azin Mulki ga al’ummai da yawa.’

Sai Hananiya ya sami Shawulu kuma ya ce masa: ‘Ɗan’uwa Shawulu, Yesu ya aike ni in buɗe maka ido.’ Nan take sai Shawulu ya soma gani. Ya koyi game da Yesu kuma ya zama mabiyinsa. Bayan ya yi baftisma, sai ya soma wa’azi a majami’u tare da ’yan’uwansa Kiristoci. Ka yi tunanin yadda Yahudawa za su yi mamaki sa’ad da suka ga Shawulu yana wa’azi game da Yesu. Sun ce: ‘Ba wannan mutumin ba ne yake tsananta wa mabiyan Yesu ba?’

Shawulu ya yi shekara uku yana yi wa mutane wa’azi a Dimashƙa. Yahudawa sun tsane Shawulu sosai kuma suka soma tunanin yadda za su kashe shi. Da ’yan’uwa suka sami labari game da abin da Yahudawan suke shirin yi, sai suka taimaka wa Shawulu ya gudu. Sun saka shi a cikin kwando kuma suka fitar da shi ta wani ƙaramin rami da ke katangar birnin.

Sa’ad da Shawulu ya koma Urushalima, ya so ya yi tarayya da ’yan’uwan da ke wurin, amma suna jin tsoro. Sai wani mabiyin Yesu mai suna Barnaba ya kawo Shawulu wurin manzannin kuma ya tabbatar musu da cewa ya yi tuban gaske. Shawulu ya ci gaba da yin wa’azi da ƙwazo tare da yan’uwan da ke Urushalima. Daga baya, ya canza sunansa zuwa Bulus.

“Kristi Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu-zunubi; cikinsu kuwa ni ne babba.”​—1 Timotawus 1:15