DARASI NA 19
Annoba ta Daya Zuwa Uku
An sa Isra’ilawa su riƙa aiki kamar bayi. Sai Jehobah ya aiki Musa da Haruna su gaya wa Fir’auna cewa: ‘Ka bar mutanena su tafi don su bauta mini a jeji.’ Amma Fir’auna mai fahariya ya ce: ‘Ba ruwana da abin da Jehobah ya faɗa kuma ba zan bar Isra’ilawa su tafi ba.’ Sai Fir’auna ya ce a daɗa wulaƙanta su. Da Jehobah ya ga hakan, sai ya ce zai koya wa Fir’auna hankali. Ta yaya ya yi hakan? Ya kawo Annoba Goma a kan mutanen ƙasar Masar. Sai Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Fir’auna yana da taurin kai. Gobe da safe, zai je Kogin Nilu. Ka je wurin ka gaya masa cewa idan bai bar mutanena su tafi ba, duka ruwan Kogin zai zama jini.’ Musa ya je wurin Fir’auna kamar yadda Jehobah ya gaya masa. Fir’auna yana kallo sa’ad da Haruna ya buga ruwan da sandarsa kuma ruwan ya zama jini. Sai ruwan kogin ya soma wari, kifayen da ke ciki suka mutu kuma ba su da ruwan sha. Har yanzu, Fir’auna ya ƙi barin Isra’ilawa su tafi.
Bayan kwana bakwai, sai Jehobah ya ce Musa ya koma wurin Fir’auna kuma ya gaya masa cewa: ‘Zan sa kwaɗi su cika ƙasar Masar idan ba ka bar mutanena su tafi ba.’ Bayan haka, Haruna ya ɗaga sandarsa, sai kwaɗi suka cika ko’ina a ƙasar. An ga kwaɗi a gidaje da kan gado da kuma a cikin kwanuka. Babu inda ba kwaɗi! Sai Fir’auna ya ce Musa ya roƙi Jehobah don kwaɗin su tafi kuma ya ce idan aka yi hakan, zai bar Isra’ilawa su tafi. Sai Jehobah ya kashe kwaɗin kuma mutanen Masar suka kwashe kwaɗi da yawa. Sai gabaki ɗaya ƙasar ta soma wari. Duk da haka, Fir’auna ya ƙi ya bar Isra’ilawa su tafi.
Sai Jehobah ya gaya wa Musa cewa: ‘Ka gaya wa Haruna ya bugi ƙasa da sandarsa kuma ƙasar za ta zama kwarkwata.’ Da ya yi hakan, sai kwarkwata suka cika ko’ina. Wasu daga cikin mutanen Fir’auna sun gaya masa cewa: ‘Wannan annoba ce daga wurin Allah.’ Duk da haka, Fir’auna ya ƙi ya bar Isra’ilawa su tafi.
“Zan sa su san ƙarfina da ikona, za su kuwa sani sunana Yahweh ne.”—Irmiya 16:21, Juyi Mai Fitar da Ma’ana