Gabatarwa
ALLAH MAI IKO DUKA shi ne Mamallakin dukan halitta. Rayuwarmu ta yanzu, da ta gobe, ta dangana ne a gare shi. Yana da ikon ya ba da lada kuma yana da ikon ya yi horo. Yana da ikon ya ba da rai kuma yana da ikon ya ɗauki rai. Idan muka samu yardarsa, za mu yi nasara; idan ba mu samu yardarsa ba, to, za mu ɗanɗana kuɗarmu. Saboda haka, yana da muhimmanci ƙwarai ya gamsu da bautarmu!
Mutane suna bauta ta hanyoyi da yawa. Idan addini yana kama da hanya, hanyoyin dukan addinai suna da yardar Allah ne? A’a, ba su da ita. Yesu, annabin Allah, ya nuna cewa da akwai hanyoyi guda biyu ne kawai. Ya ce: “Ƙofa da fāɗi take, hanya kuwa da fāɗi, wadda ta nufa wajen halaka, mutane da yawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.”—Matta 7:13, 14.
Addinai iri biyu ne kawai ake da su: ɗaya yana kai wa zuwa rai kuma ɗayan yana kai wa zuwa halaka. Manufar wannan ƙasidar domin ta taimake ka ne ka samu hanyar da take kai wa zuwa rai.