SASHE NA 5
Gaskiya Game da Sihiri, Bokanci, da Kuma Maita
1. Yaya yaɗuwar imani da sihiri, bokanci, da kuma maita take?
“A AFIRKA, ɓata lokaci ne a fara da tambayar nan, da akwai mayu ko babu,” in ji littafin nan African Traditional Religion, ya daɗa cewa “ga mutanen Afirka na kowane matsayi, maita gaskiya ce mai muhimmanci.” Waɗanda suka yi imani da sihiri, bokanci, da kuma maita sun haɗa da jahilai da kuma masana. Shugabannin addinin Musulunci da kuma na Kiristendam su ma sun yi imani da ita.
2. Bisa ga sanannen imani, daga ina ake samun ikon sihiri?
2 Bisa ga wani sanannen imani a Afirka, da akwai wani iko na ruhaniya da ba a fahimtar shi. Allah ne yake da iko bisansa. Ruhohi da kuma kakanni za su iya yin amfani da shi. Wasu mutane kuma sun san yadda za su tsotsa shi kuma su yi amfani da shi, ko ga nagarta (farin sihiri) ko kuma ga mugunta (baƙin sihiri).
3. Menene baƙin sihiri, kuma menene mutane suka yi imani zai iya yi?
3 Baƙin sihiri, ko bokanci, ana yin amfani da su ga abokan gāba. Waɗanda suke amfani da shi an yi imanin cewa suna da ikon su aiki jemage, tsuntsaye, da kuma wasu dabbobi su faɗa wa mutane. Baƙin sihiri an yi imani cewa shi yake jawo faɗa, bakaranci, ciwo, har ma da mutuwa.
4. Menene mutane da yawa suka gaskata game da mayu, kuma wane ikirari waɗanda suka taɓa yin maita suka yi?
4 Wadda ta yi kusa da shi ita ce maita. An ce mayu suna barin jikinsu daddare su tashi, ko su haɗu da wasu mayun ko kuma su cinye wanda suke so su ci. Tun da jikin mayun zai kasance a kan gado yana barci, ana samun goyon baya ga irin wannan labari musamman daga mutane da suka yi ikirari suka bar maita. Alal misali, wata jarida ta Afirka ta ɗauko abin da mayu da suka bar maita (yawanci ’yammata ƙanana) suna cewa: “Na kashe mutane 150 ta wajen haddasa haɗarin mota.” “Na kashe yara biyar ta wajen tsotse jininsu.” “Na kashe samari na uku domin sun yasar da ni.”
5. Menene farin sihiri, kuma yaya ake yin sa?
5 Farin sihiri an yi imani cewa zai yi
kāriya daga mugunta. Waɗanda suke yin farin sihiri suna saka zobuna na sihiri ko kuma kambuna. Suna shan ko kuma shafa maganin tsari a jikinsu. A gidajensu ko kuma a ƙasa, suna ɓoye abubuwa da aka yi imanin cewa suna da ikon kāriya. Suna dogara ga layu da suka ƙunshi ayoyi daga Alkur’ani ko kuma Littafi Mai Tsarki.Ƙarya da Yaudara
6. Menene Shaiɗan da aljannunsa suka yi a dā, kuma yaya ya kamata mu yi tunanin ikonsu?
6 Gaskiya ne cewa Shaiɗan da aljannunsa miyagun abokan gāban mutane ne. Suna da iko su rinjayi tunani da kuma rayuwan mutane, kuma a dā sun shiga cikin mutane da dabbobi. (Matta 12:43-45) Ko da yake ba za mu rage ikonsu ba, ba za mu ƙara musu ba.
7. Menene Shaiɗan yake so mu gaskata, kuma ta yaya aka misalta wannan?
7 Shaiɗan uban yaudara ne. Yana yaudarar mutane su yi tunanin cewa yana da iko fiye da yadda yake da shi. Alal misali: A lokacin yaƙi a wata ƙasa a Afirka, sojoji sun yi amfani da kayayyakin sauti su tsoratar da abokan gābansu. Kafin su kai farmaki, sojojin sai su saka kaset na ƙarar igogi da na bindigogi. Suna son abokan gāban su yi tunanin cewa abokan gāban da suka kawo musu farmaki suna da manyan makamai masu yawa. Hakanan, Shaiɗan yana so mutane su yi imani cewa ikonsa ba shi da iyaka. Manufarsa shi ne ya tsoratar da mutane su yi nufinsa ba nufin Jehobah ba. Bari mu bincika ƙaryace-ƙaryace uku da Shaiɗan yake so mutane su gaskata.
8. Mecece ƙarya ɗaya da Shaiɗan yake yaɗawa?
8 Ƙarya ɗaya da Shaiɗan yake ɗaukakawa ita ce: Babu mugun abu da yake faruwa cikin tsausayi; kowane irin abu da ya faru idan ba wani ne ya yi ba ya faru ne ta wajen wani iko. Alal misali, a ce yaro ya mutu domin zazzaɓin cizon sauro. Uwarsa wataƙila ta san cewa zazzaɓi cuta ne da sauro suke ɗauke da shi. Amma kuma za ta gaskata cewa wani ne ya yi amfani da maita ya aiko sauro ya ciji ɗanta.
9. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shaiɗan ba ya haddasa dukan matsaloli?
9 Ko da yake Shaiɗan yana da ikon ya haddasa wasu matsaloli, ba daidai ba ne a yi imani da cewa yana da ikon ya haddasa kowane irin matsala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsere, ba mai-sauri ke ci ba; yaƙi kuma, ba ga ƙarfafa ya ke ba; abinci kuma, ba ga masu-hikima ba; arziki kuma, ba ga masu-azanci ba; tagomashi kuma, ba ga masu-gwaninta ba: amma ga dukansu lokacinsu da zarafinsu su kan zo.” (Mai-Wa’azi 9:11) Wani mai tsere zai kasance yana da sauri fiye da wasu, amma wataƙila ba zai ci ba. Wani ‘tsausayi’ yakan sa ya faɗi. Wataƙila ya yi tuntuɓe ya faɗi ko kuma ya yi rashin lafiya ko ma tsoka ta ja. Irin waɗannan abubuwa za su iya faruwa da kowa. Ba wajibi ba ne a ji Shaiɗan ne ya haddasa su ko kuma ta wajen maita; suna faruwa ne kawai.
10. Menene aka ce game da mayu, kuma ta yaya muka sani cewa wannan ƙarya ce?
10 Ƙarya ta biyu da Shaiɗan yake yaɗawa ita ce: Mayu suna barin jikinsu kuma su yi tafiya cikin dare su taru da wasu mayu ko kuma su tsotse ko su cinye wanda
suke so su ci. A yanzu ka tambayi kanka: ‘Idan mayu za su iya yin haka, menene ainihi yake barin jikinsu?’ Kamar yadda muka gani, kurwa mutumin ne kansa, ba wani abu ba ne da zai iya barin mutum. Bugu da ƙari, ruhun kuma ikon rai ne da yake ƙarfafa jiki amma kuma ba ya iya yin kome ba tare da jiki ba.11. Me ya sa muka sani cewa mayu ba za su iya barin jikinsu ba, kuma ka yi imani da haka?
11 Babu kurwa ko kuma ruhu da zai iya barin jiki ya yi wani abu, mai kyau ko marar kyau. Saboda haka, mayu ba za su iya barin jikinsu ba. Ba za su iya yin abubuwa da suke da’awar suna yi ba ko kuma waɗanda suke tunanin sun yi.
12. Ta yaya Shaiɗan yake sa mutane su yi imani cewa sun yi abubuwa da ba su yi ba?
12 Me za mu ce game da ikirari da wasu mayu suka yi? Shaiɗan zai iya sa mutane su yi imani cewa sun yi abubuwa da ba su yi ba. Ta wajen wahayi, Shaiɗan zai iya sa mutane su yi tunanin cewa sun gani, sun ji, ko kuma sun yi abubuwa da ba su yi ba. Ta wannan hanyar, Shaiɗan yana sa rai cewa zai juyar da mutane daga Jehobah kuma ya sa su yi tunanin cewa Littafi Mai Tsarki ba gaskiya ba ne.
13. (a) Farin sihiri yana da kyau ne? (b) Menene Nassosi suka ce game da sihiri?
13 Ƙarya ta uku ita ce wannan: Farin sihiri—sihiri da aka yi imani cewa zai yi hamayya da baƙin sihiri—yana da kyau. Littafi Mai Tsarki bai bambanta tsakanin baƙin sihiri da farin sihiri ba. Ya haramta dukan sihiri. Ka yi la’akari da dokoki da Jehobah ya bai wa al’ummar Isra’ila game da sihiri da kuma waɗanda suke yin su:
-
‘Ba za ku yi sihiri ba.’—Leviticus 19:26.
-
“Namiji kuma ko mace mai-mabiya, ko wanda shi ke maye, hakika za a kashe shi.”—Leviticus 20:27.
-
“Daga cikinka ba za a iske wanda yana . . . mai-sihiri, ko mai-arwa, ko Kubawar Shari’a 18:10-14.
mai-magana da mai-mabiya.”—
14. Me ya sa Jehobah ya ba da doka a kan sihiri?
14 Waɗannan dokoki suna bayyana sarai cewa Allah ba ya son mutanensa su yi sihiri. Jehobah ya bai wa mutanensa dokar domin yana ƙaunarsu kuma ba ya so su zama bayi ga tsoro da kuma camfi. Ba ya son aljannu su matsa musu.
15. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana da iko sosai fiye da Shaiɗan?
15 Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai faɗa dalla-dalla ba game da abin da aljannu za su iya yi da abin da ba za su iya ba, ya nuna cewa Jehobah Allah yana da iko sosai fiye da Shaiɗan da aljannunsa. Jehobah ya sa an kori Shaiɗan daga sama. (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Ka lura cewa, Shaiɗan ya nemi izini ya jarraba Ayuba kuma ya yi wa Allah biyayya da gargaɗin kada ya kashe Ayuba.—Ayuba 2:4-6.
16. Ga wa za mu dogara domin kāriya?
16 Misalai 18:10 ta ce: “Sunan Ubangiji kagara ne mai-ƙarfi: Mai-adalci ya kan gudu ya shiga ciki, shi sami lafiya.” Ya kamata mu je ga Jehobah domin mu nemi kāriya. Bayin Jehobah ba sa amfani da laya ko magani domin su kāre kansu daga muguntar Shaiɗan da aljannunsa, ko kuma su tsoraci jifar bokaye. Bayin Allah sun yi imani da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.”—2 Labarbaru 16:9.
17. Game da menene Yaƙub 4:7 ta ba mu tabbaci, amma menene dole mu yi?
17 Kai ma za ka kasance da wannan tabbacin idan ka bauta wa Jehobah. Yaƙub 4:7 ta ce: “Ku zama fa masu-biyayya ga Allah amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.” Idan ka bauta wa Allah na gaskiya, ka miƙa kanka gare shi, ka tabbata cewa Jehobah zai kāre ka.