DA UKU
BABI NA ASHIRINYa Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
1. A wane lokaci ne Bitrus ya fi baƙin ciki a rayuwarsa?
BITRUS ba zai taɓa manta da lokacin da suka haɗa ido da Ubangijinsa ba. Shin kallon da Yesu ya yi masa ya nuna baƙin ciki ne ko kunya? Ba mu sani ba, amma mun san cewa labarin ya ce, “Ubangiji ya waiwaya, ya dubi Bitrus.” (Luk 22:61) Kallon nan da ya yi wa Bitrus ya nuna cewa ya yi kuskure sosai. Bitrus ya fahimci cewa ya yi ainihin abin da Yesu ya annabta. Ko da yake Bitrus ya nace cewa ba zai taɓa yin musun sanin Ubangijinsa ba, amma ya yi hakan. A wannan lokacin ne Bitrus ya fi yin baƙin ciki a rayuwarsa.
2. Wane darasi ne Bitrus yake bukatar ya koya, kuma ta yaya za mu amfana daga labarinsa?
2 Duk da haka, Bitrus yana da bege. Da yake shi mutumi ne mai bangaskiya sosai, yana da zarafin shawo kan kurakuransa kuma ya koyi ɗaya daga cikin darussan da Yesu ya koyar. Darasin game da gafartawa ne kuma kowannenmu yana bukatar ya koyi irin wannan darasin. Saboda haka, bari mu tattauna yadda Bitrus ya koyi wannan darasi mai wuya.
Mutumin da ke da Abubuwan da Zai Koya
3, 4. (a) Wace tambaya ce Bitrus ya yi wa Yesu, kuma wane tunani ne wataƙila Bitrus ya yi? (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa halayen da suka zama gama gari a lokacin sun rinjayi Bitrus?
3 Sa’ad da Bitrus yake garinsu a Kafarnahum kusan watanni shida da suka shige, ya je wurin Yesu kuma ya tambaye shi: “Ubangiji, sau nawa ɗan’uwana za ya yi mani zunubi, in gafarta masa? har sau bakwai?” Wataƙila Bitrus yana tunani cewa ta yin hakan yana da kirki sosai. Ballantana ma a zamanin, malaman addinai sun koyar cewa sau uku ne kawai ya kamata mutum ya riƙa gafartawa! Yesu ya amsa masa cewa: “Ban ce maka, har sau bakwai ba; amma, har bakwai bakwai sau saba’in.”—Mat. 18:21, 22.
4 Shin Yesu yana nufin Bitrus ya riƙa ƙirga yawan laifuffuka da aka yi masa ne? A’a, maimakon hakan, ta wajen mai da bakwai 1 Kor. 13:4, 5) Yesu ya nuna cewa taurin zuciya da halin rashin gafartawa na mutanen zamanin da ya zama gama gari ya rinjayi Bitrus, domin a lokacin ana lissafa kurakuran mutum kamar ana lissafin bashi. Amma, mutumin da ke bin ƙa’idodin Allah yana gafartawa a kowane lokaci.—Karanta 1 Yohanna 1:7-9.
da Bitrus ya ambata zuwa saba’in da bakwai, yana nufin cewa babu iyaka ga gafartawa. (5. A wane lokaci ne wataƙila muke bukatar mu koyi gafartawa sosai?
5 Bitrus bai yi mūsu da Yesu ba. Amma shin darasin Yesu ya ratsa zuciyarsa kuwa? A wasu lokatai muna koyon gafartawa sosai sa’ad da muka fahimci cewa muna bukatar gafara. A Yanzu, bari mu mai da hankali ga abubuwan da suka faru a wannan lokacin har zuwa sa’ad da Yesu ya mutu. A wannan lokaci mai wuya, Bitrus yana bukatar Ubangijinsa ya gafarta masa tun da yake ya yi kurakurai da yawa.
Yesu Ya Gafarci Bitrus Sau da Yawa
6. Mene ne Bitrus ya yi sa’ad da Yesu ya yi ƙoƙarin koya wa almajiransa game da tawali’u, kuma yaya Yesu ya bi da shi?
6 Dare na ƙarshe da Yesu zai yi a duniya yana da muhimmanci sosai. Yesu yana bukatar ya daɗa koya wa almajiransa abubuwa da yawa game da tawali’u. Ya kafa misalin kasancewa da tawali’u ta wajen wanke ƙafafunsu, irin aikin da bayi suke yi. Da farko, Bitrus ba ya son Yesu ya wanke ƙafafunsa. Amma daga baya, ya ce idan Yesu ya nace, wajibi ne ya wanke hannayensa da ƙafafunsa da kuma kansa! Yesu bai yi fushi ba, amma ya bayyana muhimmanci da kuma ma’anar abin da yake yi.—Yoh. 13:1-17.
7, 8. (a) Waɗanne kurakurai ne kuma Bitrus ya yi? (b) Ta yaya Yesu ya ci gaba da gafarta wa Bitrus da kuma yi masa alheri?
7 Jim kaɗan bayan hakan, Bitrus ya kuma yi ƙoƙarin sa Yesu fushi. Shi da kuma sauran manzannin suka soma mūsu game da wanda ya fi girma. Amma, Yesu ya yi musu gyara cikin tawali’u kuma ya ƙarfafa su don sun kasance da aminci ga Ubangijinsu. Ya kuma annabta cewa dukansu za su yashe shi. Bitrus ya amsa cewa zai kasance tare da Yesu ko a gaban mutuwa. Yesu ya annabta cewa Bitrus zai yi mūsun saninsa sau uku a daren kafin zakara ya yi cara sau biyu. Bitrus ya kuma cika baki cewa zai fi dukan sauran almajiran kasancewa da aminci!—Mat. 26:31-35; Mar. 14:27-31; Luk 22:24-28; Yoh. 13:36-38.
8 Shin Yesu ya yi fushi da Bitrus ne? Babu shakka, a wannan mawuyacin lokaci, Yesu ya ci gaba da mai da hankali ga halaye masu kyau na almajiransa ajizai. Ya san cewa Bitrus zai yashe shi, Luk 22:32) Yesu yana da tabbaci cewa Bitrus zai tuba kuma ya ci gaba da bauta wa Allah da aminci. Wannan halin gafartawa ne kuwa!
duk da haka ya ce: “Na yi maka addu’a kada bangaskiyarka ta kāsa: kai ma lokacin da ka sāke juyowa, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” (9, 10. (a) Wace gyara ce aka yi wa Bitrus a lambun Jatsaimani? (b) Mene ne kurakuran da Bitrus ya yi suka tuna mana?
9 Daga baya, a lambun Jatsaimani, Yesu ya yi wa Bitrus gyara fiye da sau ɗaya. Yesu ya ce wa Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna su yi tsaro yayin da yake addu’a. Yesu yana baƙin ciki ƙwarai kuma yana bukatar taimako, amma Bitrus da sauran sun yi ta barci. Yesu ya san kasawarsu kuma ya gafarta musu, shi ya sa ya ce: “Gaskiya ruhu ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Mar. 14:32-41.
10 Ba da daɗewa ba, taron ’yan iska suka taho, suna riƙe da tocila da takuba da kulake. A yanzu, ya kamata dukan manzannin su kasance da basira da kuma hankali. Duk da haka, Bitrus ya yi hanzarin ɗaukan mataki kuma ya yanke kunnen wani bawan babban firist mai suna Malkus da takobinsa. Yesu ya yi wa Bitrus gargaɗi cikin tawali’u, kuma ya warkar da bawan. Sai ya bayyana abin da ya sa bai kamata mabiyansa su yi faɗa ba. (Mat. 26:47-55; Luk 22:47-51; Yoh. 18:10, 11) Bitrus ya riga ya yi kurakurai da yawa da yake bukatar Ubangijinsa ya gafarta masa. Labarinsa zai iya tuna mana cewa dukanmu mukan yi zunubi sau da sau. (Karanta Yaƙub 3:2.) Wane ne a cikinmu ba ya bukatar Allah ya riƙa gafarta masa a kowace rana? Har ila, da akwai sauran abubuwan da za su faru da Bitrus a daren nan. Zai yi kurakurai mafi tsanani.
Kuskuren Bitrus Mafi Tsanani
11, 12. (a) Ta yaya Bitrus ya ɗan nuna gaba gaɗi bayan da aka kama Yesu? (b) Ta yaya Bitrus ya kasa yin abin da ya ce zai yi?
11 Yesu ya tattauna da ’yan iskan cewa idan shi suke nema, su ƙyale almajiransa su tafi. Sa’ad da ’yan iskan suka kama Yesu, Bitrus bai iya yin kome ba kuma daga baya ya bi sauran manzannin da suka gudu.
12 Wataƙila Bitrus da Yohanna sun daina guduwa sa’ad da suka yi kusa da gidan Hananiya Babban Firist na dā, wurin da aka soma kai Yesu. Sa’ad da aka fito da Yesu daga wurin, Bitrus da Yohanna suka bi shi “daga nesa.” (Mat. 26:58; Yoh. 18:12, 13) Bitrus ba matsoraci ba ne. Babu shakka, da a ce ba shi da gaba gaɗi, da ba zai je inda aka kai Yesu ba. ’Yan iskan suna riƙe da makamai, kuma Bitrus ya riga ya ji wa ɗayansu rauni. Duk da haka, bai nuna cewa yana da gaba gaɗi da har zai mutu tare da Ubangijinsa kamar yadda ya yi da’awa ba.—Mar. 14:31.
13. Idan muna so mu bi Kristi da gaske, mene ne ya wajaba mu yi?
13 Kamar Bitrus, mutane da yawa a yau suna son su bi Kristi “daga nesa,” don kada kowa ya san cewa suna binsa. Amma daga baya Bitrus da kansa ya rubuta cewa idan muna so mu bi Kristi da gaske, wajibi ne mu kusace shi sosai kuma mu bi misalinsa a duk abin da muke yi, ko da mene ne sakamakon yin hakan.—Karanta 1 Bitrus 2:21.
14. Mene ne Bitrus ya yi sa’ad da ake yi wa Yesu shari’a?
14 Bitrus ya bi waɗanda suka kama Yesu a hankali har suka iso ƙofar wani babban gida a Urushalima. Gidan Kayafa ne, babban firist mai wadata da kuma iko. Yawancin irin waɗannan gidajen suna da farfajiya da kuma manyan ƙofofi. Bitrus ya iso ƙofar kuma ba a yarda ya shiga ba. Yohanna ya riga ya shiga ciki domin ya waye babban firist ɗin. Sai ya fito kuma ya ce wa mai gadin ya ƙyale Bitrus ya shiga. Kamar Bitrus bai tsaya kusa da Yohanna ba, kuma bai shiga cikin gidan ba balle ma ya tsaya kusa da Ubangijinsa. Ya zauna a farfajiyar, inda wasu bayi da dogaran haikalin suke jin ɗumin wuta domin ana ɗari daddaren kuma suna kallon yadda ake yi wa Yesu shari’a a ciki.—Mar. 14:54-57; Yoh. 18:15, 16, 18.
15, 16. Ka bayyana yadda annabcin Yesu cewa Bitrus zai yi mūsun saninsa sau uku ya cika.
15 Hasken wutar ya sa yarinyar da ta ƙyale Bitrus ya shiga ta ga fuskarsa sosai kuma ta gane shi. Sai ta tuhume shi cewa: “Kai kuma dā kana tare da Yesu Ba-galilin nan!” Ba zato ba tsammani, Bitrus ya musunci sanin Yesu, ya yi kamar bai san abin da yarinyar take faɗa ba. Sai ya koma ya tsaya kusa da ƙofar don kada a waye shi, amma wata yarinya ta gane shi kuma ta nuna shi, ta ce: “Wannan mutum kuma dā yana tare da Yesu Ba-nazarat.” Bitrus ya rantse cewa: “Ban san mutumin ba.” (Mat. 26:69-72; Mar. 14:66-68) Wataƙila bayan wannan musu na biyu da Bitrus ya yi ne zakara ya yi cara na farko, amma bai tuna da annabcin da Yesu ya furta ɗazu ba.
16 Bayan hakan, Bitrus ya ci gaba da yin ƙoƙari kada a waye shi. Amma rukunin mutanen da ke tsaye a farfajiyar suka matso kusa da shi. Ɗaya cikinsu ɗan’uwan Malkus ne, wato bawan da Bitrus ya ji wa rauni. Ya ce wa Bitrus: “Ko ban gan ka a cikin gona tare da shi ba?” Bitrus ya nemi ya sa su yarda cewa ba gaskiya ba ne, kuma ya rantse cewa la’ana ta same shi idan ƙarya yake yi. Yoh. 18:26, 27; Mar. 14:71, 72.
Wannan ne lokaci na uku da Bitrus ya yi musun sanin Yesu. Da zarar ya furta kalamin sai zakara ya yi cara. Wannan cara ta biyu ke nan da Bitrus ya ji a daren nan.—17, 18. (a) Mene ne Bitrus ya yi sa’ad da ya ankara cewa ya yi wa Ubangijinsa laifi? (b) Wane tunani ne wataƙila Bitrus ya yi?
17 Yesu ya shigo cikin barandar yana kallon farfajiya, sai idanunsa suka haɗu da na Bitrus kamar yadda aka faɗa a somawar wannan babin. Bitrus ya ankara cewa ya yi wa Ubangijinsa laifi mai tsanani. Bitrus ya fita daga farfajiyar cike da takaici saboda kuskurensa. Ya nufa cikin birnin, hasken wata kuma ta cika ko’ina. Hawaye suka cika idanunsa kuma ya yi ta kuka sosai.—Mar. 14:72; Luk 22:61, 62.
18 Sa’ad da mutum ya ankara cewa ya yi kuskure mai tsanani, yana da sauƙi ya soma tunani cewa ba za a iya gafarta zunubansa ba. Wataƙila Bitrus ya yi tunanin cewa Yesu ba zai gafarta masa ba. Shin za a gafarta masa kuwa?
Shin Za a Gafarta wa Bitrus Kuwa?
19. Yaya wataƙila Bitrus ya ji game da kuskuren da ya yi, kuma ta yaya muka san cewa bai yi sanyin gwiwa ba?
19 Wataƙila Bitrus ya yi baƙin ciki sosai washegari sa’ad da ya ga abin da ya faru da Yesu. Babu shakka, ya tsauta wa kansa sosai sa’ad da Yesu ya mutu da ranar bayan ya sha azaba! Wataƙila Bitrus ya yi baƙin ciki sosai duk sa’ad da ya tuna da yadda ya ɓata wa Ubangijinsa rai a dare na ƙarshe kafin ya mutu. Duk da tsananin baƙin cikin da ya yi, Bitrus bai yi sanyin gwiwa ba. Mun san da hakan domin ba da daɗewa ba ya sake soma tarayya da sauran almajiran. (Luk 24:33) Babu shakka, dukan almajiran sun yi baƙin ciki saboda abin da suka yi a wannan daren kuma sun ƙarfafa juna.
20. Mene ne za mu iya koya daga shawara mafi kyau da Bitrus ya yanke?
20 Bitrus ya yanke shawara mafi kyau. Idan bawan Allah ya yi iya ƙoƙarinsa ya daidaita kuskurensa, Allah zai gafarta masa ko da kuskuren yana da tsanani. (Karanta Misalai 24:16.) Bitrus ya nuna tabbataciyar bangaskiya ta wajen kasancewa tare da sauran almajiran duk da cewa yana baƙin ciki. Idan mutum yana baƙin ciki ko nadama, zai so ya kaɗaita amma hakan zai daɗa sa yanayin ya yi muni. (Mis. 18:1) Abu mafi kyau shi ne ya kasance tare da ’yan’uwansa don ya samu ƙarfafa da zai sa ya ci gaba da bauta wa Allah.—Ibran. 10:24, 25.
21. Wane labari ne Bitrus ya ji da yake ya kasance tare da sauran almajiran Yesu?
21 Domin Bitrus ya kasance tare da sauran almajiran Yesu, ya sami labari cewa an ɗauke gawar Yesu daga kabarin. Bitrus da Yohanna suka gudu zuwa kabarin da aka binne Yesu. Yohanna da wataƙila matashi ne ya fara isa wurin kafin Bitrus. Sa’ad da Yohanna ya tarar da ƙofar a buɗe sai ya dakata, amma Bitrus ya shiga. Ko da yake ya gaji don gudun da ya yi, ya shiga kabarin kuma ya ga cewa babu kome a ciki!—Yoh. 20:3-9.
22. Me ya sa Bitrus ya daina baƙin ciki da kuma shakkar da yake yi?
22 Shin Bitrus ya amince cewa Yesu ya tashi daga matattu kuwa? Da farko, bai yarda ba duk da yake mata amintattu sun sanar musu cewa mala’iku sun ce Yesu ya tashi daga matattu. (Luk 23:55–24:11) Amma a ƙarshen ranar, Bitrus ya daina baƙin ciki da kuma shakkar da yake yi a dā. Yanzu Yesu yana da rai a matsayin ruhu mai iko! Ya bayyana ga dukan manzanninsa, amma ya fara bayyana ga Bitrus kaɗai. Manzannin sun ce: “Hakika Ubangiji ya tashi, ya kuwa bayyana ga Siman.” (Luk 24:34) Hakazalika, manzo Bulus daga baya ya rubuta game da wannan rana ta musamman da Yesu ya “bayyana ga Kefas; kāna ga su goma sha biyu.” (1 Kor. 15:5) Kefas da Siman wasu sunayen da ake kiran Bitrus ne. Hakika, Yesu ya bayyana ga Bitrus sa’ad da yake shi kaɗai.
Bitrus ya yi kura-kurai da yawa da yake bukatar Ubangijinsa ya gafarta masa, waye a cikinmu ba ya bukatar gafara kowace rana?
23. Me ya sa Kiristoci a yau da suka yi zunubi mai tsanani suke bukatar su tuna da labarin Bitrus?
23 Littafi Mai Tsarki bai bayyana dalla-dalla abin da ya faru sa’ad da Yesu da Bitrus suka sake haɗuwa ba. Amma dai, za mu iya yin tunani a kan yadda Bitrus ya ji sa’ad da ya ga ƙaunataccen Ubangijinsa domin zai samu zarafin nuna baƙin cikinsa kuma ya nemi gafara. Abu mafi muhimmanci da yake bukata shi ne a gafarta masa. Babu shakka, Yesu ya gafarta masa a yalwace. Kiristoci a yau da suka yi zunubi suna bukatar su tuna da labarin Bitrus. Kada mu taɓa tunani cewa Allah ba zai gafarta mana ba. Yesu yana wakiltar Ubansa sarai, wanda ke “gafara a yalwace.”—Isha. 55:7.
Ƙarin Tabbaci na Gafartawa
24, 25. (a) Ka bayyana abin da ya faru a daren da Bitrus ya je sū a Tekun Galili. (b) Mene ne Bitrus ya yi sa’ad da Yesu ya yi mu’ujiza washegari da safe?
24 Yesu ya gaya wa almajiransa su je Galili, inda za su sake haɗuwa da shi. Sa’ad da suka isa wurin, Bitrus ya tafi Tekun Galili Mat. 26:32; Yoh. 21:1-3.
don sū. Da yawa cikinsu suka bi shi. Bitrus ya sake ganin kansa a tafkin da yake yawan kasancewa shekaru da yawa da suka shige. Babu shakka, ya tuna da ƙarar tafiyar jirgin da ta raƙumin ruwan da yadda yake riƙe tarunsa. Ko yaya dai, ba su kama kifi daddaren ba.—25 Amma da sassafe, wani ya kira su daga bakin tekun kuma ya umurce su su saka tarunsu cikin ɗayan ɓangaren jirgin. Suka yi hakan kuma suka kama kifaye guda ɗari da hamsin da uku! Bitrus ya san wannan mutumin. Ya yi tsalle daga jirgin zuwa Yoh. 21:4-14.
bakin tekun. A bakin tekun, Yesu ya ba su kifin da aka gasa da wutan gawayi kuma ya mai da hankali ga Bitrus.—26, 27. (a) Wane zarafi ne Yesu ya ba Bitrus har sau uku? (b) Wane tabbaci ne Yesu ya ba da don ya nuna cewa ya gafarta wa Bitrus?
26 Yesu ya tambayi Bitrus in yana ƙaunar Ubangijinsa ‘fiye da wannan,’ wato kifin da suka kama. Shin Bitrus ya fi son aikin sū, maimakon Yesu? Kamar dai yadda Bitrus ya musunci Ubangijinsa sau uku, Yesu ya ba shi zarafin nuna yadda yake ƙaunarsa sau uku a gaban mabiyansa. Sa’ad da Bitrus ya yi hakan, Yesu ya gaya masa yadda zai nuna wannan ƙaunar. Zai yi hakan ta wajen sa bautar Jehobah a kan gaba da ciyar da kuma ƙarfafa amintattun mabiyansa.—Luk 22:32; Yoh. 21:15-17.
27 Da hakan, Yesu ya kasance da tabbaci cewa har ila Bitrus yana da amfani a gare shi da kuma Ubansa. Bitrus zai kasance da matsayi mai tamani a ikilisiyar da Kristi ke ja-gora. Wannan cikakken tabbaci ne cewa Yesu ya gafarta wa Bitrus! Babu shakka, Bitrus ya yi hamdala cewa Yesu ya gafarta masa kuma ya koyi darasi daga kuskurensa.
28. Ta yaya Bitrus ya cika sunansa?
28 Bitrus ya yi hidimarsa shekaru da yawa cikin aminci. Ya ƙarfafa ’yan’uwansa kamar yadda Yesu ya umurce shi a dare na ƙarshe da yi a duniya. Bitrus ya ƙarfafa da kuma ciyar da mabiyan Kristi cikin haƙuri da kuma tawali’u. Ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi kamar dutse kuma ya kafa wa ’yan’uwa a cikin ikilisiya misali mai kyau kamar yadda Yesu ya faɗa sa’ad da ya ba shi suna Bitrus, wanda yake nufin Dutse. Wasiƙu biyu da ya rubuta da aka saka cikin Littafi Mai Tsarki sun kuma tabbatar da hakan. Waɗannan wasiƙun sun nuna cewa Bitrus bai taɓa manta da darasin da ya koya daga wurin Yesu game da gafartawa ba.—Karanta 1 Bitrus 3:8, 9; 4:8.
29. Ta yaya za mu iya yin koyi da bangaskiyar Bitrus da kuma jin ƙan Ubangijinsa?
29 Ya kamata mu ma mu koyi wannan darasin. Shin muna neman gafarar Allah kullum don kurakuranmu kuwa? Shin mun amince cewa ya gafarta mana kuma zai tsarkake mu? Kuma shin muna gafarta wa waɗanda suke tare da mu kuwa? Idan muka yi hakan, za mu yi koyi da bangaskiyar Bitrus da kuma jin ƙan Ubangijinsa.