NA 1
SASHEKu Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
‘Shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamace ya yi su.”
Jehobah * Allah ne ya ɗaura aure na farko. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa shi ya halicci mace ta farko kuma “ya kawo ta wurin mutumin.” Hakan ya faranta wa Adamu rai sosai, sai ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana.” (Farawa 2:22, 23) Har wa yau, Jehobah yana so mutane su ji daɗin aurensu.
Kana iya ganin kamar bayan ka yi aure kome zai tafi sumul. A gaskiya, ma’aurata da suke ƙaunar juna sosai ma suna iya samun matsala a wasu lokatai. (1 Korintiyawa 7:28) A cikin wannan ƙasidar, akwai ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da idan ka bi su, za ka ji daɗin aurenka kuma iyalinka za su zauna lafiya.—Zabura 19:8-11.
1 KU RIƘE MATSAYIN DA JEHOBAH YA BA KU
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Miji ne shugaban iyali.—Afisawa 5:23.
Idan kana da aure, Jehobah yana so ka kula da matarka da kyau. (1 Bitrus 3:7) Ya halicce ta a matsayin mataimakiya, kuma yana so ka ƙaunace ta kuma ka mutunta ta. (Farawa 2:18) Wajibi ne ka ƙaunaci matarka sosai kuma ka sa bukatunta gaba da naka.—Afisawa 5:25-29.
Idan ke matar aure ce, Jehobah yana so ki daraja mijinki sosai kuma ki taimaka masa ya cika hakkinsa da kyau. (1 Korintiyawa 11:3; Afisawa 5:33) Ki bi shawararsa kuma ki ba shi haɗin kai da dukan zuciyarki. (Kolosiyawa 3:18) Idan kika yi hakan, za ki kasance da daraja sosai a wurin mijinki da kuma Jehobah.
SHAWARA:
-
Ka tambayi matarka me ya kamata ka yi don ka zama maigida na kirki. Ka saurare ta sosai kuma ka ƙoƙarta ka yi gyara
-
Ka kasance da haƙuri. Zai ɗan ɗauki lokaci kafin ku fahimci yadda za ku riƙa faranta wa juna rai
2 KA MAI DA HANKALI GA ABIN DA KE DAMUN MATARKA
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Ka sa bukatun matarka gaba da naka. (Filibiyawa 2:3, 4) Ka mutunta matarka kuma ka tuna cewa Jehobah ya bukaci kowane bawansa ya “zama salihi ga kowa.” (2 Timotawus 2:24, Littafi Mai Tsarki) Yin “magana da garaje” yana kama da “sussukan takobi. Amma harshen mai-hikima lafiya ne.” Saboda haka, ka lura da kalaman da kake furtawa. (Misalai 12:18) Ruhu mai tsarki zai taimake ka ka yi magana mai daɗin ji kuma cikin ƙauna.—Galatiyawa 5:22, 23; Kolosiyawa 4:6.
SHAWARA:
-
Ka roƙi Allah ya taimake ka ka guji yin fushi da kuma manne wa ra’ayinka sa’ad da kai da matarka kuke tattauna batutuwa masu muhimmanci
-
Ka yi tunani sosai a kan abin da za ka faɗa da kuma yadda za ka faɗe shi
3 KU TSAI DA SHAWARA TARE
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Bayan aure, kai da matarka kun zama “nama ɗaya.” (Matta 19:5) Duk da haka, kowannenku yana da ra’ayinsa. Saboda haka, kuna bukatar ku yi ƙoƙari ku daidaita tunaninku da kuma yadda kuke ji. (Filibiyawa 2:2) Yana da muhimmanci ku tsai da shawara tare. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane ƙuduri a bisa shawara ya kan kafu.” (Misalai 20:18) Ku riƙa bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da kuke tsai da shawara mai muhimmanci.—Misalai 8:32, 33.
SHAWARA:
-
Ka ga wa matarka abin da ke zuciyarka, ba kawai ku yi taɗi ko kuma ka gaya mata ra’ayinka ba
-
Ka nemi ra’ayin matarka kafin ka tsai da shawara
^ sakin layi na 4 Jehovah is the name of God as revealed in the Bible.