Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA BIYU

Alhini—Muna Fuskantar Takura a Kowane Bangare

Alhini—Muna Fuskantar Takura a Kowane Bangare

Wata ’yar’uwa mai suna June ta ce: “Ni da mijina mun kashe aurenmu bayan shekara ashirin da biyar. Yarana sun daina bauta wa Jehobah. Na yi fama da cututtuka masu tsanani dabam-dabam. Sai na soma baƙin ciki sosai. Na rasa abin da yake yi mini daɗi a duniyar nan kuma na karaya. Na daina halartar taro da kuma fita wa’azi.”

ALHINI yana shafan kowa, har da masu bauta wa Allah. Marubucin zabura ya ce: “Sa’ad da nake alhini, ina cikin damuwa.” (Zabura 94:19, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya ce a kwanaki na ƙarshe “shagulgula na wannan rai” zai iya sa bauta wa Jehobah ya kasance da wuya. (Luka 21:34) Hakan ya shafe ka? Matsalar kuɗi ko damuwa ta iyali ko kuma rashin lafiya yana ci maka tuwo a ƙwarya ne? Ta yaya Jehobah zai taimaka maka ka jimre?

Mafificin Iko

Muna bukatar taimako don mu jimre alhini. Manzo Bulus ya ce: “Mun matsu ga kowane sashe, amma ba mu ƙuntata ba; mun damu, amma bai kai fid da zuciya ba; . . . an fyaɗa mu a ƙasa, amma ba a halaka mu ba.” Wane ne yake ba mu ƙarfin juriya sa’ad da muke alhini? Jehobah Allah Maɗaukakin Sarki ne yake tanadar mana da “mafificin . . . iko.”—2 Korintiyawa 4:7-9.

Ka tuna da yadda ka amfana daga “mafificin . . . iko” da Allah yake bayarwa. Wataƙila, wani jawabi mai ban ƙarfafa ya sa ka ƙara fahimtar yadda Jehobah yake ƙaunarka. Ko kuma sa’ad da ka yi wa mutane wa’azi ka ƙara kasance da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa game da Aljanna. Sa’ad da muka halarci taron Kirista kuma muka yi wa wasu wa’azi, muna samun ƙarfin jure matsaloli. Ƙari ga haka, muna samun kwanciyar hankali kuma hakan yana taimaka mana mu bauta wa Jehobah da farin ciki.

‘Ka Ɗanɗana, Ka Duba, Ubangiji Nagari Ne’

Hakika, mukan fuskanci matsaloli dabam-dabam a lokaci ɗaya. Alal misali, Jehobah ya ce mu biɗi Mulkinsa farko a rayuwarmu kuma mu ci gaba da yin ayyukan da suka shafi ibada. (Matta 6:33; Luka 13:24) Shin idan hamayya daga wurin waɗanda suke cikin iyali da abokan aiki, da rashin lafiya ko kuma matsalolin iyali suna hana ka yin wasu ayyukan ibada fa? Idan ba ka sami lokaci da kuma ƙarfin zuwa taro saboda aikin da kake yi fa? Hakika, yawan hidimomi da bukatu za su iya jawo maka baƙin ciki. Wataƙila kana tunani cewa Jehobah yana bukatar ka yi abubuwan da suka fi ƙarfinka.

Jehobah ya fahimci yanayinmu kuma ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Ƙari ga haka, ya san cewa zai ɗauki lokaci kafin mu sake samun ƙarfi da kuma halin bauta masa yadda ya kamata.—Zabura 103:13, 14.

Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya kula da annabi Iliya. Sa’ad da Iliya ya yi sanyin gwiwa kuma ya tsorata, sai ya gudu zuwa daji. Shin Jehobah ya tsauta masa kuma ya tilasta masa ya koma aikinsa ne? A’a. Sau biyu, Jehobah ya aika mala’ika zuwa wurinsa. Mala’ikan ya ta da shi daga barci kuma ya ba shi abinci don ya ci. Duk da haka, bayan kwanaki 40 Iliya bai daina fargaba da tsoro ba. Mene ne Jehobah ya ƙara yi don ya taimaka masa? Na ɗaya, Jehobah ya nuna masa cewa zai iya kāre shi. Na biyu, Jehobah ya yi wa Iliya magana da “ƙaramar murya marar-ƙarfi” don ya ƙarfafa shi. A ƙarshe, Jehobah ya bayyana wa Iliya cewa akwai dubban mutane da suke bauta masa da aminci. Ba da daɗewa ba bayan haka, Iliya ya koma yin aikinsa da himma. (1 Sarakuna 19:1-19) Wane darasi ne hakan ya koya mana? Sa’ad da Iliya yake baƙin ciki sosai, Jehobah ya bi da shi da haƙuri da kuma tausayi. Jehobah bai canja ba. Yana ƙaunarmu kamar yadda ya ƙaunaci Iliya.

Ka yi tunani a kan abin da za ka iya ba wa Jehobah. Kada ka gwada abin da kake yi a yau da abin da ka yi a dā. Alal misali: Mai tsere da ya daina tsere na tsawon watanni ko shekaru ba zai tashi dare ɗaya ya soma tsere kamar yadda yake yi a dā ba. A maimakon haka, zai soma tsere kaɗan-kaɗan kuma a hankali zai sake samun ƙarfi yin tsere kamar dā. Kiristoci suna tseren rai kuma suna horar da kansu don su cim ma wannan maƙasudin. (1 Korintiyawa 9:24-27) Hakazalika, zai dace ka kafa maƙasudi da za ka iya cim ma a yanzu. Alal misali, za ka iya kafa maƙasudin halartan wani taron ikilisiya. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka cim ma maƙasudinka. Yayin da kake samun ƙarfafa, ka ‘ɗanɗana, ka duba’ kuma za ka gane cewa “Ubangiji nagari ne.” (Zabura 34:8) Ka tuna cewa duk abin da ka yi don ka nuna ƙaunarka ga Jehobah, ko da a ganinka, abin bai taka kara ya karya ba, yana da muhimmanci a gaban Jehobah.—Luka 21:1-4.

Jehobah ba ya bukatar mu yi abin da ya fi karfinmu

“Abin da Ya Ƙarfafa Ni”

Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa ’yar’uwa June ta soma bauta masa da ƙwazo kamar yadda ta yi a dā? Ta ce: “Na yi ta yin addu’a ga Jehobah kuma na roƙe shi ya taimake ni. Daga baya, surkuwata ta gaya min cewa za a yi wani babban taro a garin da muke. Sai na halarci taron na kwana ɗaya kawai. Na yi farin ciki sosai da na sake tarayya da Shaidun Jehobah. Taron ne abin da ya ƙarfafa ni. Yanzu haka, ina bauta wa Jehobah da farin ciki! Rayuwa tana da ma’ana a gare ni. Na gane cewa ina bukatar ’yan’uwana maza da mata kuma ya dace in amince da taimakonsu. Ina godiya cewa na sami zarafin dawowa.”