BABI NA 38
Abin da Ya Sa Za Mu Kaunaci Yesu
KA YI tunanin kana cikin jirgin ruwa da yake nitsewa. Za ka so wani ya cece ka?— To, idan wani ya ba da ransa domin ya cece ka fa?— Haka Yesu Kristi ya yi. Kamar yadda muka koya a Babi na 37, ya ba da ransa fansa domin mu tsira.
Hakika, Yesu ba daga nitsewa ya cece mu ba. Daga menene ya cece mu? Ka tuna?— Daga zunubi da kuma mutuwa da muka gada daga wurin Adamu. Ko da yake wasu mutane sun yi munanan abubuwa ƙwarai, Yesu ya mutu dominsu ma. Za ka ɗauki kasada haka domin ka cece irin waɗannan miyagun mutane?—
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da ƙyar wani za ya yarda ya mutu sabili da mutum mai-adalci; wataƙila dai sabili da nagarin mutum wani ya yi ƙarfin hali har shi mutu.” Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa Yesu ya “mutu domin marasa-ibada.” Wannan ya haɗa da mutane ma da ba sa bauta wa Allah! Littafi Mai Tsarki ya ci gaba da cewa: “Tun muna masu-zunubi [muna miyagun abubuwa] tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.”—Romawa 5:6-8.
Za ka iya tuna wani manzon da ya taɓa yin mugun abu?— Manzon ya rubuta: “Kristi Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu-zunubi; cikinsu kuwa ni ne babba.” Manzo Bulus ne ya faɗi haka. Ya ce ya taɓa kasancewa “marasa-wayo” kuma ya ci gaba cikin “ƙeta.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; 1 Timothawus 1:15; Titus 3:3.
Ka yi tunanin yawan ƙaunar da Allah yake da ita da ta sa ya aiko Ɗansa ya mutu domin irin waɗannan mutane! Don Allah ka ɗauki Littafi Mai Tsarki naka mu karanta game da wannan a cikin Yohanna sura 3, aya ta 16. Nan ta ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya [wato, mutane da suke zama cikin duniya] har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.”
Yesu ya nuna cewa yana ƙaunarmu kamar yadda Ubansa yake ƙaunarmu. Za ka tuna cewa a Babi na 30 na wannan littafin, mun karanta game da wuyar da Yesu ya sha a daren da aka kama shi. An kai shi gidan Babban Firist Kayafa, a nan aka tuhumce shi. Aka kawo ’yan shaidar zur su yi ƙarya game da Yesu, kuma mutanen suka naushe shi. Sa’an nan ne Bitrus ya yi musun sanin Yesu. Yanzu bari mu yi kamar muna wurin muna ganin abin da yake faruwa.
Safiya ta yi. Yesu bai yi barci ba daddare. Domin tuhuma ta daren ba gaskiya ba ce, firistoci ɗin suka tara ’yan Majalisa, ko kuma babban kotun Yahudawa, suka sake tuhumarsa. A nan ma suka sake zargin Yesu da yi wa Allah laifi.
Sai firistoci ɗin suka sa a ɗaure Yesu aka kai shi ga Bilatus, gwamna daga Roma. Suka gaya wa Bilatus cewa: ‘Yesu yana hamayya da gwamnati. Ya kamata a kashe shi.’ Amma Bilatus ya fahimci cewa firistocin ƙarya suke yi. Saboda haka, Bilatus ya gaya musu: ‘Ni ban ga wani laifi da wannan mutum ya yi ba. Zan sallame shi.’ Sai firistocin da wasu suka ce da babbar murya: “A’a! Ka kashe shi!’
Daga baya, Bilatus ya yi ƙoƙari ya gaya wa mutanen cewa zai ƙyale Yesu. Amma firistocin suka sa mutane suka yi ta kuwwa: ‘Idan ka bar shi kai ma kana hamayya da gwamnati! Ka kashe shi!’ Jama’ar ta yi ta surutu. Ka san abin da Bilatus ya yi?—
Ya yi abin da suke so. Da farko ya sa aka yi wa Yesu bulala. Sai ya saka shi a hannun sojoji su kashe shi. Suka yi wa Yesu rawani da ƙaya suka ta yi masa ba’a suna durƙusawa a gabansa. Sai suka ba wa Yesu babban sanda ko kuma gungume ya ɗauka suka fita da shi bayan
gari zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai. A nan suka buga wa Yesu ƙusa a hannun da ƙafa a kan gungume. Sai suka ɗaga suka tsayar da gungumen, Yesu ya kasance a rataye. Jininsa yana zuba. Zafi kuma ya yi ƙuna.Yesu bai mutu a take ba. Yana rataye a wurin. Manyan firistoci suka yi masa ba’a. Waɗanda suke wucewa kuma suka ce: ‘Idan kai ɗan Allah ne, ka sauko daga kan gungumen!’ Amma Yesu ya san abin da Ubansa ya aiko shi ya yi. Ya sani cewa dole ne ya ba da kamiltaccen ransa saboda mu mu sami damar samun rai na har abada. A ƙarshe, daidai ƙarfe uku na rana, Yesu ya yi wa Ubansa kuka kuma ya mutu.—Matta 26:36–27:50; Markus 15:1; Luka 22:39–23:46; Yohanna 18:1–19:30.
Yesu ya bambanta da Adamu ƙwarai. Adamu bai nuna yana ƙaunar Allah ba. Ya yi wa Allah rashin biyayya. Adamu kuma bai nuna yana ƙaunarmu ba. Domin ya yi zunubi, dukanmu an haife mu cikin zunubi. Amma Yesu ya nuna yana ƙaunar Allah kuma yana ƙaunarmu. Ya yi wa Allah biyayya. Kuma ya ba da ransa domin ya kawar da ƙeta da Adamu ya yi mana.
Kana godiya domin wannan abu mai ban mamaki da Yesu ya yi?— Sa’ad da kake wa Allah addu’a, kana yi masa godiya domin ya ba mu Ɗansa?— Manzo Bulus ya yi godiya domin abin da Kristi ya yi dominsa. Bulus ya rubuta cewa Ɗan Allah “ya ƙaunace ni, ya ba da kansa kuma domina.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Galatiyawa 2:20.) Yesu ya mutu dominmu. Ya bayar da kamiltaccen ransa saboda mu sami rai na har abada! Hakika wannan dalili ne mai ƙarfi da ya kamata mu yi ƙaunar Yesu.
Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci da suke birnin Koranti: ‘Ƙaunar Kristi ta motsa mu ga aiki.’ Wane irin aiki ne ya kamata ƙaunar Kristi ta motsa mu mu yi? Me kake tsammani?— Ka lura da amsar Bulus: “Kristi ya mutu domin kowa saboda su rayu dominsa. Ba za su rayu domin su faranta wa kansu rai ba.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; 2 Korinthiyawa 5:14, 15; New Life Version.
Za ka iya tunanin hanyoyi da za ka nuna cewa rayuwarka domin ka faranta wa Kristi rai ne?— Hanya ɗaya ta wajen gaya wa wasu abin da ka koya game da shi ne. Ko kuma ka yi tunani game da wannan: Za ka iya kaɗaita, saboda kada mamarka da babanka su ga abin da kake yi, babu mutumin da zai iya ganin abin da kake yi. Za ka kalli wani abu a telibijin ko kuma wataƙila wani abu a Intane da ka sani cewa ba zai faranta wa Yesu rai ba?— Ka tuna cewa Yesu yana da rai kuma yana ganin dukan abin da muke yi!
Wani dalilin da ya sa ya kamata mu ƙaunaci Yesu shi ne domin muna so mu yi kwaikwayon Jehovah. “Uba yana ƙauna ta,” in ji Yesu. Ka san abin da ya sa yake ƙaunar Yesu, da kuma abin da ya sa ya kamata mu ma mu ƙaunace shi?— Domin Yesu yana shirye ya mutu domin a yi nufin Allah. (Yohanna 10:17) Saboda haka, bari mu yi abin da Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunace ku, ya bada kansa kuma domin ku.”—Afisawa 5:1, 2.
Domin mu ƙara godiya ga Yesu domin abin da ya yi saboda mu, don Allah ka karanta Yohanna 3:35; 15:9, 10; da kuma 1 Yohanna 5:11, 12.