BABI NA 10
Ikon Yesu a Kan Aljanu
KA TUNA dalilin da ya sa mala’ikan Allah ya zama Shaiɗan Iblis?— Muradinsa ne na son a bauta masa ya sa ya juya wa Allah baya. Wasu mala’iku sun zama mabiyan Shaiɗan ne?— Hakika, sun bi shi. Littafi Mai Tsarki ya kira su ‘mala’ikun Shaiɗan,’ ko kuma aljanu.—Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Waɗannan miyagun mala’iku, ko kuma aljanu, sun yarda da Allah ne?— ‘Aljanu sun yarda da cewa da akwai Allah,’ in ji Littafi Mai Tsarki. (Yaƙub 2:19) Amma yanzu suna jin tsoro. Domin sun sani cewa Allah zai yi musu horo domin miyagun abubuwa da suka yi. Menene suka yi da ba shi da kyau?—
Littafi Mai Tsarki ya ce waɗannan mala’ikun sun bar ainihin wajen zamansu a sama suka zo duniya suka zauna tare da mutane. Sun yi wannan ne domin suna so su yi jima’i da mata kyawawa da suke duniya. (Farawa 6:1, 2; Yahuda 6) Menene ka sani game da jima’i?—
Jima’i sa’ad da namiji da tamace suka yi kusa ne a hanya ta musamman. Daga baya, jariri zai yi girma a cikin macen. Amma mala’iku su yi jima’i ba daidai ba ne. Allah yana son mata da miji ne kawai waɗanda suka yi aure su yi jima’i. Ta haka idan aka haifi jariri, mata da mijin za su kula da jaririn.
Da mala’ikun suka ɗauki jikin mutane suka yi jima’i da mata a duniya, jariransu suka yi girma suka fi mutane. Masu ƙeta ne kuma sun ji wa mutane. Sai Allah ya kawo ambaliya ta halaka waɗannan da kuma miyagun mutane. Amma ya sa Nuhu ya ƙera jirgi, ko kuma babban jirgin ruwa, ya ceci mutane kaɗan da suka yi abin da yake da kyau. Babban Malami ya ce abin da ya faru a Rigyawar yana da muhimmanci mu tuna da shi.—Farawa 6:3, 4, 13, 14; Luka 17:26, 27.
Da ambaliyar ta zo, ka san abin da ya faru da miyagun mala’ikun?— Suka daina amfani da jikin mutane da suka yi, suka koma sama. Allah bai karɓe su ba a kan mala’ikunsa, sai suka zama mala’ikun Shaiɗan, ko aljanu. Kuma menene ya faru da ’ya’yan
nasu?— Sun mutu a cikin Rigyawar. Kuma haka dukan sauran mutane da ba su yi wa Allah biyayya ba.Tun daga lokacin ambaliyar, Allah bai sake ƙyale aljanun su zama kamar mutane ba kuma. Amma ko da yake ba za mu iya ganinsu ba, aljanun suna ƙoƙarin su sa mutane su yi abubuwa da suke miyagu. Sun haddasa masifa fiye da dā. Hakan domin an jefo su ne daga sama zuwa duniya.
Ka san abin da ya sa ba za mu iya ganin aljanun ba a nan?— Domin su ruhohi ne. Amma za mu iya tabbata cewa suna raye. Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan yana ‘ruɗin mutane a dukan duniya,’ kuma aljanunsa suna taimakonsa.—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.
Shin Iblis da aljanunsa za su iya ruɗinmu ne, ko kuma su yi mana wayo?— E, za su iya idan ba mu mai da hankali ba. Amma ba ma bukatar mu ji tsoro. Babban Malami ya ce: ‘Iblis ba shi da kome cikina.’ Idan muka kusaci Allah, zai kāre mu daga Iblis da kuma aljanunsa.—Yohanna 14:30.
Yana da muhimmanci mu san abubuwa marasa kyau da aljanu za su iya ƙoƙarin su sa mu yi. Saboda haka ka yi tunani game da shi. Wane abu ne marar kyau aljanun suka yi da suka zo duniya?— Kafin Rigyawar, sun yi jima’i da mata, abin da bai kamata ba ga mala’iku. A yau aljanu suna so idan mutane ba su yi biyayya ba ga dokar Allah game da jima’i. Bari in tambaye ka, su waye ne kawai ya kamata su yi jima’i?— Gaskiyarka, masu aure ne kawai.
A yau wasu yara maza da mata suna yin jima’i, amma hakan ba shi da kyau. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da al’aurar namiji ko kuma azzakari. (Kubawar Shari’a 23:1) Al’aurar tamace ana kiranta farji. Jehovah ya halicci waɗannan ɓangaren jiki domin dalili na musamman da masu aure ne kawai ya kamata su more su. Yana sa aljanun su yi farin ciki sa’ad da mutane suka yi abubuwa da Jehovah ya hana. Alal misali, aljanun suna so yaro da yarinya su yi wasa da azzakari ko kuma farjin juna. Ba ma son mu faranta wa aljanu rai, ko ba haka ba?—
Har yanzu da akwai abin da aljanun suke so da Jehovah ba ya so. Ka san ko menene wannan?— Faɗa. (Zabura 11:5) Faɗa shi ne lokacin da mutane suka zama masu ƙeta suka bugi wasu. Ka tuna cewa abin da ’ya’yan aljanun suka yi ke nan.
Aljanun kuma suna so su tsoratar da mutane. Wani lokaci suna likimo cewa su mutane da suka mutu ne. Suna iya kwaikwayon muryar mutane ma da sun riga sun mutu. A wannan hanyar aljanun suna ruɗin mutane da yawa su yarda cewa mutane da suka mutu suna da rai kuma za su iya magana da rayayyu. Hakika, aljanu suna sa mutane da yawa su yarda da fatalwa.
Saboda haka dole ne mu mai da hankali kar Shaiɗan da aljanunsa su ruɗe mu. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: ‘Shaiɗan yana ƙoƙarin 2 Korinthiyawa 11:14, 15) Amma a gaskiya, aljanu miyagu ne. Bari mu ga yadda za su yi ƙoƙarin su sa mu zama kamarsu.
ya sa kansa ya zama kamar mala’ikan kirki, kuma bayinsa suna yin haka su ma.’ (A ina ne mutane suke koyo game da faɗa da jima’i da bai dace ba da ruhohi da kuma fatalwa?— Ba daga kallon wasannin telibijin, da zuwan gidan siliman ko kuma miyagun abokai a makaranta ba? Yin waɗannan abubuwa suna kawo mu kusa da Allah ne ko kuma kusa da Iblis da aljanunsa? Me ka ce?—
Wa kake tsammani yake so mu saurari kuma mu kalli abin da ba shi da kyau?— Haka ne, Shaiɗan ne da aljanunsa. To, me ya kamata ni da kai mu yi?— Muna bukatar mu karanta, mu saurari, kuma mu kalli abubuwa masu kyau da za su taimake mu mu bauta wa Jehovah. Za ka iya tuna wasu cikin waɗannan abubuwa masu kyau da za mu yi?—
Idan muka yi abin da yake da kyau, ba mu da dalilin jin tsoron aljanu. Yesu ya fi su ƙarfi, kuma suna tsoronsa. Akwai ranar da aljanun suka yi wa Yesu kuka: “Ka zo domin ka halaka mu?” (Markus 1:24) Ba za mu yi farin ciki ba ne idan lokaci ya zo domin Yesu ya halaka Shaiɗan da aljanunsa?— A yanzu, za mu tabbata cewa Yesu zai kāre mu daga aljanu idan muka kasance kusa da shi da kuma Ubansa na sama.
Bari mu karanta game da abin da muke bukatar mu yi a 1 Bitrus 5:8, 9 da kuma Yaƙub 4:7, 8.