Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 16

Mene ne Yake Da Muhimmancin Gaske?

Mene ne Yake Da Muhimmancin Gaske?

Wace matsala wannan mutumin yake da ita?

DA AKWAI mutumin da ya zo wurin Yesu wata rana. Ya san cewa Yesu yana da hikima sosai, domin haka ya ce masa: ‘Malam, ka gaya wa ɗan’uwana ya ba ni wasu abubuwa da yake da su.’ Mutumin yana tunanin cewa ya kamata ya sami wasu cikin abubuwan.

Da kai ne Yesu, da me za ka ce?— Yesu ya lura cewa mutumin yana da matsala. Matsalarsa ba ta bukatar abin ɗan’uwan nasa ba ne. Matsalarsa ita ce bai san ainihin abin da yake da muhimmanci a rayuwa ba.

Bari mu yi tunani game da wannan. Menene ya kamata ya zama abu mafi muhimmanci a gare mu? Ya kamata ne mu sami abin wasa mai kyau, sababbin kaya, ko kuma irin waɗannan abubuwa?— A’a, akwai abubuwa mafi muhimmanci. Kuma wannan ne darasin da Yesu yake so ya koyar. Saboda haka, ya ba da labarin wani mutumin da ya mance da Allah. Kana so ka ji labarin?—

Wannan mutumin yana da dukiya mai yawa. Yana da filaye da rumbuna. Abin da ya shuka suka yi girma da kyau. Ba shi da wuri a cikin rumbunansa da zai yi ajiyar dukan abin da ya girbe. To, menene zai yi? Sai ya ce wa kansa: ‘Zan rushe rumbunana in gina manya. Sai in ajiye abin da na girbe da dukan abubuwana masu kyau a cikin sababbin rumbunan.’

Mai arziki yana tsammani wannan shi ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ya yi. Yana tsammanin yana da wayo sosai a ajiyar abubuwa da yawa. Ya ce wa kansa: ‘Ina da abubuwa da yawa da na ajiye. Za su biya bukatata na shekaru da yawa. Yanzu zan iya hutawa. Zan ci in sha, in more rayuwata.’ Amma tunanin mutumin ba daidai ba ne. Ka san abin da ya sa?— Yana tunani ne game da kansa da farin cikinsa kawai. Ya mance da Allah.

Menene wannan mai arziki yake tunaninsa?

Saboda haka Allah ya yi magana da mutumin. Ya ce masa: ‘Kai wawan mutum. Da daren nan za ka mutu. Yanzu wa zai mallaki abubuwan da ka tara?’ Mutumin zai iya amfani da abubuwan ne bayan ya mutu?— A’a, wani dabam zai mallake su. Yesu ya ce: “Hakanan ne mai-ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.”—Luka 12:13-21.

Na san ba ka so ka zama kamar wannan mai arzikin, ko kana so ne?— Abu mai muhimmanci a rayuwarsa shi ne tara abin duniya. Wannan kuskure ne. Koyaushe yana bukatar ƙari. Amma ba “mawadaci ba ne ga Allah.”

Mutane da yawa kama suke da wannan mai arzikin. Koyaushe suna bukatar ƙari. Amma haka zai iya kawo manyan matsaloli. Alal misali, kana da abin wasa?— Wane irin abin wasa kake da shi? To, idan wani abokinka yana da kwallo, ko mota, ko wani abin wasa da ba ka da shi. Daidai ne ka sa iyayenka su saya maka?—

Da akwai lokacin da abin wasa zai kasance kamar ya fi muhimmanci. Amma me zai faru bayan ɗan lokaci?— Zai tsufa. Zai lalace, ba za ka so shi ba ma a lokacin. Hakika, kana da wani abu wanda ya fi abin wasa tamani. Ka san wannan abin?—

Menene kake da shi da ya fi abin wasa muhimmanci?

Ranka. Ranka yana da muhimmanci ƙwarai domin idan ba tare da shi ba, ba za ka iya yin kome ba. Amma rayuwarka ta dangana ne a kan yin abin da zai faranta wa Allah rai, ko ba haka ba ne?— Saboda haka, kada mu zama kamar wawan mai arziki da ya mance da Allah.

Ba yara ba ne kawai za su iya yin irin wannan wauta na mai arzikin. Manyan mutane ma da yawa suna yin haka. Wasu koyaushe suna neman fiye da abin da suke samu. Wataƙila suna da abinci da za su ci, tufafi da za su saka, da kuma gida da za su zauna. Amma suna bukatar ƙari. Suna bukatar tufafi da yawa. Kuma suna bukatar manyan gidaje. Waɗannan abubuwa suna bukatar kuɗi. Saboda haka, suna aiki sosai domin su samu kuɗi da yawa. Muddin sun samu kuɗi, haka nan za su nemi ƙarinsa.

Wasu manyan mutane suna ƙoƙarin su sami kuɗi har ba su da lokaci na zama da iyalinsu. Kuma ba su da lokacin bauta wa Allah. Kuɗinsu zai iya rayar da su ne?— A’a, ba zai iya ba. Za su iya amfani da kuɗinsu ne bayan sun mutu?— A’a. Wannan domin matattu ba sa iya yin kome.—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Amma wannan yana nufi ne cewa ba shi da kyau mu sami kuɗi?— A’a. Za mu iya sayan abinci da kuma tufafi da kuɗi. Littafi Mai Tsarki ya ce kāriya ce. (Mai-Wa’azi 7:12) Idan muna son kuɗi, to lallai za mu sami matsaloli. Za mu zama kamar mai arzikin da ya tara dukiya amma ba shi da wadata wurin Allah.

Menene yake nufi a kasance da wadata wurin Allah?— Yana nufin mu saka Allah farko a rayuwarmu. Wasu mutane sun ce sun gaskata da Allah. Suna tunanin cewa gaskatawa ne kawai abin da ake bukata. Amma suna da wadata wurin Allah ne?— A’a, suna kama da mai arzikin da ya mance da Allah.

Yesu bai taɓa manta da Ubansa na samaniya ba. Bai yi ƙoƙarin ya tara kuɗi ba. Kuma bai mallaki abubuwa da yawa ba. Yesu ya san abin da yake da muhimmanci a rayuwa. Ka san abin da yake da muhimmanci a rayuwa?— Wadata wurin Allah.

Menene wannan yaron yake yi da yake da muhimmanci da gaske?

Ka gaya mini, ta yaya za mu wadata wurin Allah?— Ta yin abin da yake faranta masa rai. Yesu ya ce: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:29) Allah yana farin ciki sa’ad da muka yi abin da yake so mu yi. Yanzu ka gaya mini, waɗanne abubuwa za ka yi ka faranta wa Allah rai?— Hakika, za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki, ka riƙa zuwa taron Kirista, ka yi addu’a ga Allah, ka taimaki wasu su koyi game da Allah. Waɗannan lallai abubuwa ne masu muhimmanci a rayuwa.

Domin Yesu ya wadata wurin Allah, Jehovah ya kula da shi. Ya ba Yesu ladar rayuwa har abada. Idan mun yi yadda Yesu ya yi, Jehovah zai ƙaunace mu kuma ya kula da mu. Domin haka, bari mu zama kamar Yesu kuma kada mu zama kamar mai arziki wanda ya mance da Allah.

Ga wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda ma kasance da ra’ayi mai kyau game da abin duniya: Misalai 23:4; 28:20; 1 Timothawus 6:6-10; da kuma Ibraniyawa 13:5.