BABI NA 43
Su Waye Ne ’Yan’uwanmu?
WATA rana Babban Malami ya yi tambaya mai ban mamaki. Ya ce: “Wace ce uwata? Su wanene kuma ’yan’uwana?” (Matta 12:48) Za ka iya amsa waɗannan tambayoyi?— Wataƙila ka sani cewa Maryamu ce mamar Yesu. Amma ka san sunayen ’yan’uwansa maza?— Yana da ’yan’uwa mata ne?—
Littafi Mai Tsarki ya ce sunayen ƙannen Yesu su ne “Yaƙub, da Yusufu, da Siman, da Yahuda.” Kuma Yesu yana da ’yan’uwa mata waɗanda suke raye sa’ad da yake wa’azi. Tun da Yesu ne ɗan fari, dukan waɗannan ƙannensa ne.—Matta 13:55, 56; Luka 1:34, 35.
’Yan’uwan Yesu ma almajiransa ne?— Littafi Mai Tsarki ya ce da farko “ba su bada gaskiya gareshi ba.” (Yohanna 7:5) Amma daga baya, Yakubu da Yahuda suka zama almajiransa, har ma sun rubuta littattafai a Littafi Mai Tsarki. Ka san littattafai da suka rubuta?— Sun rubuta, Yaƙub da Yahuda.
Ko da yake ba a faɗi sunan ’yan’uwan Yesu mata ba a cikin Littafi Mai Tsarki, mun sani cewa yana da aƙalla ƙanne mata guda biyu. Yana yiwuwa su fi haka yawa. Waɗannan ’yan’uwansa mata sun zama mabiyansa ne?— Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba, saboda haka, ba mu sani ba. Amma ka san abin da ya sa Yesu ya yi wannan tambayar, “Wace ce uwata, su wanene kuma ’yan’uwana?”— Bari mu bincika.
Yesu yana koyar da almajiransa sa’ad da wani ya katse masa hanzari ya ce: “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje,
suna biɗa su yi magana da kai.” Saboda haka, Yesu ya yi amfani da wannan zarafi ya koyar da darasi mai muhimmanci ta yin wannan tambayar mai ban mamaki: “Wace ce uwata, Su wanene kuma ’yan’uwana?” Ya miƙa hannunsa ya nuna almajiransa ya amsa tambayar, yana cewa: “Ga uwata da ’yan’uwana!”Sa’an nan Yesu ya yi bayani game da abin da yake nufi, yana cewa: “Iyakar wanda za shi yi nufin Ubana wanda ke cikin sama, shi ne ɗan’uwana, da ’yar’uwata, da uwata.” (Matta 12:47-50) Wannan ya nuna yadda Yesu yake kusa da almajiransa. Yana koya mana cewa almajiransa daidai suke da ɗan’uwansa da ’yar’uwarsa da kuma mamarsa na zahiri.
A wannan lokacin ’yan’uwan Yesu—Yaƙub, Yusufu, da Siman, da Yahuda— ba su gaskata cewa Yesu ɗan Allah ba ne. Ba su gaskata da abin da mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa mamarsu ba. (Luka 1:30-33) Saboda haka, wataƙila ba su yi wa Yesu kirki ba. Dukan wanda yake haka ba ɗan’uwa ba ne da ’yar’uwa na gaske. Ka san wanda ba ya yi wa ɗan’uwansa ko ’yar’uwarsa kirki ba?—
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Isuwa da Yakubu kuma Isuwa ya yi fushi sosai ya ce: “In kashe ɗan’uwana Yakubu.” Mamarsu, Rifkatu ta tsorata ƙwarai ta sa aka tura Yakubu wani wuri saboda kada Isuwa ya kashe shi. (Farawa 27:41-46) Amma, bayan shekaru da yawa, Isuwa ya gyara halinsa ya rungumi Yakubu ya yi masa sumba.—Farawa 33:4.
Daga baya Yakubu ya haifi ’ya’ya 12. Amma ’ya’yan Yakubu manya ba sa ƙaunar ƙaninsu Yusufu. Suna kishinsa domin babansu ya fi ƙaunarsa. Saboda haka, suka sayar da shi ga masu sayan bayi da suke kan hanyarsu zuwa ƙasar Masar. Sa’an nan suka gaya wa babansu cewa naman daji ya kashe Yusufu. (Farawa 37:23-36) Wannan ba abin ƙyama ba ne?—
Daga baya ’yan’uwan Yusufu sun tuba daga abin da suka yi. Saboda haka, Yusufu ya gafarta musu. Ka
ga yadda Yusufu yake kama da Yesu?— Manzannin Yesu suka gudu sa’ad da yake cikin matsala, Bitrus ya yi musun saninsa. Duk da haka, kamar Yusufu, Yesu ya yafe musu duka.Da akwai kuma wa da ƙane, Kayinu da Habila. Za mu iya koyon darasi daga wannan ma. Allah ya ga zuciyar Kayinu cewa ba ya ƙaunar ƙanensa. Saboda haka, Allah ya gaya wa Kayinu ya canja al’amarinsa. Idan Kayinu yana ƙaunar Allah da gaske da ya saurare shi. Amma ba ya ƙaunar Allah. Wata rana Kayinu ya ce wa Habila: ‘Mu je cikin daji.’ Sai Habila ya bi Kayinu. Da suke cikin daji su kaɗai, Kayinu ya bugi ɗan’uwansa da ƙarfi sosai ya kashe shi.—Farawa 4:2-8.
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa da akwai darasi na musamman da ya kamata mu koya daga wannan. Ka san ko menene wannan?— ‘Wannan shi ne saƙon da ka ji da farko: Ya kamata mu yi ƙaunar juna; ba kamar Kayinu ba, da ya zama mugu.’ Saboda haka, ’yan’uwa ya kamata su yi ƙaunar juna. Kada su zama kamar Kayinu.—1 Yohanna 3:11, 12.
Me ya sa bai kamata mu so zama kamar Kayinu ba?— Domin Littafi Mai Tsarki ya ce ‘ya zo ne daga wurin mugu,’ Shaiɗan Iblis. Tun da Kayinu ya yi aikin Iblis, kamar Iblis ne babansa.
Ka ga abin da ya sa yake da muhimmanci ka ƙaunaci ’yan’uwanka?— Idan ba ka ƙaunace su ba, ’ya’yan waye kake kwaikwayo?— ’Ya’yan Shaiɗan. Ba za ka so ka yi haka ba, ko za ka so ne?— To ta yaya za ka tabbatar cewa kana so ka zama yaron Allah?— Ta wajen ƙaunar ’yan’uwanka ne da gaske.
Amma mecece ƙauna?— Ƙauna juyayi ce mai yawa da yake sa mu mu yi abin kirki ga wasu mutane. Muna nuna cewa muna ƙaunar wasu sa’ad da muka yi musu abin kirki. Amma su waye ne ’yan’uwanmu da ya kamata mu yi ƙaunarsu?— Ka tuna, Yesu ya
koyar cewa waɗanda suka taru ne suka kafa baban iyali na Kirista.Yaya muhimmancin mu yi ƙaunar ’yan’uwanmu yake?— Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa [ko ’yar’uwansa] ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yohanna 4:20) Saboda haka, ba za mu iya ƙaunar mutane kaɗan ba kawai a cikin iyali na Kirista. Dole ne mu ƙaunace su duka. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Kana ƙaunar dukan ’yan’uwa?— Ka tuna, idan ba ka yi haka ba, ba za ka yi ƙaunar Allah ba da gaske.
Ta yaya za mu nuna muna ƙaunar ’yan’uwanmu da gaske?— Idan muna ƙaunarsu ba za mu rabu da su ba domin ba ma so mu yi musu magana. Za mu kasance abokin dukansu. Za mu riƙa yi musu kirki ko da yaushe kuma mu raba abin da muke da shi da su. Kuma idan suka shiga wata matsala za mu taimaka musu domin da gaske mu babban iyali ne.
Sa’ad da muka ƙaunaci ’yan’uwanmu da gaske, menene wannan yake tabbatarwa?— Wannan yana tabbatar da cewa mu almajiran Yesu ne, Babban Malami. Ko ba abin da muke so mu zama ba ke nan?—
An tattauna yadda za mu nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu a Galatiyawa 6:10 da kuma 1 Yohanna 4:8, 21. Ka buɗe Littafi Mai Tsarki naka mu karanta waɗannan ayoyi?