BABI NA 11
Taimako Daga Malai’ikun Allah
WASU mutane suna cewa za su yarda da abin da kawai suke gani ne. Amma wannan wauta ce. Da akwai abubuwa da yawa da ba mu taɓa gani da idanunmu ba. Za ka iya gaya mini sunan ɗaya cikinsu?—
Iska da muke sheƙa fa? Za mu iya jin hucinta?— Ka ɗaga hannunka kuma ka hura. Kana jin wani abu?— Ka ji amma ba za ka iya ganin iskar ba, ko za ka iya ne?—
Mun riga mun yi magana a kan ruhohi da ba za mu iya ganinsu ba. Mun koyi cewa wasu masu nagarta ne wasu kuma miyagu. Ka gaya mini sunan wasu ruhohi masu nagarta da ba za mu iya ganinsu ba.— Haka yake, da Jehovah Allah, da Yesu, kuma akwai mala’iku masu nagarta. Da akwai miyagun mala’iku ne?— Littafi Mai Tsarki ya ce da akwai su. Ka gaya mini abin da ka koya game da su.—
Abu ɗaya da muka sani shi ne cewa da mala’iku masu nagartan da masu muguntan dukansu sun fi mu ƙarfi. Babban Malami yana da sani sosai game da mala’iku. Wannan domin shi ma mala’ika ne kafin a haife shi a duniya. Ya zauna tare da wasu mala’iku a sama. Ya san miliyoyin mala’iku. Dukan waɗannan mala’iku suna da suna ne?—
E, mun koyi cewa Allah ya ba wa taurari suna. Domin haka za mu iya tabbata cewa ya ba mala’ikun ma suna. Kuma mun sani cewa suna magana da junansu domin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da ‘yaren mala’iku.’ (1 Korinthiyawa 13:1) Me kake tsammanin mala’iku suke magana a kai? Suna magana game da mu ne a duniya?—
Mun sani cewa mala’ikun Shaiɗan, ko kuma aljanu, suna ƙoƙarin
su sa mu yi wa Jehovah rashin biyayya. Saboda haka za su yi magana game da yadda za su yi haka. Suna son mu zama kamarsu domin kada Jehovah ya yi ƙaunarmu mu ma. Amma yaya game da mala’ikun Allah masu aminci? Kana tsammanin su ma suna magana game da mu?— Hakika, suna yi. Suna so su taimake mu. Bari in gaya maka yadda mala’ikun Allah suka taimaki mutane da suke ƙaunar Jehovah kuma suke bauta masa.Alal misali, da akwai wani mutum mai suna Daniel da ya zauna a Babila. Mutane da yawa a wajen ba su ƙaunaci Jehovah ba. Har mutanen sun kafa doka da za ta hori kowanne mutum da ya yi addu’a ga Jehovah Allah. Amma Daniel ba zai daina yi wa Jehovah addu’a ba. Ka san abin da suka yi wa Daniel?—
E, miyagun mutanen suka sa aka jefa Daniel a ramin zakoki. A cikin ramin Daniel ne kawai sai kuma zakoki da suke jin yunwa. Ka Daniel 6:18-22.
san abin da ya faru a lokacin?— ‘Allah ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakuna,’ in ji Daniel. Ba su yi masa rauni ba ko kaɗan! Mala’iku za su iya yin abubuwan ban mamaki ga waɗanda suke bauta wa Jehovah.—Sai kuma lokacin da Bitrus yake kurkuku. Za ka iya tuna cewa Bitrus abokin Babban Malami ne, Yesu Kristi. Wasu mutane ba sa so sa’ad da Bitrus ya gaya musu cewa Yesu Ɗan Allah ne. Saboda haka, suka saka Bitrus a kurkuku. Sojoji suna gadin Bitrus domin kada ya gudu. Da akwai wanda zai taimake shi ne?—
Bitrus yana barci tsakanin masu gadi biyu, kuma an sa masa sarka
a hannunsa. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Sai mala’ikan Jehovah ya zo, wani haske kuma ya haskaka cikin ɗakin: ya taɓa Bitrus a wajen haƙarƙarinsa, mala’ikan ya tashe shi, ya ce, “Tashi tsaye da sauri.”’Sai sarkar da take hannun Bitrus ta faɗi! Sai mala’ikan ya ce masa: ‘Ka saka kayanka, ka ɗaure takalmanka ka biyo ni.’ Masu gadin ba za su iya hana su ba domin mala’ikan yana taimakon Bitrus. Sai suka isa ƙofa ta ƙarfe, wani abin mamaki ya faru. Ƙofar ta buɗe da kanta! Wannan mala’ikan ya ’yantar da Bitrus domin ya ci gaba da wa’azi.—Ayukan Manzanni 12:3-11.
Mala’ikun Allah za su iya taimakonmu mu ma?— E, za su taimake mu. Shin wannan yana nufi ne cewa ba za su taɓa bari a cuce mu ba?— A’a, mala’iku ba sa hana a cuce mu ba idan muka yi wauta. Amma ko ba mu yi wauta ba, za mu iya cutuwa. Ba a gaya wa mala’ikun su kāre wannan daga faruwa ba. Maimakon haka, Allah ya ba su aiki na musamman da za su yi.
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mala’ika da yake gaya wa mutane a ko’ina su bauta wa Allah. (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Ta yaya mala’ikan ya gaya musu wannan? Ya yi ihu ne daga sama saboda kowa ya ji?— A’a, maimakon haka, mabiyan Yesu a duniya suna gaya wa wasu game da Allah, kuma mala’ikun sun ja-gorance su game da wannan aikin nasu. Mala’ikun suna tabbata cewa waɗanda da gaske suke so su san Allah suna samun daman jin wa’azin. Za mu iya saka hannu cikin wannan aikin wa’azi kuma mala’ikun za su taimake mu.
To, yaya idan mutane da ba sa ƙaunar Allah suka tsokane mu? Yaya idan suka saka mu a kurkuku? Mala’ikun za su ’yantar da mu ne?— Za su iya. Amma wannan ba abin da suke yi ba ne kullum.
Mabiyin Yesu Bulus ya taɓa shiga kurkuku. Yana tafiya a cikin jirgin ruwa a cikin hadari. Amma mala’ikun ba su cece shi nan da nan Ayukan Manzanni 27:23-25.
ba. Wannan domin da akwai wasu mutane da suke da bukatar su ji game da Allah. Wani mala’ika ya ce: “Kada ka ji tsoro, Bulus, dole za ka tsaya gaban Kaisar.” Za a kai Bulus gaban mai mallakar duniya, Kaisar, saboda Bulus ya yi masa wa’azi. Mala’ikun sun san inda Bulus yake kuma sun taimake shi. Za su taimake mu mu ma idan da gaske muna bauta wa Allah.—Har yanzu da akwai wani babban aiki da mala’ikun za su yi, kuma za su yi aikin ba da daɗewa ba. Lokacin da Allah zai halaka miyagun mutane ya yi kusa sosai. Dukan waɗanda ba su bauta wa Allah ba za a halaka su. Waɗanda ba su yarda da mala’iku ba domin ba sa ganinsu za su ga cewa lallai sun yi kuskure.—2 Tassalunikawa 1:6-8.
Menene wannan zai kasance a gare mu?— Idan muna ɓangare ɗaya da mala’ikun Allah, za su taimake mu. Amma muna ɓangarensu ne?— Muna ɓangarensu idan muna bauta wa Jehovah. Kuma idan muna bauta wa Jehovah, za mu gaya wa wasu mutane su bauta masa su ma.
Don ka ƙara koyar yadda mala’iku suke shafan rayuwar mutane, karanta Zabura 34:7; Matta 4:11; 18:10; Luka 22:43 da kuma Ayukan Manzanni 8:26-31.