BABI NA 2
Wasika Daga Wurin Allah Mai Kauna
KA GAYA mini, wane littafi ka fi so?— Wasu yara za su zaɓi wanda yake magana game da dabbobi. Wasu za su zaɓi littafi da yake da hotuna da yawa a ciki. Yana da daɗi a karanta waɗannan littattafai.
Amma littattafai mafi kyau a dukan duniya su ne waɗanda suke koyar da mu gaskiya game da Allah. Amma ɗaya daga cikin waɗannan littattafai ya fi duk sauran tamani. Ka san ko wanne ne?— Littafi Mai Tsarki.
Me ya sa Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci?— Domin daga wurin Allah yake. Ya gaya mana game da shi da kuma abubuwa masu kyau da zai yi dominmu. Kuma ya nuna mana abin da ya kamata mu yi domin mu faranta masa rai. Kamar wasiƙa ce daga wurin Allah.
Allah zai iya rubuta dukan Littafi Mai Tsarki daga sama kuma ya ba wa mutum. Amma bai yi haka ba. Ko da yake tunanin daga Allah ne, ya yi amfani da bayinsa a duniya su yi yawancin rubutun Littafi Mai Tsarki.
Ta yaya Allah ya yi haka?— Domin ka fahimci yadda ya yi, ka yi la’akari da wannan. Sa’ad da muka ji muryar wani a rediyo, muryar wataƙila ta zo ne daga mutumin da yake nesa. Sa’ad da muke kallon telibijin, za mu iya ganin hotunan mutane daga wasu ƙasashe ma na duniya, kuma za mu iya jin abin da suke faɗa.
Mutane za su iya tafiya zuwa har duniyar wata a cikin nasu kumbo, kuma za su iya aiko da saƙonni daga can. Ka san da haka?— Idan mutane za su iya yin haka, Allah zai iya aikowa da saƙo daga sama?—
Hakika zai iya! Kuma ya yi haka da daɗewa kafin mutane suka samu rediyo da telibijin.Musa mutum ne wanda ya ji Allah ya yi magana. Musa bai iya ganin Allah ba, amma ya ji muryar Allah. Miliyoyin mutane suna nan sa’ad da wannan ya faru. Hakika, a wannan ranar, Allah ya sa dutse ya jijjiga, aka yi tsawar aradu da walƙiya. Mutane sun sani cewa Allah ya yi magana, amma sun tsorata. Saboda haka suka gaya wa Musa: “Kada Allah shi yi zance da mu, domin kada mu mutu.” Daga baya, Musa ya rubuta abubuwa da Allah ya ce. Kuma abin da Musa ya rubuta suna cikin Littafi Mai Tsarki.—Fitowa 20:18-21.
Musa ya rubuta littattafai biyar na farko na Littafi Mai Tsarki.
Amma ba shi kaɗai ba ne aka yi amfani da shi a rubutun. Allah ya yi amfani da mutane 40 su rubuta wasu ɓangarorin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan mutane sun rayu a dā can, kuma ya yi shekaru da yawa kafin aka kammala rubuta Littafi Mai Tsarki. Hakika, ya ɗauki wajen shekara 1,600! Abin mamaki shi ne cewa ko da yake wasu cikin waɗannan mutane ba su sadu ba, dukan abin da suka rubuta ya jitu.Wasu mutane da Allah ya yi amfani da su su rubuta Littafi Mai Tsarki fitattun mutane ne. Ko da yake Musa dā makiyayi ne, ya zama shugaban al’ummar Isra’ila. Sulemanu sarki ne, shi mutum ne mafi hikima kuma mafi arziki a duniya. Amma wasu marubutan ba fitattu ba ne. Amos ya kula da itatuwa da suke haifan inabi.
Bugu da ƙari, wani marubucin Littafi Mai Tsarki likita ne. Ka san sunansa?— Sunansa Luka. Wani marubuci kuma dā mai karɓan haraji ne. Sunansa Matta. Har ila wani kuma lauya ne, masani ne na dokar addinin Yahudawa. Ya rubuta yawancin littattafai na Littafi Mai Tsarki fiye da kowa. Ka san sunansa?— Sunansa Bulus. Kuma almajiran Yesu, Bitrus da Yohanna masūnta ne, kuma marubutan Littafi Mai Tsarki.
Yawancin waɗannan marubutan Littafi Mai Tsarki sun rubuta game da abin da Allah zai yi a nan gaba. Ta yaya suka san waɗannan abubuwa ma kafin su faru?— Allah ne ya ba su bayani. Ya gaya musu abin da zai faru.
A lokacin da Yesu, Babban Malami, yake duniya, an riga an rubuta yawancin ɓangarorin Littafi Mai Tsarki. Ka tuna cewa, Babban Malamin yana sama dā. Ya san abin da Allah ya yi. Ya gaskata cewa Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne?— Hakika ya gaskata.
Sa’ad da Yesu ya yi magana da mutane game da ayyukan Allah, ya karanta Littafi Mai Tsarki. Wasu lokatai ya gaya musu abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Yesu kuma ya ba mu ƙarin bayani game da Allah. Yesu ya ce: “Abin da na ji kuma a wurinsa, shi ni ke faɗa ma duniya.” Yohanna 8:26) Yesu ya ji abubuwa da yawa daga wurin Allah domin ya zauna tare da Allah. Kuma a ina za mu karanta waɗannan abubuwa da Yesu ya faɗa?— A cikin Littafi Mai Tsarki. An rubuta su duka dominmu ne mu karanta.
(Hakika, sa’ad da Allah ya yi amfani da mutane su yi rubutu, sun yi rubutun ne a yare da suke yi yau da kullum. Saboda haka yawancin Littafi Mai Tsarki an rubuta ne a Ibrananci, wasu kuma da Aramaic, da yawa kuma a Helenanci. Tun da yawancin mutane a yau ba su san yadda za su karanta waɗannan harsunan ba, an rubuta Littafi Mai Tsarki a cikin wasu harsuna. A yau ɓangaren Littafi Mai Tsarki ana karanta shi a cikin harsuna fiye da 2,260. Ka yi tunanin wannan! Littafi Mai Tsarki wasiƙar Allah ce ga mutane a ko’ina. Amma ko sau nawa aka ƙara rubuta shi, saƙonsa ya kasance daga wurin Allah.
Abin da Littafi Mai Tsarki
ya ce yana da muhimmanci a gare mu. An rubuta shi can da daɗewa. Amma ya gaya mana abubuwa da za su faru a yau. Kuma ya gaya mana abin da Allah zai yi ba da daɗewa ba a nan gaba. Abin da ya ce, abin ban sha’awa ne! Ya ba mu bege mai ban mamaki.Littafi Mai Tsarki kuma ya gaya mana yadda Allah yake so mu yi rayuwa. Ya gaya mana abin da yake mai kyau da abin da ba shi da kyau. Kana bukatar ka san wannan, ni ma haka. Ya gaya mana game da mutane da suka yi abin da ke mugu da kuma abin da ya faru da su, saboda mu guje wa masifa da ta same su. Ya kuma gaya mana game da mutane da suka yi abin da yake nagari da kuma sakamakon da suka samu. An rubuta dukan wannan domin amfaninmu ne.
Amma domin mu amfana daga Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu san amsar wata tambaya. Tambayar ita ce: Wanene ya ba mu Littafi Mai Tsarki? Me za ka ce?— Hakika, dukan Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. To, ta yaya za mu nuna cewa lallai muna da hikima?— Ta wajen saurara ga Allah da kuma yin abin da ya ce.
Saboda haka muna bukatar mu ɗauki lokaci mu karanta Littafi Mai Tsarki tare. Sa’ad da muka samu wasiƙa daga wani da muke ƙauna sosai, muna karanta ta a kai a kai. Tana da tamani a gare mu. Haka Littafi Mai Tsarki ya kamata ya kasance a gare mu domin wasiƙa ce daga Wanda ya fi ƙaunarmu. Wasiƙa ce daga wurin Allah.
Ka ɗauki ’yan mintoci kaɗan ka karanta waɗannan nassosi da suka nuna cewa hakika Littafi Mai Tsarki da gaske Kalmar Allah ce, an rubuta saboda amfaninmu: Romawa 15:4; 2 Timothawus 3:16, 17; da kuma 2 Bitrus 1:20, 21.