BABI NA 35
Za Mu Iya Farfaɗowa Daga Mutuwa!
IDAN muka mutu, Allah zai so ya ta da mu kuwa daga matattu, wato, ya ba mu rai?— Nagarin mutum Ayuba ya yi imani cewa Allah yana so ya yi haka. Saboda haka, sa’ad da Ayuba yake tsammanin ya kusa ya mutu, ya ce wa Allah: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka.” Ayuba ya ce Jehovah Allah zai yi marmarin, ko kuma ya so sosai, ya ta da shi daga matattu.—Ayuba 14:14, 15.
Yesu kamar Ubansa, Jehovah Allah yake. Yesu yana so ya taimake mu. Sa’ad da wani kuturu ya ce masa, “idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni,” Yesu ya amsa: “Na yarda.” Kuma ya warkar da kuturun.—Tafiyar tsutsa tamu ce; Markus 1:40-42.
Yesu ya koya daga wurin Ubansa ya ƙaunaci yara. Sau biyu, Jehovah ya yi amfani da bayinsa su ta da yara daga matattu a dā. Iliya ya roƙi Jehovah ya ta da ɗan wata mata da ta yi masa kirki. Kuma Jehovah 1 Sarakuna 17:17-24; 2 Sarakuna 4:32-37.
ya ta da shi. Jehovah kuma ya yi amfani da bawansa Elisha ya ta da wani yaro ƙarami.—Ba abin farin ciki ba ne a sani cewa Jehovah yana ƙaunarmu sosai?— Ba sa’ad da muke da rai ba ne kawai yake tunaninmu. Yana tuna da mu idan muka mutu ma. Yesu ya ce Ubansa yana ɗaukan waɗanda suka mutu ma cewa suna raye! (Luka 20:38) Littafi Mai Tsarki ya ce ‘ba mutuwa ba, ba rai ba, ba abubuwa da suke nan ba, ba abubuwa da suke zuwa ba da za su iya raba mu da ƙaunar Allah.’—Romawa 8:38, 39.
Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa Jehovah yana kula da yara ƙanana. Za ka iya tuna cewa Yesu ya ba da lokaci ya yi wa yara magana game da Allah. Amma ka sani cewa Allah ya ba wa Yesu iko ya ba wa yara rai idan suka mutu?— Bari mu yi magana game da lokacin da Yesu ya ta da yarinya ’yar shekara 12, ’yar mutumin da ake kira Yariyus.
Yariyus yana tare da matarsa da ’yarsu tilo a kusa da Tekun Galili. Wata rana sai yarinyar ta fara ciwo mai tsanani, kuma Yariyus ya fahimci cewa za ta mutu. Sai Yariyus ya fara tunanin Yesu, wannan mutumin kirki da ya ji labarinsa cewa yana warkar da mutane. Yariyus ya je ya neme shi. Ya sami Yesu a bakin Tekun Galili, yana koyar da mutane da yawa.
Yariyus ya ratse tsakanin mutane ya durƙusa a gaban Yesu. Ya ce wa Yesu: ‘ ’Yata tana ciwo sosai. Don Allah ka zo ka taimake ta. Ina roƙonka.’ Babu ɓata lokaci, Yesu ya bi Yariyus. Taron da suka zo wurin Babban Malami ma suka bi su. Amma bayan sun yi ɗan nisa, wasu mutane suka zo daga gidan Yariyus suka gaya masa: ‘ ’Yarka ta mutu! Me ya sa kuma za ka wahalar da malamin?’
Yesu ya ji sa’ad da mutanen suka faɗi haka. Ya san cewa Yariyus
yana baƙin ciki ƙwarai domin ya yi rashin ’yarsa tilonsa. Saboda haka, Ya gaya masa: ‘Kada ka ji tsoro, ka ba da gaskiya kawai, za ta warke.’ Suka ci gaba da tafiya har suka isa gidan Yariyus. A gidan abokanan iyalin suna kuka. Suna baƙin ciki domin abokiyarsu ƙarama ta mutu. Amma Yesu ya gaya musu: ‘Kada ku yi kuka. ’Yar yarinyar ba matacciya take ba, barci take yi.’Da Yesu ya faɗi haka, mutanen suka fara dariya, domin sun sani cewa yarinyar ta mutu. To, me kake tsammani ya sa Yesu ya ce barci take yi? Wane darasi kake tsammani yake so ya koya wa mutane?— Yana so su sani ne cewa mutuwa kamar barci ne mai zurfi. Yana so ya koya musu ne cewa ta wurin ikon Allah, zai iya ba wa mutumin da ya mutu rai da sauƙi kamar yadda muke farkawa daga barci.
Yesu ya sa kowa ya fita daga gidan ban da manzanninsa Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna da kuma baban yarinyar da mamarta. Sai ya shiga inda yarinyar take. Ya riƙe hannunta ya ce: ‘Yarinya, ki tashi!’ Nan da nan ta tashi ta fara magana! Babanta da mamarta suka yi farin ciki mai yawa.—Markus 5:21-24, 35-43; Luka 8:40-42, 49-56.
Yohanna 5:28, 29.
Yanzu ka yi tunani game da wannan. Tun da Yesu zai iya ba wa wannan yarinyar rai, zai iya yin haka ne ga wasu?— Kana tsammanin zai yi haka da gaske?— Hakika, zai yi haka. Yesu da kansa ya ce: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.”—Kana tsammanin Yesu yana so ya ta da mutane daga matattu?— Wani misali daga Littafi Mai Tsarki ya amsa wannan tambayar. Abin da ya faru a kusa da birnin Nayin ya nuna cewa Yesu yana juyayin mutane da suke baƙin ciki a lokacin jana’iza.
Wata mace tana jana’izar ɗanta sa’ad da jama’a suka fito daga Nayin. Da farko mijinta ya mutu, kuma yanzu ɗanta tilonta ya mutu. Tana baƙin ciki ƙwarai! Mutanen Nayin da yawa suna bi sa’ad da aka ɗauki gawar ɗan aka fito da ita bayan gari. Matar tana baƙin ciki, kuma mutane suka yi ƙoƙari su yi mata ta’aziyya.
A wannan ranar, Yesu da almajiransa suna kan hanyar shiga birnin Nayin. Kusa da ƙofar gari, suka haɗu da jama’ar da suke tafiya su binne ɗan matar. Da Yesu ya ga matar da take kuka, ya yi juyayinta. Baƙin cikinta ya taɓa shi. Ya so ya taimake ta.
Da juyayi da kuma tabbaci ya sa ta saurara, ya ce: “Kada ki yi kuka.” Abin da ya yi ya jawo hankalin kowa gare shi. Da Yesu ya je wajen gawar yaron, dukan mutane sun yi mamakin abin da zai yi. Yesu ya yi magana da yaron da ya mutu, ya umurce shi: ‘Samari, na ce maka tashi!’ A take, ya tashi ya zauna! Ya fara magana.—Luka 7:11-17.
Ka yi tunanin yadda matar za ta ji! Yaya za ka ji idan wanda kake ƙauna ya tashi daga matattu?— Wannan bai nuna ba cewa 2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.
Yesu yana ƙaunar mutane da gaske kuma yana so ya taimake su?— Ka yi tunanin yadda za ka kasance a sabuwar duniya ta Allah sa’ad da za ka marabci mutane da suka mutu zuwa rai!—A lokacin, wasu cikin waɗanda za a tashe su mutane ne da muka sani dā, har da yara ma. Za mu san su kamar yadda Yariyus ya san ’yarsa sa’ad da Yesu ya tashe ta. Wasu kuma mutane ne da suka mutu shekaru dubbai da suka shige. Allah ba zai manta da su ba domin sun rayu a dā.
Ba abin farin ciki ba ne da Jehovah Allah da kuma Ɗansa Yesu suna ƙaunarmu sosai haka?— Suna so mu rayu ba na ɗan lokaci ba amma har abada!
Don Allah ka karanta game da bege mai kyau ga matattu a Ishaya 25:8; Ayukan Manzanni 24:15; da kuma 1 Korinthiyawa 15:20-22.