BABI NA 29
“Ku Sani Kuma Ƙaunar Kristi”
1-3. (a) Mene ne ya motsa Yesu ya so ya zama kamar Ubansa? (b) Waɗanne ɓangarori ne na ƙaunar Yesu za mu bincika?
KA TAƁA ganin ɗan yaro yana ƙoƙarin ya zama kamar ubansa? Yaron zai yi koyi da yadda ubansa yake tafiya, yake magana, ko kuma yadda yake yin abu. Da shigewar lokaci yaron zai koyi ɗabi’a da kuma ruhaniyar ubansa. Hakika, ƙauna da kuma sha’awar da yaron yake da su ga ubansa mai ƙauna suka motsa yaron ya so ya yi kamar ubansa.
2 Dangantaka da take tsakanin Yesu da Ubansa na sama kuma fa? “Ina ƙaunar Uban,” in ji Yesu a wani lokaci. (Yohanna 14:31) Babu wanda zai ƙaunaci Jehobah fiye da wannan Ɗan, wanda yake tare da Uban da daɗewa kafin wasu halittu suka wanzu. Ƙauna ta motsa wannan Ɗa mai ibada ya so ya zama kamar Ubansa.—Yohanna 14:9.
3 A babobi na farkon wannan littafi, mun tattauna game da yadda Yesu ya yi cikakken koyi da iko, shari’a, da kuma hikimar Jehobah. Amma ta yaya Yesu ya nuna ƙauna irin ta Ubansa? Bari mu bincika ɓangarori uku na ƙaunar Yesu—ruhunsa na sadaukar da kai, da kuma juyayinsa mai taushi, da kuma kasancewarsa a shirye ya gafarta.
“Ba Ƙaunar da ta Fi Wannan”
4. Ta yaya Yesu ya kafa misali mafi girma na ƙauna ta sadaukar da kai?
4 Yesu ya kafa shahararren misali na ƙauna ta sadaukar da kai. Sadaukar da kai ta ƙunshi rashin son kai, saka bukatun wasu da kuma damuwarsu gaba da namu. Ta yaya Yesu ya gwada irin wannan ƙaunar? Shi da kansa ya yi bayani: “Ba ƙaunar da ta fi wannan, wato mutum ya ba da ransa saboda abokansa.” (Yohanna 15:13) Yesu da son ransa ya ba da kamiltaccen ransa dominmu. Ita ce nuna ƙauna mafi girma da wani mutum ya taɓa yi. Amma Yesu ya nuna ƙauna ta sadaukar da kai a wasu hanyoyi.
5. Me ya sa barin sama hadaya ce ta ƙauna daga wajen Ɗa makaɗaici na Allah?
5 A rayuwarsa kafin ya zama mutum, Ɗa makaɗaici na Allah yana da gata da kuma matsayi mai girma a sama. Yana da dangantaka ta kusa da Jehobah da kuma halittun ruhu da yawa. Duk da wannan albarkatu, wannan Ɗa ƙaunatacce “ya mai da kansa kamar ba kome ba, ya ɗauki matsayin bawa, cikin siffar ɗan Adam aka haife shi, ya kuma bayyana cikin kamannin mutum.” (Filibiyawa 2:7) Ya zo da son rai ya zauna a cikin mutane a cikin duniya da take “a hannun mugun nan.” (1 Yohanna 5:19) Wannan ba hadaya ta ƙauna ba ce daga wajen Ɗan Allah?
6, 7. (a) A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ƙauna marar son kai a lokacin hidimarsa ta duniya? (b) Wane misali ne mai taɓa zuciya, na ƙauna marar son kai aka rubuta a Yohanna 19:25-27?
6 A dukan hidimarsa a duniya, Yesu ya nuna ƙauna ta sadaukar da kai a hanyoyi da yawa. Ba shi da son kai ko kaɗan. Ya shagala cikin hidimarsa sosai da ya sadaukar da sukuni da mutane suke morewa. “Karnukan daji suna da ramukansu, tsuntsaye kuma suna da wurin kwanansu,” in ji shi, “amma Ɗan mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.” (Matiyu 8:20) Tun da gwanin sassaƙa ne, da Yesu ya ɗauki lokaci ya gina wa kansa kyakkyawan gida ko kuma ya yi kyawawan kujeru don ya samu kuɗi da yawa. Amma bai yi amfani da iyawarsa domin ya samu abin duniya ba.
7 Misalin ƙauna ta sadaukar da kai ta Yesu an rubuta ta a Yohanna 19:25-27. Ka yi tunanin abubuwa da suka cika wa Yesu zuciya a ranar mutuwarsa da rana. Sa’ad da yake wahala a kan gungume, ya damu da mabiyansa, aikin wa’azi, da kuma musamman amincinsa da kuma yadda hakan zai shafi sunan Ubansa. Hakika, dukan rayuwar ’yan Adam na nan gaba ya dogara a kansa! Duk da haka, kafin ya mutu, Yesu ya nuna damuwarsa ga uwarsa, Maryamu, wadda gwauruwa ce a lokacin. Yesu ya gaya wa manzo Yohanna ya kula da Maryamu kamar a ce ita ce uwarsa, kuma daga baya manzon ya ɗauke ta zuwa gidansa. Saboda haka, Yesu ya yi tanadin kula da uwarsa a zahiri da kuma a ruhaniya. Wannan lallai nuna ƙauna ce marar son kai!
Ya “Ji Tausayinsu”
8. Mece ce ma’anar kalmar Helenanci da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da ita wajen kwatanta tausayin Yesu?
8 Yesu yana da tausayi, kamar Ubansa. Nassosi sun kwatanta Yesu da cewa mutum ne wanda yake ƙoƙarin ya taimake mutane da suke cikin wahala domin ya tausaya musu. Domin ya kwatanta tausayin Yesu, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar Helenanci da aka fassara ya “ji tausayinsu.” Wani manazarci ya ce: “Ta kwatanta . . . motsin zuci da yake motsa mutum ƙwarai da gaske. Kalma ce mafi ƙarfi na tausayi a Helenanci.” Ka yi la’akari da wasu yanayi da tausayi na ƙwarai ya motsa Yesu ya yi aiki.
9, 10. (a) Wane yanayi ne ma ya sa Yesu da manzanninsa suka nemi wajen da babu kowa? (b) Sa’ad da ba a bar shi ya huta ba, me Yesu ya yi, kuma me ya sa?
9 Ya motsa ya biya bukatu na ruhaniya. Labarin da yake Markus 6:30-34 ya nuna abin da ainihi ya motsa Yesu ya yi juyayi. Ka ƙaga yanayin. Manzannin suna murna domin yanzu suka gama zagayarsu ta wa’azi. Suka koma wajen Yesu suna ɗokin su ba da rahoton dukan abin da suka gani da kuma waɗanda suka ji. Amma mutane sun taru, ba su ba Yesu da almajiransa damar su ci abinci ba ma. Yesu ya lura cewa manzannin sun gaji. “Ku zo mu tafi wurin da ba kowa, don ku ɗan huta,” ya gaya musu. Suka shiga jirgi, suka tafi bakin kogi na arewacin Galili inda babu kowa. Amma taron sun gansu suna tafiya. Wasu kuma suka ji game da haka. Dukan waɗannan suka ruga zuwa bakin kogi na arewacin, suka isa kafin jirgin!
10 Yesu ya yi fushi ne cewa an hana shi hutu? Ko kaɗan! Da ganin taron ya tausaya musu, sun kai dubbai suna jiransa. Markus ya rubuta: “Ya ga taro mai yawa, ya kuma ji tausayinsu, domin suna kamar tumakin da ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.” Yesu ya ga cewa waɗannan mutane ne da suke da bukata ta ruhaniya. Suna kama da tumaki ne da suke ɓacewa babu taimako, domin ba su da makiyayi da zai yi musu ja-gora ko kuma ya kāre su. Yesu ya sani cewa shugabannan addinai marasa tausayi sun ƙyale su da ya kamata su zama makiyayi masu kula. (Yohanna 7:47-49) Ya yi juyayin mutanen, saboda haka ya fara koya musu game da “Mulkin Allah.” (Luka 9:11) Ka lura cewa Yesu ya yi juyayin mutane kafin ma ya ga yadda za su amsa game da abin da zai koyar. Wato, tausayi ba shi ne sakamakon koyar da taron ba, maimakon haka dalilin koyar da taron ne.
11, 12. (a) Yaya ake ɗaukan kutare a lokatan Littafi Mai Tsarki, amma yaya Yesu ya amsa sa’ad da wani mutum kuturta “ta ci ƙarfinsa” ya dumfare shi? (b) Yaya taɓa shi da Yesu ya yi ya shafi kuturun, kuma yaya abin da ya faru wa wani likita ya kwatanta hakan?
11 Ya motsa ya sauƙaƙe wahala. Da yake Yesu yana da tausayi, mutane masu cututtuka iri-iri suka matsa wajensa. Wannan musamman ya bayyana sa’ad da Yesu yake tafiya kuma jama’a suna bin sa, wani mutum da kuturta “ta ci ƙarfinsa” ya dumfare shi. (Luka 5:12) A zamanin Littafi Mai Tsarki ana ware kutare domin a kāre wasu daga kamuwa da kuturta. (Littafin Ƙidaya 5:1-4) Da shigewar lokaci, malaman Yahudawa suka ɗaukaka ra’ayi na rashin tausayi game da kutare kuma suka kafa nasu dokoki na zalunci. a Amma ka lura da yadda Yesu ya amsa wa kuturun: “Wani mai cutar fatar jiki [kuturu] ya zo wurin Yesu, ya durƙusa yana roƙo yana cewa, ‘Idan ka yarda, kana iya ka tsabtace ni in zama marar ƙazanta.’ Sai tausayi ya kama Yesu, ya miƙa hannunsa ya taɓa shi, ya ce masa, ‘Na yarda, na tsabtace ka, ka zama marar ƙazanta!’ Nan da nan sai cutar fatar jikinsa ta bar shi, ya kuwa zama marar ƙazanta.” (Markus 1:40-42) Yesu ya sani cewa taka doka ce kuturun ya kasance a nan. Duk da haka, maimakon ya kore shi, Yesu ya yi juyayinsa ya yi abin da ba za a yi tsammani ba. Yesu ya taɓa shi!
12 Ka yi tunanin yadda kuturun ya ji domin wannan taɓa shi da ya yi? Ka yi la’akari da wannan labari. Likita Paul Brand, ƙwararre ne wajen magance kuturta, ya ba da labarin wani kuturu da ya yi wa magani a Indiya. A lokacin da yake gwada kuturun, likitan ya ɗora hannunsa a kafaɗar kuturun yana bayanin yadda za a yi wa mutumin magani, ta wajen wata mai fassara. Sai kuturun ya fashe da kuka. “Na yi baƙar magana ne?” likitan ya yi tambaya. Mai fassarar ta tambayi mutumin da yarensa, kuma ta amsa: “A’a, likita. Ya ce yana kuka ne domin ka ɗora hannunka a kafaɗarsa. Ya ce har sai da ya zo nan babu wanda ya taɓa taɓa shi na shekaru da yawa.” Ga kuturun da ya dumfari Yesu, kuma Yesu ya taɓa shi, hakan yana da ma’ana mai zurfi. Bayan ya taɓa shi, cutar da ta sa ya zama abin ƙyama ta rabu da shi!
13, 14. (a) Wace jana’iza ce Yesu ya haɗu da ita sa’ad da ya dumfari birnin Nayin, kuma mene ne musamman ya sa yanayin ya kasance abin tausayi? (b) Tausayin Yesu ya motsa shi ya yi wane aiki domin gwauruwa daga Nayin?
13 Ya motsa ya kawar da baƙin ciki. Baƙin cikin wasu ya motsa Yesu ƙwarai. Alal misali, ka yi la’akari da labarin Luka 7:11-15. Ya faru ne a kusan tsakiyar hidimarsa, Yesu ya dumfari bayan gari na birnin Galili a Nayin. Yayin da Yesu ya yi kusa da ƙofar birnin ya haɗu da wasu suna jana’iza. Musamman yanayin abin baƙin ciki ne. Saurayi—wanda ya kasance ɗan tilo ne—ya rasu, kuma uwarsa gwauruwa ce. Wataƙila ta taɓa kasancewa cikin irin wannan jana’iza—na mijinta. A wannan lokacin na ɗanta ne, wanda wataƙila shi ne kawai yake tallafa mata. Taron da suke raka ta wataƙila sun ƙunshi ƙarin masu makoki waɗanda suke kuka kuma mawaƙa suna waƙar baƙin ciki. (Irmiya 9:17, 18; Matiyu 9:23) Sai Yesu ya kafa ido wa uwar da take baƙin ciki, babu shakka tana tafiya kusa da makara da aka ɗauki ɗanta a kai.
14 Yesu ‘ya ji tausayi’ domin uwar da ta yi rashi. Da murya mai ba da tabbaci, ya ce mata: “Kada ki yi kuka.” Ba a gayyace shi ba, ya je ya taɓa makarar. Waɗanda suke ɗauke da makarar—da kuma wataƙila sauran taron—suka tsaya. Da muryar iko, Yesu ya yi wa gawar magana: “Saurayi, na ce maka, ka tashi.” Me ya faru daga nan? “Wannan da ya mutu ya tashi ya zauna, ya fara magana” kamar a ce daga barci aka tashe shi! Sai furuci mafi taɓa zuciya ya biyo baya: “Yesu kuma ya miƙa shi ga mamarsa.”
15. (a) Labarin Littafi Mai Tsarki game da juyayi da Yesu ya yi ya nuna wace nasaba ce tsakanin tausayi da kuma aiki? (b) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu a wannan?
15 Me muka koya daga wannan labarin? Ka lura da nasaba da take tsakanin tausayi da aiki. Yesu ba zai ga wasu suna wahala ba kuma bai yi juyayinsu ba, kuma ba zai ji tausayinsu ba ba tare da yin wani abu ba. Ta yaya za mu bi misalinsa? Kiristoci, muna da wajibi na yin wa’azin bishara da kuma almajirantarwa. Ainihi ƙaunar Allah ce take motsa mu. Amma, mu tuna cewa wannan ma aikin tausayi ne. Sa’ad da muka ji tausayin mutane kamar yadda Yesu ya yi, zuciyarmu za ta motsa mu mu yi dukan abin da za mu iya mu gaya musu bisharar. (Matiyu 22:37-39) Game da jin tausayin ’yan’uwa masu bi waɗanda suke wahala ko kuma suke baƙin ciki fa? Ba za mu iya kawar da wahala ta zahiri cikin mu’ujiza ba ko kuma mu ta da matattu. Amma, za mu iya nuna tausayi ta wajen nuna damuwarmu ko kuma mu ba da taimako da ya dace.—Afisawa 4:32.
‘Uba, Ka Gafarta Musu’
16. Ta yaya kasancewar Yesu a shirye ya yi gafara ya bayyana sa’ad da yake kan gungume na azaba?
16 Yesu ya nuna ƙaunar Ubansa daidai a wata hanya mafi muhimmanci—yana hanzarin “yin gafara.” (Zabura 86:5) Wannan kasancewa a shirye ya bayyana sa’ad da yake kan gungumen azaba. Da aka tilasta masa mutuwa mai azaba kuma abin kunya, da ƙusoshi suka huda hannayensa da ƙafafuwansa, me Yesu ya yi magana a kai? Ya roƙi Jehobah ya hukunta waɗanda suka kashe shi ne? Akasarin haka, kalmomin ƙarshe na Yesu sun haɗa da: “Uba, bari ka gafarta musu, gama ba su san abin da suke yi ba.”—Luka 23:34. b
17-19. A wace hanya ce Yesu ya nuna cewa ya gafarta wa manzo Bitrus domin musun saninsa da ya yi sau uku?
17 Wataƙila misalin gafartawa mafi motsawa na Yesu ya bayyana a hanyar da ya bi da manzo Bitrus. Babu tambaya cewa Bitrus yana ƙaunar Yesu sosai. A daren ƙarshe na rayuwar Yesu, daren 14 ga Nisan, Bitrus ya ce masa: “Ubangiji, ina a shirye in je har ma kurkuku tare da kai. In ma mutuwa ce, mu mutu tare.” Awoyi kaɗan bayan haka, sau uku Bitrus ya musanta sanin Yesu! Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya faru sa’ad da Bitrus ya yi musunsa na uku: “Ubangiji kuma ya juya ya dubi Bitrus.” Nauyin alhakinsa ya dame shi, Bitrus “ya fita waje, ya fashe da kuka mai-zafi.” Sa’ad da Yesu ya mutu daga baya a wannan ranar, manzon wataƙila yana tunanin, ‘Ubangijina ya gafarta mini kuwa?’—Luka 22:33, 61, 62.
18 Bitrus bai daɗe da jirar amsa ba. An tashi Yesu a safiyar ranar 16 ga Nisan, kuma kamar a wannan ranar ce ya ziyarci Bitrus. (Luka 24:34; 1 Korintiyawa 15:4-8) Me ya sa Yesu ya mai da hankali a kan wannan manzon da ya yi musun saninsa? Wataƙila Yesu yana so ne ya tabbatar wa Bitrus da ya tuba cewa har yanzu Ubangijinsa yana ƙaunarsa kuma ya riƙe shi da tamani. Amma Yesu ya yi fiye da haka ya tabbatar wa Bitrus.
19 Daga baya Yesu ya bayyana wa almajiran a Tekun Galili. A wannan lokacin, Yesu sau uku ya tambayi Bitrus (wanda ya yi musun sanin Ubangijinsa sau uku) game da ƙaunar Bitrus gare shi. Bayan ta ukun, Bitrus ya amsa: “Ya Ubangiji, ai, ka san dukan kome, ka san ina sonka.” Hakika, Yesu wanda ya san zuciya, ya sani cewa Bitrus yana sonsa kuma yana ƙaunarsa. Har ila, Yesu ya ba wa Bitrus zarafin ya tabbatar da ƙaunarsa. Ƙari ga haka, Yesu ya umurci Bitrus ya “ciyar” kuma ya yi “kiwon” ‘tumakinsa.’ (Yohanna 21:15-17) Da farko, an ba wa Bitrus aiki ya yi wa’azi. (Luka 5:10) Amma yanzu, cikin nuna yarda na ban mamaki, Yesu ya ba shi ƙarin hakki mai nauyi—ya kula da waɗanda za su zama mabiyan Kristi. Ba da daɗewa ba bayan haka, Yesu ya ba Bitrus fitaccen matsayi a ayyukan almajiransa. (Ayyukan Manzanni 2:1-41) Lallai Bitrus ya samu kwanciyar rai da ya san cewa Yesu ya gafarta masa kuma har ila ya amince da shi!
Ka San “Ƙaunar Kristi”?
20, 21. Ta yaya za mu zo ga cikakken “sani kuma ƙaunar Kristi wadda ta wuce gaban a san ta”?
20 Hakika, Kalmar Jehobah ta kwatanta ƙaunar Kristi da kyau. Amma, yaya ya kamata mu amsa wa ƙaunar Yesu? Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu “san ƙaunar [Krist] wadda ta fi gaban sani.” (Afisawa 3:19) Kamar yadda muka gani, labaran Lingila game da rayuwa da kuma hidimar Yesu ya koya mana abu da yawa game da ƙaunar Kristi. Amma, cikakken ‘sanin ƙaunar Kristi’ ya ƙunshi fiye da koyon abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi.
21 Furucin Helenanci da aka fassara “ku sani” yana nufin “a zahiri, ta wajen gani.” Sa’ad da muka nuna ƙauna a hanyar da Yesu ya yi—ba da kanmu ga wasu ba tare da son kai ba, cikin tausayi muna biya musu bukatunsu, kuma muna gafarta musu daga zuciyarmu—sa’annan za mu fahimci da gaske yadda ya ji. A wannan hanyar, ta wajen fuskantarta za mu “sani kuma ƙaunar Kristi wadda ta wuce gaban a san ta.” Kada mu manta cewa da zarar mun zama kamar Kristi, haka za mu kusaci wanda Yesu ya yi koyi da shi sosai, Allahnmu mai ƙauna, Jehobah.
a Dokar shugabannan addinan Yahudawan ta ce kada kowa ya yi kusa har na wajen kafa shida daga kuturu. Amma kuma idan iska tana busawa, a yi nisan kafa 150 daga kuturun. Midrash Rabbah ya faɗi game da wani malami wanda yake ɓuya wa kutare da kuma wani da yake jifar kutare da duwatsu domin kada su yi kusa da shi. Da haka kutare sun san baƙin cikin ƙiyayya da kuma ganin ana ƙyamarsu, ba a sonsu.
b Ɓangare na farko na Luka 23:34 bai bayyana ba a cikin wasu littattafai na dā. Amma, domin waɗannan kalmomi sun bayyana a cikin wasu littattafai da yawa da suke da tabbaci, an haɗa su cikin New World Translation da kuma wasu fassara masu yawa. Wataƙila Yesu yana magana game da sojojin Roma da suka kashe shi. Ba su san abin da suke yi ba, ba su san ainihin waye ne Yesu. Mai yiwuwa yana magana ne game da Yahudawa da suka ce a kashe shi, amma daga baya za su ba da gaskiya a gare shi. (Ayyukan Manzanni 2:36-38) Hakika, shugabannan addinai da suka sa aka kashe shi suna da alhaki, domin sun yi haka ne cikin sani da kuma mugunta. Ga yawancinsu, gafara ba za ta yiwu ba.—Yohanna 11:45-53.