BABI NA 30
“Ku Yi Zaman Ƙauna”
1-3. Me zai faru sa’ad da muka yi koyi da misalin Jehobah na nuna ƙauna?
“YA FI albarka a bayar da a karɓa.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Waɗannan kalmomin Yesu sun bayyana wannan muhimmiyar gaskiya: Ƙauna marar son kai tana kawo albarka. Ko da yake da akwai farin ciki wajen karɓar ƙauna, farin cikin ya fi ma yawa wajen bayarwa, ko kuma nuna, ƙauna ga wasu.
2 Babu wanda ya san wannan fiye da Ubanmu na samaniya. Kamar yadda muka gani a babobi na baya a wannan sashe, Jehobah ne misali mafi girma na ƙauna. Babu wanda ya nuna ƙauna a babbar hanya ko kuma ta dogon lokaci fiye da yadda ya yi. To, wani abin mamaki ne da aka kira Jehobah ‘Allah mai farin ciki’?—1 Timoti 1:11.
3 Allahnmu mai ƙauna yana so mu yi ƙoƙari mu zama kamarsa, musamman idan ya zo ga nuna ƙauna. Afisawa 5:1, 2 ta gaya mana: “Tun da yake kun zama ’ya’ya waɗanda Allah yake ƙauna, sai ku ɗauki misali daga wurin Allah a cikin zamanku. Ku yi zaman ƙauna.” Sa’ad da muka yi koyi da misalin Jehobah na nuna ƙauna, muna samun farin ciki mai yawa da yake zuwa daga bayarwa. Muna samun gamsuwar sanin cewa muna faranta wa Jehobah rai, domin Kalmarsa ta aririce mu mu yi “ƙaunar juna.” (Romawa 13:8) Amma har yanzu da akwai wasu dalilai da ya sa ya kamata mu yi “zaman ƙauna.”
Abin da Ya Sa Ƙauna ta Zama Wajibi
4, 5. Me ya sa yake da muhimmanci mu nuna ƙauna ta sadaukar da kai ga ’yan’uwa masu bi?
4 Me ya sa yake da muhimmanci mu nuna ƙauna ga ’yan’uwa masu bi? Wato, ƙauna ita ce ainihin Kiristanci na gaskiya. Idan ba tare da ƙauna ba, ba za mu yi gami na kud da kud da ’yan’uwa Kiristoci ba, kuma mafi muhimmanci, ba mu kasance kome ba a idanun Jehobah. Ka yi la’akari da yadda Kalmar Allah ta nanata wannan gaskiya.
5 A darensa na ƙarshe a rayuwarsa ta duniya, Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Sabon umarni nake ba ku, ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma ku ƙaunaci juna. Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yohanna 13:34, 35) “Kamar yadda na ƙaunace ku”—hakika, an umurce mu mu nuna irin ƙaunar da Yesu ya nuna. A Babi na 29, mun lura cewa Yesu ya kafa misali mai kyau wajen nuna ƙauna ta sadaukar da kai, yana saka bukatun wasu a gaba da nasa. Dole ne mu ma mu nuna ƙauna marar son kai, kuma dole ne mu yi ta a bayyane yadda ƙaunarmu za ta bayyana ga waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista. Hakika, ƙauna ta ’yan’uwantaka mai sadaukar da kai alama ce da za a san mabiyan Kristi da ita.
6, 7. (a) Ta yaya muka sani cewa Kalmar Jehobah ta ɗora muhimmanci ƙwarai a kan ƙauna? (b) Kalmomin Bulus da aka rubuta a 1 Korintiyawa 13:4-8 sun mai da hankali a kan wane ɓangare ne na ƙauna?
6 Idan babu ƙauna cikinmu fa? In “ba ni da ƙauna,” Bulus ya ce, “na zama kamar ƙararrawa mai yawan ƙara ne kawai, ko ganga mai yawan ƙara.” (1 Korintiyawa 13:1) Ganga mai yawan ƙara yana da ƙara marar daɗi. Jan ƙarfe mai-ƙara kuma fa? Kwatancen da ya dace kuwa! Mutumin da ba shi da ƙauna, kamar abin kiɗa ne mai yin amo marar daɗi da yake watsar da jama’a maimakon ya jawo su. Ta yaya wannan mutumin zai more dangantaka ta kusa da wasu? Bulus kuma ya sake cewa: “Ko da . . . ina da bangaskiya sosai, har yadda zan iya kawar da duwatsu, amma in dai ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.” (1 Korintiyawa 13:2) Ka yi tunani, mutumin da ba shi da ƙauna, “wofi ne marar amfani,” duk da aikin da zai yi! (The Amplified Bible) Ba a bayyane ba ne sarai cewa Kalmar Allah ta ɗora muhimmanci ƙwarai a kan ƙauna?
7 Amma, ta yaya za mu nuna wannan halin a sha’aninmu da wasu? Domin mu amsa wannan tambayar bari mu bincika kalmomin Bulus da suke 1 Korintiyawa 13:4-8. Abin da aka nanata a waɗannan ayoyi ba game da ƙaunarmu ba ne ga Allah ko kuma ƙaunar Allah a gare mu. Amma, Bulus ya mai da hankali ne a kan yadda mu za mu nuna ƙauna ga juna. Ya kwatanta wasu abubuwa da ƙauna take yi da wasu kuma da ba ta yi.
Abin da Ƙauna Take Yi
8. Ta yaya yawan haƙuri zai taimake mu wajen sha’ani da wasu?
8 “Ƙauna tana da haƙuri.” Saboda haka, ƙauna tana nufin yin haƙuri da mutane. (Kolosiyawa 3:13) Muna bukatar irin wannan haƙurin ne? Domin mu mutane ne ajizai muna bauta tare, daidai ne mu yi tsammani cewa wani lokaci, ’yan’uwanmu Kiristoci za su ba mu haushi, mu ma mukan sa su yi fushi. Amma haƙuri da jimiri za su iya taimakonmu mu haƙura da wasu ƙananan matsala da kuma fushi daga yin sha’aninmu da wasu—ba tare da ta da wa ikilisiya hankali ba.
9. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin kirki ga wasu?
9 “Ƙauna tana da . . . kirki.” Kirki ana nuna shi cikin kalmomi masu kyau masu taimako na sanin ya kamata. Ƙauna tana motsa mu mu nemi hanyoyi da za mu yi kirki, musamman ga waɗanda suke cikin bukata. Alal misali, wani ɗan’uwa da ya tsufa zai kasance da kewa yana bukatar ziyara ta ban ƙarfafa. Wataƙila gwauruwa mai ’ya’ya ko kuma ’yar’uwa da take cikin iyali da ya rabu a zancen addini za ta bukaci taimako. Wani wanda yake ciwo ko kuma yake fuskantar bala’i zai bukaci ya ji kalmomi masu daɗi daga amintaccen aboki. (Karin Magana 12:25; 17:17) Sa’ad da muka yi amfani da zarafi muka nuna kirki a irin waɗannan hanyoyi, muna nuna cewa ƙaunarmu ta gaskiya ce.—2 Korintiyawa 8:8.
10. Ta yaya ƙauna take taimakawa a ɗaukaka kuma a faɗin gaskiya, har a lokacin da ba shi da sauƙi a yi haka?
10 “Ƙauna . . . takan ji daɗin gaskiya.” Wata fassara ta ce: “Ƙauna . . . tana goyon bayan gaskiya.” Ƙauna tana motsa mu mu ɗaukaka gaskiya kuma mu faɗi gaskiya ga juna. (Zakariya 8:16) Alal misali, idan wanda muke ƙauna ya saka hannu cikin zunubi mai tsanani, ƙaunar Jehobah—da kuma wanda ya yi zunubi—za ta taimake mu mu ɗaukaka mizanan Allah maimakon mu yi ƙoƙarin mu ɓoye, mu rage, ko ma mu yi ƙarya game da laifin. Hakika, gaskiyar yanayin zai yi wuya mu yarda. Amma idan muna son lafiyar wanda muke ƙauna, za mu so ya karɓa kuma ya yi na’am da horon Allah na ƙauna. (Karin Magana 3:11, 12) Mu Kiristoci masu ƙauna, kuma muna son “mu aikata abin da yake daidai cikin ayyukanmu duka.”—Ibraniyawa 13:18.
11. Domin ƙauna “takan sa haƙuri cikin kowane hali,” me ya kamata mu yi ƙoƙarin yi game da kurakuran ’yan’uwanmu masu bi?
11 “Ƙauna takan sa haƙuri cikin kowane hali.” Wannan furucin a zahiri yana nufin “tana rufe dukan abu.” (Kingdom Interlinear) Bitrus na Fari 4:8 ta ce: “Ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” Hakika, Kirista wanda ƙauna take yi masa ja-gora ba zai yi ɗokin fallasa dukan kasawar ’yan’uwansa Kiristoci ba. Ko yaya, kurakuran ’yan’uwanmu masu bi ba masu girma ba ne kuma ƙauna za ta iya rufe su.—Karin Magana 10:12; 17:9.
12. Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa ya tabbata da abu mafi kyau game da Filimon, kuma mene ne za mu koya daga misalin Bulus?
12 “Ƙauna tana . . . da bangaskiya cikin kowane hali.” Fassarar Moffatt ta ce ƙauna “koyaushe tana ɗokin gaskata abu mafi kyau.” Ba ma yawan tuhumar ’yan’uwanmu masu bi, mu riƙa shakkar dukan abin da suka yi. Ƙauna tana taimakonmu mu gaskata “abu mafi kyau” game da ’yan’uwanmu kuma mu amince da su. a Ka lura da misali a wasiƙar Bulus zuwa ga Filimon. Bulus ya yi rubutu ne domin ya ƙarfafa Filimon ya yi wa Unisimus bawa da ya gudu maraba, wanda ya zama Kirista. Maimakon ya tilasta wa Filimon, Bulus ya yi roƙo da ke bisa ƙauna. Ya nuna tabbacin cewa Filimon zai yi abin da ya dace, yana cewa: “Na tabbata za ka yi biyayya. Shi ya sa na rubuta wannan da sanin cewa za ka aikata fiye da yadda na faɗa.” (Aya ta 21) Sa’ad da ƙauna ta motsa mu muka furta irin wannan amincin ga ’yan’uwanmu, za mu fito da abu mafi kyau daga gare su.
13. Ta yaya za mu nuna cewa muna begen abu mafi kyau ga ’yan’uwanmu?
13 “Ƙauna tana . . . sa zuciya cikin kowane hali.” Kamar yadda ƙauna take da aminci, haka take da bege. Ƙauna tana motsa mu mu so abu mafi kyau ga ’yan’uwanmu. Alal misali, ko an iske ɗan’uwa yana “cikin yin laifi,” muna begen cewa zai amsa ƙoƙarinmu cikin ƙauna mu gyara shi. (Galatiyawa 6:1) Muna kuma da begen cewa waɗanda suka raunana a bangaskiya za su farfaɗo. Muna haƙuri da irin waɗannan, muna yin iyakacin ƙoƙarinmu mu taimake su su yi ƙarfi cikin bangaskiya. (Romawa 15:1; 1 Tasalonikawa 5:14) Ko wanda muke ƙauna ya bauɗe, ba ma fid da rai cewa wata rana zai komo hankalinsa ya dawo ga Jehobah, kamar yadda ɗan da ya ɓata na almarar Yesu ya nuna.—Luka 15:17, 18.
14. A waɗanne hanyoyi ne za a iya gwada jimirinmu a cikin ikilisiya, kuma ta yaya ƙauna za ta taimake mu mu aikata haka?
14 “Ƙauna takan sa . . . jimiri cikin kowane hali.” Jimiri yana sa mu kahu a lokacin da mun fuskanci ɓacin rai ko wahala. Gwajin jimiri ba daga waje da ikilisiya kawai suke zuwa ba. Wasu lokatai, za mu fuskanci gwaji daga cikin ikilisiya. Domin ajizanci, wani lokaci ’yan’uwanmu za su ɓata mana rai. Baƙar magana za ta iya ɓata mana rai. (Karin Magana 12:18) Wataƙila ba a bi da al’amarin ikilisiya yadda muke tsammanin ya dace ba. Halin wani ɗan’uwa da ake girmama shi zai riƙa ɓata wa mutane rai, zai sa mu yi tunani, ‘Yaya Kirista zai yi irin wannan abin?’ Idan muka fuskanci irin wannan yanayin, za mu ja da baya ne daga ikilisiyar, mu daina bauta wa Jehobah? Ba za mu yi haka ba idan muna da ƙauna! Hakika, ƙauna za ta hana mu makancewa ga laifin ɗan’uwa, da ba za mu ƙara ganin wani abin kirki a gare shi ba ko kuma ma a dukan ikilisiyar. Ƙauna tana sa mu kasance da aminci ga Allah kuma mu tallafa wa ikilisiya ko mene ne wasu mutane ajizai suka ce ko kuma suka yi.—Zabura 119:165.
Abin da Ƙauna Ba Ta Yi
15. Mene ne kishi marar kyau, kuma ta yaya ƙauna za ta taimake mu mu guji wannan motsin rai mai halakarwa?
15 “Ƙauna ba ta jin kishi.” Kishi marar kyau zai iya sa mu mu yi hassadar abin da wasu suke da shi—dukiyarsu, albarkarsu, ko kuma iyawarsu. Irin wannan kishin yana da son kai, motsin rai da yana iya halakarwa, idan ba a kama kai ba, zai iya ta da hankalin ikilisiya. Me zai taimake mu mu tsayayya wa “kishi”? (Yakub 4:5) A cikin kalma guda, ƙauna. Wannan hali zai iya sa mu yi farin ciki da waɗanda kamar suna da matsayi a rayuwa da mu ba mu da shi. (Romawa 12:15) Ƙauna za ta sa, ba za mu yi fushi ba idan aka yabi wani domin iyawarsa ko kuma abin da ya cim ma.
16. Idan da gaske muna ƙaunar ’yan’uwanmu, me ya sa za mu guje wa taƙama game da abin da muke yi a hidimar Jehobah?
16 “Ƙauna . . . ba ta yin taƙama.” Ƙauna tana hana mu nuna iyawarmu ko kuma abin da muka cim ma. Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu da gaske, yaya za mu riƙa taƙama game da nasararmu a hidima ko kuma gatarmu a ikilisiya? Irin wannan taƙama za ta rushe waɗansu ne, ta sa su ji ba su kai kome ba idan aka gwada su da mu. Ƙauna ba za ta bar mu mu yi taƙama ba game da abin da Allah ya ƙyale mu mu yi a hidimarsa. (1 Korintiyawa 3:5-9) Bugu da ƙari, “ƙauna ba ta yin taƙama,” ko kuma kamar yadda wata fassara ta ce, ba ta “babban ra’ayi game da muhimmancinta.” Ƙauna tana hana mu kasancewa da ra’ayi mai girma game da kanmu.—Romawa 12:3.
17. Ƙauna tana motsa mu mu nuna wane la’akari da wasu, kuma wane irin hali za mu guje wa?
17 “Ƙauna . . . ba ta yin ɗaga kai” (ko rashin hankali.) Mutumin da yake yin rashin hankali yana abubuwa a hanyar da ba ta dace ba ko kuma mai kawo ɓacin rai. Irin wannan tafarkin ba ta da ƙauna, domin ya nuna rashin la’akari da yadda wasu suke ji. Akasin haka, da kirki a cikin ƙauna da yake motsa mu mu nuna la’akari da wasu. Ƙauna tana ɗaukaka halaye masu kyau, hali mai ibada, da kuma daraja ’yan’uwanmu masu bi. Saboda haka, ƙauna ba za ta yarda mana mu yi “wawanci” ko abin kunya ba—hakika, halin da zai ɓata wa ’yan’uwanmu Kirista rai.—Afisawa 5:3, 4.
18. Me ya sa mutum mai ƙauna ba zai nace a yi kome a nasa hanyar ba?
18 “Ƙauna . . . ba ta sonkai.” A nan Revised Standard Version ya ce: “Ƙauna ba ta dagewa ga ra’ayinta kawai.” Mutum mai ƙauna ba zai bukaci a yi kome daidai da ra’ayinsa ba, sai ka ce ra’ayinsa koyaushe daidai yake. Ba ya yi wa wasu wayo, ya yi amfani da ikon rinjayarsa ya mallaki waɗanda suke da ra’ayi dabam. Irin wannan taurin kai yana bayyana girman kai ne, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Girman kai yakan kai ga halaka.” (Karin Magana 16:18) Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, za mu daraja ra’ayinsu, kuma a inda ya yiwu, za mu yarda da abin da suka ce. Ruhun sanin ya kamata ya jitu da kalmomin Bulus: “Kada ka yi wa kanka kaɗai abu mai kyau, amma ka yi wa ɗan’uwanka kuma.”—1 Korintiyawa 10:24.
19. Ta yaya ƙauna take taimakonmu mu amsa sa’ad da wasu suka yi mana laifi?
19 “Ƙauna . . . ba ta jin tsokana, ba ta riƙe laifi a zuciya.” Ƙauna ba ta fusata da wuri domin abin da mutane suka ce ko kuma suka yi. Hakika, daidai ne mu fusata sa’ad da wasu suka yi mana laifi. Amma idan ma muka yi fushi, ƙauna ba za ta bar mu mu ci gaba da fusata ba. (Afisawa 4:26, 27) Ba za mu nukura game da abin ɓacin rai da ya faru, kamar a ce ana rubuta su ne cikin littafi saboda kada a manta da su. Maimakon haka, ƙauna tana motsa mu mu yi koyi da Allahnmu mai ƙauna. Kamar yadda muka gani a Babi na 26, Jehobah yana yin gafara ne idan da kyakkyawan dalilin yin haka. Idan ya gafarta mana, ya mance da batun, wato, ba zai kama mu da laifi ba kuma a nan gaba. Ba ma godiya ne cewa Jehobah ba ya nukura?
20. Yaya za mu ji idan ɗan’uwa mai bi ya fāɗa a tarkon zunubi kuma ya wahala domin haka?
20 “Ƙauna . . . ba ta jin daɗin mugunta.” The New English Bible a nan ya ce: “Ƙauna . . . ba ta farin ciki domin zunubin wani mutum.” Fassarar Moffatt ta ce: “Ƙauna ba ta murna sa’ad da wasu suka yi kuskure.” Ƙauna ba ta murna da rashin adalci, saboda haka ba za mu rage munin kowacce irin lalata ba. Yaya za mu ji idan ɗan’uwanmu mai bi ya fāɗa a tarkon zunubi kuma ya wahala domin haka? Ƙauna ba za ta ƙyale mu mu yi murna ba, kamar ana cewa, ‘Ya yi kyau! Allah ya kama shi!’ (Karin Magana 17:5) Amma muna farin ciki yayin da wani ɗan’uwa da ya yi zunubi dā ya komo ruhaniyarsa.
“Hanyar da Ta Fi Duka Kyau”
21-23. (a) Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce “ƙauna ba ta ƙārewa”? (b) Mene ne za a bincika a babi na ƙarshe?
21 “Ƙauna ba ta ƙārewa.” Mene ne Bulus yake nufin da waɗannan kalmomin? Kamar yadda ka gani a cikin matanin, yana magana ne a kan kyautar ruhu da take tsakanin Kiristoci na farko. Waɗannan kyauta suna alamta cewa tagomashin Allah yana kan sabuwar ikilisiya da aka kafa. Amma ba dukan Kiristoci ba ne za su iya warkarwa, su yi annabci, ko kuma su yi magana cikin wasu harsuna. Amma, wannan ba wani abu ba ne; domin kyauta ta mu’ujiza ta ƙare. Duk da haka, wata aba za ta rage, abar da kowanne Kirista zai iya koyonta. Ta fi kowacce shahara, za ta fi kowacce kyauta ta mu’ujiza daɗewa. Hakika, Bulus ya kira ta “hanyar da ta fi duka kyau.” (1 Korintiyawa 12:31) Mece ce wannan “hanyar da ta fi duka kyau”? Hanyar ƙauna ce.
22 Babu shakka, ƙauna ta Kiristoci da Bulus ya kwatanta “ba ta ƙārewa,” wato, ba ta kai ƙarshenta. Har wa yau, ƙauna ta sadaukar da kai take nuna mabiyan Yesu na gaskiya. Ba ma ganin tabbacin irin wannan ƙaunar a ikilisiyar masu bauta wa Jehobah a dukan duniya? Wannan ƙaunar za ta kasance har abada, domin Jehobah ya yi wa bayinsa masu aminci alkawarin rai madawwami. (Zabura 37:9-11, 29) Bari mu ci gaba da yin ƙoƙarinmu mu yi “zaman ƙauna.” Ta wajen haka, za mu samu farin ciki mai yawa da yake zuwa daga bayarwa. Fiye ma da haka, za mu ci gaba da rayuwa—hakika, mu ci gaba da rayuwa—dindindin wajen yin koyi da Allahnmu mai ƙauna, Jehobah.
Ana gane mutanen Jehobah ta wajen ƙaunarsu ga wasu
23 A wannan babi da ya ƙare sashe na zance a kan ƙauna, mun tattauna yadda za mu nuna ƙauna ga wasu. Amma domin hanyoyi da yawa da muke amfana daga ƙaunar Jehobah, da ikonsa, da shari’arsa, da kuma hikimarsa, ya kamata mu yi tambaya, ‘Yaya za mu nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa da gaske?’ Za a bincika wannan tambayar a babi na ƙarshe.
a Hakika, ƙaunar Kirista ba aba ba ce da za a ruɗe ta da sauri. Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargaɗi: “Ku mai da hankali da masu kawo rabe-rabe tsakaninku, waɗanda suke sa ku dalilin tuntuɓe, . . . Ku yi nesa da su!”—Romawa 16:17.