BABI NA 1
“Lallai, Wannan Allahnmu Ne!”
1, 2. (a) Waɗanne tambayoyi ne za ka so ka yi wa Allah? (b) Mene ne Musa ya tambayi Allah?
YAYA za ka ji idan ka sami zarafin tattaunawa da Allah? Tunanin hakan kaɗai ma yana tsoratarwa. Mamallakin dukan halitta yana magana da kai! Ka yi jinkiri da farko, amma sai ka yi ƙoƙari ka amsa. Ya saurare ka, ya amsa ka, ya ma ce ka yi kowacce irin tambayar da kake so. Yanzu, wace tambaya ce za ka yi?
2 A dā can, akwai wani mutumin da ya kasance cikin irin wannan yanayin. Sunansa Musa. Abin da ya zaɓa ya tambayi Allah zai ba ka mamaki. Bai yi tambaya ba game da kansa, ko kuma abin da zai same shi a nan gaba, ko kuma game da dalilin da ya sa mutane suke wahala. Maimakon haka, ya tambayi sunan Allah. Za ka iya cewa wannan bai dace ba, domin Musa ya riga ya san sunan Allah. Tambayarsa lalle tana da ma’ana mai zurfi. Hakika, ita ce tambaya mafi muhimmanci da Musa ya yi. Amsar ta shafi dukanmu. Za ta iya taimaka maka ka zama aminin Allah. Ta yaya? Bari mu bincika wannan tattaunawa ta musamman.
3, 4. Mene ne ya faru kafin Musa ya yi taɗi da Allah, kuma mene ne suka tattauna?
3 Musa ɗan shekara 80 ne a lokacin. Ya yi shekara arba’in yana hijira daga mutanensa Isra’ilawa, waɗanda bayi ne a ƙasar Masar. Wata rana, sa’ad da yake kiwon garken surukinsa, ya ga abin mamaki. Ɗan kurmi yana cin wuta, amma bai ƙone ba. Sai Musa ya ratse don ya duba. Wataƙila ya firgita sa’ad da ya ji murya ta yi masa magana a tsakiyar wutar! Ta wajen mala’ika, Allah da Musa suka yi taɗi na dogon lokaci. Allah ya gaya wa Musa cewa yana so ya koma ƙasar Masar don ya ceci Isra’ilawa da suke zaman bauta.—Fitowa 3:1-12.
4 A wannan lokacin, da Musa zai yi wa Allah tambayoyi da yawa. Amma, ka lura da tambayar da ya zaɓa ya yi: “Sa’ad da na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninmu ya aike ni zuwa gare ku,’ in kuma suka tambaye ni cewa, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce musu?”—Fitowa 3:13.
5, 6. (a) Tambayar da Musa ya yi ta koya mana wace gaskiya ce mai muhimmanci? (b) Wane abu mai sa baƙin ciki ne aka yi da sunan Allah? (c) Me ya sa yake da muhimmanci da Allah ya bayyana sunansa ga ’yan Adam?
5 Abu na fari da wannan tambayar ta koya mana shi ne cewa, Allah yana da suna. Bai kamata mu yi wasa da wannan gaskiyar ba. Duk da haka, mutane da yawa suna yin hakan. A fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa, an cire sunan Allah, an sauya shi da laƙabi kamar su, “Ubangiji” da kuma “Allah.” Wannan shi ne ɗaya cikin abu mafi sa baƙin ciki da addinai suka yi. Me ya sa? Domin abu na farko da muke yi sa’ad da muka sadu da wani shi ne mu san sunansa. Haka yake idan ya zo ga sanin Allah. Ba wani ba ne da ba shi da suna wanda yake nesa, wanda ba za a taɓa saninsa ba, ko kuma a fahimce shi. Ko da yake ba a iya ganin sa, amma yana wanzuwa da gaske kuma sunansa Jehobah.
6 Bugu da ƙari, sa’ad da Allah ya bayyana sunansa, wani abin mamaki, abin sha’awa yana shirin aukuwa. Yana gayyatar mu mu zo mu san shi. Yana so mu zaɓi abin da ya fi kyau a rayuwa, wato mu kusace shi. Amma Jehobah bai gaya mana sunansa kawai ba. Ya kuma koya mana abin da sunan yake nufi.
Ma’anar Sunan Allah
7. (a) Mene ne sunan Allah yake nufi? (b) Mene ne Musa yake so ya sani da gaske sa’ad da ya tambayi Allah sunansa?
7 Jehobah ya zaɓi sunansa da kansa, kuma sunan yana cike da ma’ana. “Jehobah” yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Hakika, shi ne ya sa dukan abubuwa suka wanzu. Yana kuma tabbatar da cewa dukan nufinsa sun cika, kuma zai iya sa bayinsa ajizai su zama duk abin da yake so. Hakan yana da ban-razana sosai. Amma sunan Allah ya koya mana ƙarin abubuwa game da shi. Hakika, Musa yana so ya sami ƙarin bayani. Ka san cewa Jehobah ne Mahalicci, kuma ya san sunansa. Mutane sun daɗe suna yin amfani da sunan. Babu shakka, sa’ad da Musa ya tambayi sunan Allah, yana so ya sami ƙarin bayani game da halayen Jehobah. Wato, yana cewa ne: ‘Mene ne zan gaya wa mutanenka Isra’ilawa game da kai da zai gina bangaskiyarsu gare ka, ya tabbatar musu da gaske cewa za ka cece su?’
8, 9. (a) Ta yaya Jehobah ya amsa tambayar Musa, kuma mene ne ba daidai ba game da yadda ake yawan fassara amsarsa? (b) Mene ne ma’anar furucin nan “Zan Zama Abin da Nake So In Zama”?
8 Sa’ad da Jehobah yake amsa Musa, ya ambata wani abu game da sunansa. Ya ce: “Zan Zama Abin da Nake So In Zama.” (Fitowa 3:14, NW) Fassara da yawa na Littafi Mai Tsarki sun ce: “Ni ina yadda nake.” Amma yadda aka mai da hankali aka fassara shi a cikin New World Translation ya nuna cewa Allah ba kawai yana tabbatar da wanzuwarsa ba ne. Maimakon haka, yana koya wa Musa ne da kuma dukanmu cewa “zai zaɓi ya zama,” duk abin da ake bukata domin ya cika alkawuransa. Ga yadda aka fassara ayar nan a cikin juyin J. B. Rotherham: “Zan Zama dukan abin da nake so.” Wani gwani a Ibrananci na Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a kan wannan furucin: “Ko yaya yanayin ko kuma bukatar . . . , Allah zai ‘zama’ maganin wannan bukatar.”
9 Me wannan yake nufi ga Isra’ilawa? Kowacce irin tangarɗa da za su fuskanta, ko yaya wahalar da za su iske kansu ciki ta zama, Jehobah zai zama dukan abin da ake bukata domin ya cece su daga zaman bauta kuma ya kai su Ƙasar Alkawari. Babu shakka, wannan sunan ya sa sun dogara ga Allah. Zai sa mu ma a yau mu dogara da shi. (Zabura 9:10) Me ya sa?
10, 11. Ta yaya sunan Jehobah ya sa mu ɗauke shi a matsayin Uba nagari? Ka ba da misali.
10 Alal misali: Iyaye suna bukatar yin abubuwa dabam-dabam kullum don su kula da ’ya’yansu. A rana guda, uwa za ta zama nas, mai girki, malama, mai ba da horo, alƙali, da dai sauransu. Mutane da yawa suna jin ayyuka masu yawa da ake bukata daga wurinsu ya fi ƙarfinsu. Sun lura da dogara ƙwarai da ’ya’yansu suke yi gare su, ba sa shakkar cewa Baba ko Mama, za su lallashe su, su sulhunta su, su gyara abin wasa da ya lalace, kuma su amsa kowacce irin tambayar da suka yi. Wasu iyaye suna jin ba su cancanci irin dogarar da ’ya’yansu suke yi gare su ba. A wasu lokuta, suna jin kunya domin kasawarsu. Suna ji kamar ba su isa ba sam su yi waɗannan ayyuka.
11 Jehobah ma Uba ne mai ƙauna. Duk da haka, ba tare da karya mizanansa ba, babu abin da ba zai iya zama ba domin ya kula da ’ya’yansa na duniya a hanya mafi kyau. Saboda haka, sunansa Jehobah, ya nuna mana cewa yana so mu ɗauke shi a matsayin Uba nagari. (Yakub 1:17) Musa da dukan sauran amintattun Isra’ilawa ba da jimawa ba suka fahimci cewa Jehobah yana aikata abubuwa cikin jituwa da sunansa. Sun yi mamaki sa’ad da Jehobah ya zama duk abin da suke bukata. Ya ci nasara a kan dukan maƙiyansu, ya raba ruwan Jar Teku, ya ba su dokoki masu kyau, ya yi adalci sa’ad da ya hukunta su, ya ba su abinci da ruwa a cikin jeji, ya kuma tabbatar da cewa tufafinsu da takalmarsu ba su lalace ba, da dai sauransu.
12. Ta yaya halin Fir’auna game da Jehobah ya bambanta da na Musa?
12 Saboda haka, Allah ya bayyana sunansa, ya ba da bayanin ma’anarsa, kuma har ya gwada cewa ma’anarsa gaskiya ce. Babu shakka, Allah yana so mu san shi. Mu kuma fa? Musa yana so ya san Allah. Wannan muradi mai ƙarfi ya shafi rayuwar Musa kuma ya kai shi ga kusantar Ubanmu na sama sosai. (Littafin Ƙidaya 12:6-8; Ibraniyawa 11:27) Abin nadama, kaɗan ne kawai cikin tsarar Musa suke da irin wannan muradin. Sa’ad da Musa ya gaya wa Fir’auna, sarkin Masar mai girman kai sunan Jehobah, Fir’auna ya ce: ‘Wane ne wannan Jehobah?’ (Fitowa 5:2) Fir’auna ba ya son ya samu ƙarin sani game da Jehobah. Maimakon haka, yana wa Allahn Isra’ila rashin kunya cewa ba shi da muhimmanci ko kuma amfani. Irin wannan hali gama-gari ne a yau. Yana makanta mutane ga ɗaya cikin muhimmiyar gaskiyar cewa, Jehobah shi ne Ubangiji, Sarki Mafi Girma.
Jehobah Ubangiji Sarki Mai Girma
13, 14. (a) Me ya sa aka ba Jehobah laƙabi da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma mene ne wasu cikinsu? (Ka duba akwati a shafi na 14.) (b) Me ya sa Jehobah ne kaɗai ya isa a ce da shi “Allah Mafi Ɗaukaka”?
13 Jehobah yana iya yin duk wani abin da yake so, shi ya sa yake da laƙabi da yawa a cikin Nassi. Waɗannan laƙabin ba su fi sunansa muhimmanci ba. Maimakon haka, suna koya mana ƙarin abin da sunansa yake nufi. Alal misali, an kira shi “Allah Mafi Ɗaukaka.” (Zabura 57:2) Wannan laƙabi na ɗaukaka, da ya bayyana sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana matsayin Jehobah. Shi kaɗai yake da ikon ya Mallaki dukan halitta. Ka bincika abin da ya sa.
14 Babu wani kamar Jehobah domin shi kaɗai ne ya halicci kome. Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:11 ta ce: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cancanci ka karɓi ɗaukaka, da girma, da iko. Gama ka halicci kome da kome, kuma ta wurin nufinka suka kasance aka kuma halicce su.” Waɗannan kalmomin masu ɗaukaka ba za su kasance ga wani dabam ba. Kowanne abu a sararin sama, Jehobah ne ya halicce shi! Babu shakka, Jehobah ya cancanci daraja, iko, da ɗaukaka domin shi ne Allah Mafi Ɗaukaka da kuma Mahaliccin dukan abu.
15. Me ya sa aka kira Jehobah “Sarkin zamanai”?
15 Wani laƙabin da Jehobah ne kawai yake da shi “Sarkin zamanai” ne. (1 Timoti 1:17; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 15:3) Mene ne wannan yake nufi? Yana da wuya hankalinmu mai iyaka ya fahimta, amma Jehobah madawwami ne a duka gefe biyu, wato gaba da baya. Zabura 90:2 ta ce: “Kai Allah ne har abada, marar farko marar ƙarshe.” Saboda haka, Jehobah ba shi da mafari, yana kasance koyaushe. An kira shi yadda ya dace, wato “Wanda Yake Tun Dā” domin yana wanzuwa tun daga dawwama kafin wani ko wani abu ya wanzu! (Daniyel 7:9, 13, 22) Wane ne zai iya tuhumar cancantarsa na Allah Mafi Ɗaukaka?
16, 17. (a) Me ya sa ba za mu iya ganin Jehobah ba, kuma me ya sa wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba? (b) Da yake ba za mu iya gani da kuma taɓa Jehobah ba, shin hakan yana nufi ne cewa bai wanzu ba da gaske?
16 Duk da haka, wasu suna tuhumar wannan cancantar, kamar yadda Fir’auna ya yi. Kaɗan daga cikin damuwar shi ne mutane ajizai sun dogara sosai bisa abin da suke iya gani da idanunsu. Ba za mu iya ganin Allah Mafi Ɗaukaka ba. Shi ruhu ne, ba ya ganuwa ga idanun mutane. (Yohanna 4:24) Ban da haka ma, idan mutum jini da nama ya tsaya a gaban Jehobah Allah, ai sai mutuwa ke nan. Jehobah da kansa ya gaya wa Musa cewa: “Amma fuskata, ba za ka iya ganinta ba, gama mutum ba zai iya ganin fuskata ya rayu kuma ba.”—Fitowa 33:20; Yohanna 1:18.
17 Wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba. Musa ya ga ɗaukakar Jehobah kaɗan, ta wajen mala’ika da yake wakilanci. Mene ne sakamakon wannan? Fuskar Musa ta yi “ƙyalli” na wani lokaci bayan haka. Isra’ilawa sun ji tsoro su dubi fuskar Musa. (Fitowa 33:21-23; 34:5-7, 29, 30) Saboda haka, babu shakka cewa babu mutumin da zai iya ganin Allah Mafi Ɗaukaka! Da yake ba za mu iya ganin sa da kuma taɓa shi ba, shin hakan yana nufi ne cewa bai wanzu ba da gaske? A’a, mun yarda da wanzuwar abubuwa da yawa da ba ma iya gani. Alal misali, iska da kuma tunani. Bugu da ƙari, Jehobah yana nan dindindin, shigewar lokaci ba ta shafansa, har biliyoyin shekaru babu iyaka! A wannan hanya, ya fi kome da za mu iya gani ko kuma mu taɓa, domin duniyar da muke gani tana tsufa kuma ta ruɓe. (Matiyu 6:19) Ya kamata ne mu yi tunaninsa kamar wani abu ko iko ne kawai da bai damu da mu ba? Bari mu gani.
Allah Mai Mutuntaka
18. Wane wahayi aka ba wa Ezekiyel, kuma mene ne fuskoki huɗu na “masu-rai” da suke kusa da Jehobah yake alamtawa?
18 Ko da yake ba za mu iya ganin Allah ba, da akwai wajeje masu ban sha’awa cikin Littafi Mai Tsarki da suka ba mu damar leƙa cikin sama kanta. Sura ta farko ta Ezekiyel misali ne guda. An ba wa Ezekiyel wahayin ƙungiyar Jehobah ta sama, wadda ya gani kamar karusar haske mai yawa. Musamman waɗanda suka burge shi sune kwatancin manyan ruhohi da suka kewaye Jehobah. (Ezekiyel 1:4-10) Waɗannan “masu-rai” suna da nasaba da Jehobah, kuma sifarsu ta bayyana mana wani abu mai muhimmanci game da Allah da suke yi wa bauta. Kowanne yana da fuskoki huɗu, wato ta bijimi, ta zaki, ta gaggafa, da kuma ta mutum. Waɗannan babu shakka suna alamta halaye ne huɗu na musamman na mutuntakar Jehobah.—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:6-8, 10.
19. Wane hali ne (a) fuskar bijimi take alamtawa? (b) ta zaki fa? (c) ta gaggafa fa? (d) ta mutum fa?
19 A cikin Littafi Mai Tsarki, bijimi sau da yawa yana nufin ƙarfi, kuma hakan ya dace, domin dabbar tana da ƙarfi sosai. Zaki kuma, sau da yawa yana zaman shari’a, domin shari’a ta gaskiya tana bukatar gaba gaɗi, hali da aka san zaki da shi. Gaggafa an san ta domin idanunta, tana ganin har ɗan abu mitsitsi a nesa. Saboda haka fuskar gaggafa tana alamar hikimar hangar nesa na Allah. Fuskar mutum kuma fa? Mutum da aka halitta a kamanin Allah, ya kaɗaita wajen nuna hali na Allah mafi girma, wato ƙauna. (Farawa 1:26) Waɗannan sashen mutuntakar Jehobah, wato ƙarfi, shari’a, hikima, da kuma ƙauna, an nanata su sau da yawa a cikin Nassosi da za a iya kiransu halayen Allah na musamman.
20. Ya kamata mu damu ne cewa mutuntakar Jehobah za ta canja, kuma me ya sa ka faɗi haka?
20 Ya kamata mu damu ne cewa Allah wataƙila ya canja cikin shekaru dubbai tun lokacin da aka kwatanta shi cikin Littafi Mai Tsarki? A’a, mutuntakar Allah ba ta canjawa. Ya gaya mana: “Ni Yahweh ba na canjawa.” (Malakai 3:6) Maimakon ya riƙa canjawa kawai bisa ga motsin zuci, Jehobah ya tabbatar da kansa Uba ne cikakke ta hanyar da yake bi da kowanne yanayi. Yana nuna fasalolin mutuntakarsa da ta dace. Ɗaya daga cikin halayensa huɗu, wadda ta fi ita ce ƙauna. Tana bayyana a dukan abin da Allah yake yi. Yana nuna ƙarfinsa, shari’arsa, da kuma hikimarsa cikin ƙauna. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya faɗi wani abu mai girma game da Allah da kuma wannan halin. Ya ce: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Ka lura cewa bai ce Allah yana da ƙauna ba ko kuma Allah yana ƙauna. Maimakon haka, ya ce Allah ƙauna ne. Ƙauna ita ce asali, ita take motsa shi ya yi dukan abin da yake yi.
“Lallai wannan Allahnmu ne!”
21. Yaya za mu ji sa’ad da muka ƙara fahimtar halayen Jehobah?
21 Ka taɓa ganin ɗan yaro yana nuna wa abokansa ubansa da farin ciki da kuma alfahari, “Ga babana”? Masu bauta wa Jehobah suna da dalilan jin haka game da Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya annabta lokaci da amintattun mutane za su yi ihu: “Lallai wannan Allahnmu ne!” (Ishaya 25:8, 9) Da zarar ka ƙara fahimi game da halayen Jehobah, hakanan za ka ji kana da Uba mafi kyau da za a iya tunaninsa.
22, 23. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Ubanmu na sama, kuma ta yaya muka sani cewa yana so mu kusace shi?
22 Babu shakka, Ubanmu Jehobah mai ƙauna ne kuma yana kula da mu. Shi ba marar juyayi ba ne kuma ba ya nisanta kansa daga mu yadda wasu suke da’awa. Ba za mu so mu matso kusa da Allah marar juyayi ba, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce Ubanmu na sama ba haka yake ba. Amma ya kira shi “Allah mai albarka.” (1 Timoti 1:11) Yana yin fushi kuma yana yin farin ciki. A lokacin da ’yan Adam suka taka ƙa’idodin da Jehobah ya kafa domin amfaninsu, Kalmar Allah ta ce: “Zuciyarsa ta ɓaci ƙwarai”. (Farawa 6:6; Zabura 78:41) Amma sa’ad da muka yi abu da hikima cikin jituwa da Kalmarsa, muna ‘faranta zuciyarsa.’—Karin Magana 27:11.
23 Ubanmu yana so mu kusace shi. Kalmarsa ta ƙarfafa mu mu ‘nemi Allah, ko halama ma a lallaba mu same shi, ko da shi ke ba shi da nisa da kowanne ɗayanmu ba.’ (Ayyukan Manzanni 17:27) Amma, yaya zai yiwu ’yan Adam su kusaci Allah Mafi Ɗaukaka a sama duniya?