RATAYE
Sara wa Tuta, Kada Kuri’a, da kuma Hidima ta Farar Hula
Sara wa Tuta. Shaidun Jehobah sun gaskata cewa durƙusa wa tuta ko kuma sara mata, sau da yawa a lokacin da ake waƙa ta ƙasa, bauta ce da take nuna cewa ba za a iya samun ceto daga Allah ba sai daga shugabanni a Ƙasa. (Ishaya 43:11; 1 Korintiyawa 10:14; 1 Yohanna 5:21) Ɗaya daga cikin irin waɗannan shugabanni shi ne Sarki Nebuchadnezzar a Babila ta dā. Domin ya burge mutane da matsayinsa da kuma ɗaukakarsa ta addini, wannan sarki mai iko ya kafa gunki kuma ya tilasta wa mutanensa su durƙusa masa sa’ad da ake waƙa, kamar irin ta ƙasa. Amma, Ibraniyawa uku, Shadrach, Meshach, da Abednego, suka ƙi yin sujada, har a bakin ransu.—Daniel, sura ta 3.
Wani ɗan tarihi, Carlton Hayes ya rubuta, a zamaninmu, “alamar kishin ƙasa da kuma abin bauta ita ce tuta. Maza suna cire hulunansu sa’ad da aka shige da tuta; kuma domin yabon tutar masu waƙa suke rubuta waƙar, yara kuma suna waƙa.” Ƙishin ƙasa, ya daɗa, yana da “ranakunsa masu tsarki,’ kamar su ranar huɗu ga Yuli a Amirka, da kuma ranar “tsarkakkunsa da jarumansa” da “haikulansa” ko kuma
wajen bauta. A wani biki a Brazil, wani shugaban sojoji ya ce: “Ana daraja kuma ana bauta wa tuta . . . daidai da yadda ake bauta wa ƙasa.” Hakika, “tuta tana da tsarki kamar yadda alamar gicciya take da tsarki,” in ji The Encyclopedia Americana.Ba da daɗewa ba, kundin sani da aka ambata a baya ya nuna cewa taken ƙasa “furci ne na ƙauna da aminci da ya haɗa da addu’ar ja-gora da kāriya ga mutane ko kuma sarakunansu.” Bayin Jehobah ba marasa sanin ya kamata ba ne, sun ɗauki irin waɗannan bukukuwa da suka shafi sara wa tuta da kuma yin taken ƙasa a matsayin bauta. Hakika, sa’ad da yake magana a kan sara wa tuta da kuma rantsuwar aminci da ’ya’yan Shaidun Jehobah suka ƙi yi a makaranta, littafin nan The American Character ya ce: “Kotun Ƙoli ta ƙasa ta tabbata cewa waɗannan abubuwa da ake yi kullum bauta ce a ƙararraki masu yawa.”
Ko da yake su ba za su yi bukukuwan da suke ganin sun saɓa wa nassosi ba, mutanen Jehobah suna daraja damar da wasu suke da ita ta yin hakan. Kuma suna daraja tuta a matsayin alama suna kuma yi wa gwamnatoci da aka kafa biyayya a matsayin “masu-mulki” da suke “mai-hidiman Allah.” (Romawa 13:1-4) Shi ya sa Shaidun Jehobah suke bin umurnin su yi addu’a “domin sarakuna da dukan waɗanda ke cikin matsayin manya.” Dalilin yin haka shi ne, “domin mu yi ranmu mai-natsuwa da hankali kwance cikin dukan ibada da kimtsa fuska.”—1 Timothawus 2:2.
Jefa ƙuri’a a lokacin zaɓe na siyasa. Kiristoci na gaskiya suna daraja ’yancin wasu na jefa ƙuri’a. Ba sa nuna rashin yarda ga zaɓaɓɓukan da ake yi, kuma suna ba waɗanda aka zaɓa haɗin kai. Amma, babu ruwansu da ayyukan siyasa ta ƙasa. (Matta 22:21; 1 Bitrus 3:16) Menene Kirista zai yi a ƙasashen da jefa ƙuri’a dole ne ko kuma a yanayin da ake jin haushin waɗanda ba su je wajen jefa ƙuri’a ba? Tuna cewa Shadrach, Meshach, da Abednego sun tafi har filin Dura, Kirista da ke cikin irin wannan yanayi, zai iya zuwa inda ake jefa ƙuri’a idan lamirinsa ya ƙyale haka. Amma kuma zai kula domin kada ya yi watsi da matsayinsa na tsakatsaki. Ya yi la’akari da waɗannan mizanai guda shida:
-
Mabiyan Yesu “ba na duniya ba ne.”—Yohanna 15:19.
-
Kiristoci suna wakiltan Kristi ne da kuma Mulkinsa.—Yohanna 18:36; 2 Korintiyawa 5:20.
-
Ikilisiyar Kirista tana da haɗin kai a imaninta, kuma dukan waɗanda suke cikinta suna da ƙauna irin ta Kristi.—1 Korintiyawa 1:10; Kolossiyawa 3:14.
-
Waɗanda suka zaɓi wani mutum suna da hakkin abin da ya yi.—Ka lura da mizanin da ke rubuce cikin 1 Samuila 8:5, 10-18; 1 Timotawus 5:22.
-
Jehobah ya ɗauki muradin Isra’ilawa na samun sarki a matsayin sun ƙi shi ne.—1 Samuila 8:7.
-
Dole ne Kiristoci su kasance da gaba gaɗi sa’ad da suke magana da mutane daga kowace irin ƙungiyar siyasa game da mulkin Allah.—Matta 24:14; 28:19, 20; Ibraniyawa 10:35.
Hidima ta farar hula. A wasu ƙasashe, hukuma ta bukaci mutane da suka ƙi aikin soja su yi wasu ayyuka ta farar hula na wani ɗan lokaci. Sa’ad da muka fuskanci irin wannan batu, ya kamata mu yi addu’a game da shi, wataƙila mu tattauna shi da wani Kirista da ya manyanta, sai kuma mu yanke shawararmu bisa abin da lamirinmu da aka koyar ya yarda da shi.—Misalai 2:1-5; Filibbiyawa 4:5.
Kalmar Allah ta gaya mana mu “yi biyayya ga mahukunta, ga masu-iko; su ji magana, su zama shiryayyu ga kowane kyakkyawan aiki, . . . masu-laushin hali.” (Titus 3:1, 2) Idan muka fahimci wannan, sai mu yi wa kanmu wasu tambayoyi: ‘Karɓan wannan aiki na farin hula zai sa na yi shirka ne ko kuma zai sa in saka hannu cikin addinin ƙarya?’ (Mikah 4:3, 5; 2 Korintiyawa 6:16, 17) ‘Yin wannan aikin zai sa in kasa cika hakki na ne na Kirista?’ (Matta 28:19, 20; Afisawa 6:4; Ibraniyawa 10:24, 25) ‘A wani ɓangare kuma, yin wannan aikin zai ba ni lokaci ne in faɗaɗa hidima ta ta ruhaniya, wataƙila har in shiga hidima ta cikakken lokaci?’—Ibraniyawa 6:11, 12.
Idan Kirista ya ce zai yi aikin farin hula maimakon ya je kurkuku, ’yan’uwa Kiristoci sai su daraja shawararsa. (Romawa 14:10) Idan kuma ya ce ba zai iya irin wannan aiki ba, ya kamata mutane su daraja wannan shawarar.—1 Korintiyawa 10:29; 2 Korintiyawa 1:24.