Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah
Ya Mai Ƙaunar Jehobah:
‘Za ka san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda da kai,’ in ji Yesu. (Yohanna 8:32) Wannan furcin yana da ban ƙarfafa! Hakika, sanin gaskiya yana yiwuwa, har a waɗannan “kwanaki na ƙarshe” inda ƙarya da rashin gaskiya suka yalwata. (2 Timothawus 3:1) Ka tuna sa’ad da da farko ka fahimci gaskiya yadda aka yi bayanin ta cikin Kalmar Allah? Wannan hakika yana da ban farin ciki!
Duk da haka, ko da yake yana da muhimmanci mu sami cikakken sani na gaskiya kuma mu kasance muna gaya wa mutane game da shi a kai a kai, dole ne kuma halinmu ya kasance ya jitu da gaskiya. Domin mu yi haka, muna bukatar mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah. Menene wannan ya ƙunsa? Abin da Yesu ya ce a daren mutuwarsa ya amsa wannan tambayar. Ya gaya wa manzanninsa masu aminci: “Idan kun kiyaye dokokina, za ku zauna cikin ƙaunata: kamar yadda na kiyaye dokokin Ubana, ina zaune kuwa cikin ƙaunatasa.”—Yohanna 15:10.
Ka lura cewa Yesu ya kasance cikin ƙaunar Allah ta wajen kiyaye dokokin Ubansa. Haka yake a gare mu a yau. Domin mu tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, muna bukatar mu bi tafarkin gaskiya a kowace rana a rayuwarmu. A wannan dare kuma, Yesu ya ce: “Idan kun san waɗannan abu, masu-albarka ne idan kun yi su.”—Yohanna 13:17.
Muna begen cewa wannan littafin zai taimake ka ka ci gaba da bin gaskiya a rayuwarka kuma da haka ka tsare kanka cikin “ƙaunar Allah. . . zuwa ga rai na har abada.”—Yahuda 21.
Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah