FARA MAGANA DA MUTANE
DARASI NA 1
Ka Fadi Abin da Mutumin Zai So
Ƙaꞌida: “Ƙauna . . . ba ta sonkai.”—1 Kor. 13:4, 5.
Abin da Yesu Ya Yi
1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Yohanna 4:6-9. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:
Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?
2. Idan muka soma da zancen wani abu da mutumin yake so, ba mamaki mutumin zai saurare mu da kyau.
Ka Yi Koyi da Yesu
3. Ka yi shirin tattauna batutuwa dabam-dabam. Kar ka nace cewa sai abin da ka shirya ne za ka tattauna da mutum. Za ka iya somawa da abin da yake zuciyar mutane a yau. Ka tambayi kanka cewa:
4. Ka dinga lura. Ka tambayi kanka cewa:
-
‘Mene ne tufafin mutumin, da yanayin fuskarsa, ko gidansa suka nuna mini game da imaninsa da kuma alꞌadarsa?’
5. Ka saurara.
KA KUMA KARANTA
Mat. 7:12; 1 Kor. 9:20-23; Filib. 2:4; Yak. 1:19