Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 4

Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki

Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki

Wane alkawari ne Jephthah ya yi wa Jehobah?

’Yar Jephthah ta cika alkawarin babanta, ko da yake hakan bai yi mata sauki ba

Ka ga yarinyar da ke cikin wannan hoton?— Ita yarinyar wani mutumi ne mai suna Jephthah. Littafi Mai Tsarki bai faɗi sunanta ba, amma mun san cewa ta sa babanta da kuma Jehobah farin ciki. Yanzu za mu koya game da ita da kuma babanta Jephthah.

Jephthah mutumin kirki ne kuma ya koya wa ’yarsa game da Jehobah sosai. Shi mutumi ne mai ƙarfi da kuma shugaba mai kyau. Shi ya sa Isra’ilawa suka ce ya zama shugabansu a lokacin da za su je su yaƙi maƙiyansu.

Jephthah ya yi addu’a cewa Allah ya taimake shi ya ci nasara. Jephthah ya yi alkawari cewa idan suka ci yaƙin, zai ba Jehobah duk wanda ya fara fitowa daga cikin gidansa sa’ad da ya dawo. Wannan mutumin zai zauna kusa da mazaunin Allah kuma ya riƙa aiki a cikin mazaunin duk rayuwarsa. Mazauni wuri ne da mutane suke zuwa su bauta wa Allah a lokacin. Ka san wani abu ne? Jephthah ya ci nasara a yaƙin! Ka san wanda ya fara fitowa sa’ad da Jephthah ya dawo gida?—

Yarinyar Jephthah ce! Ita kaɗai ya haifa, kuma yanzu dole ne Jephthah ya rabu da ita. Hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Amma, ka tuna cewa ya riga ya yi alkawari. Nan da nan sai yarinyar ta ce: ‘Baba, ka riga ka yi wa Jehobah alkawari, sai ka cika.’

Kowace shekara, kawayen ’yar Jephthah suna zuwa wajenta su gaishe ta

’Yar Jephthah ma ta yi baƙin ciki sosai. Me ya sa? Domin a mazaunin, ba za ta iya yin aure ba balle ma ta haihu. Amma, tana son babanta ya cika alkawarinsa kuma tana so ta sa Jehobah farin ciki. Ta fi son hakan maimakon ta yi aure ko kuma ta haihu. Sai ta bar gida kuma ta soma aiki a mazaunin duk rayuwarta.

Kana ganin abin da ta yi ya sa babanta da Jehobah farin ciki?— E, haka ne! Idan kana biyayya kuma kana ƙaunar Jehobah, za ka zama kamar ’yar Jephthah. Kai ma za ka sa iyayenka da Jehobah farin ciki sosai.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Kubawar Shari’a 6:4-6

  • Alƙalawa 11:30-40

  • 1 Korintiyawa 7:37, 38