RATAYE
“Kurwa” da Kuma “Ruhu”—Menene Ainihi Ma’anar Waɗannan Kalmomi?
SA’AD da ka ji kalmomin nan “kurwa” ko kuma “ruhu,” menene yake faɗo maka a zuciya? Mutane da yawa sun gaskata cewa waɗannan kalmomi suna nufin wani abu marar ganuwa da ke zaune cikin mu. Suna tsammanin cewa sa’ad da mutum ya mutu wannan abin sai ya fice daga jikin mutum ya ci gaba da rayuwa. Tun da yake wannan koyarwar ta yaɗu sosai, mutane da yawa sun yi mamaki da suka fahimci cewa wannan ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ce. To, menene kurwa, kuma menene ruhu bisa koyarwar Kalmar Allah?
“KURWA” YADDA AKA YI AMFANI DA ITA CIKIN LITTAFI MAI TSARKI NA ASALI
Da farko, bari mu bincika kurwa. Za ka tuna cewa ainihi an rubuta Littafi Mai Tsarki ne da Ibrananci da kuma Helenanci. Sa’ad da suke rubutu game da kurwa, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan neʹphesh a Ibrananci ko kuma kalmar Helenanci psy·kheʹ. Waɗannan kalmomi biyu sun bayyana fiye da sau 800 a cikin Nassosi, kuma New World
Translation ya fassara su “kurwa.” Idan ka bincika yadda aka yi amfani da wannan kalmar “kurwa” a cikin Littafi Mai Tsarki, za ka ga cewa wannan kalmar ainihi tana nufin (1) mutane, (2) dabbobi, ko kuma (3) ran mutum ko na dabba. Bari mu dubi wasu nassosi da suka gabatar wannan.Mutane.“A zamanin Nuhu, . . . mutane kima, watau masu-rai takwas, suka tsira ta wurin ruwa.” (1 Bitrus 3:20) A nan kalmar nan “masu-rai” a bayyane yake cewa tana nufin mutane—Nuhu, matarsa, ’ya’yansa uku, da matansu. Fitowa 16:16 ta yi maganar umurni da aka ba wa Isra’ilawa game da tara manna. An gaya musu: “tara . . . gwalgwadon yawan masu-rai naku, haka za ku ɗiba, kowane mutum domin waɗanda ke cikin [tanti] nasa.” Saboda haka yawan manna da aka tara bisa ga yawan mutane da ke cikin kowace iyali ne. Wasu wurare da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “masu-rai” ga mutum ko mutane ana samun su a Farawa 46:18; Joshuwa 11:11; Ayukan Manzanni 27:37 da kuma Romawa 13:1.
Dabbobi. A cikin tarihin halitta na Littafi Mai Tsarki mun karanta: “Allah ya ce, Bari ruwaye su yawaita haifan masu-motsi waɗanda ke da rai, tsuntsaye kuma su tashi birbishin duniya cikin sararin sama. Allah kuwa ya ce, Bari ƙasa ta fidda mai-rai kowane bisa ga irinsa, bisashe, da masu-rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu: haka kuwa ya zama.” (Farawa 1:20, 24) A nan, kifaye, tsuntsaye, dabbobi, da kuma namun daji duka an kira su da kalma guda—“masu-rai.” An kira dabbobi masu-rai a Farawa 9:10, Leviticus 11:46; da kuma Lissafi 31:28.
Ran mutum. A wasu lokatai kalmar nan “kurwa” tana nufin ran mutum. Jehobah ya gaya wa Musa: “Dukan mutanen da suka nemi ranka sun mutu.” (Fitowa 4:19) Menene abokan gaban Musu suke nema? Suna ƙoƙari ne su kashe Musa. Da farko, sa’ad da Rahila take haifan Banyamin, “sa’anda ranta yana fita, (gama ta mutu).” (Farawa 35:16-19) A wannan lokaci Rahila ta mutu. Ka yi la’akari kuma da kalmomin Yesu: “Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau ya kan bada ransa domin tumaki.” (Yohanna 10:11) Yesu ya ba da kurwarsa, ko kuma ransa, domin mutane. A wannan wurare na Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “kurwa” a yare na asali bayyane yake cewa tana nufin ran mutum. Za ka sami ƙarin misalai na wannan a 1 Sarakuna 17:17-23; Matta 10:39; Yohanna 15:13; da kuma Ayukan Manzanni 20:10.
Ƙara nazarin Kalmar Allah za ta nuna maka cewa babu inda aka haɗa kalmar nan “kurwa” da “rashin mutuwa” ko “dawwama.” Maimakon haka, Nassosi a yare na asali sun ce kurwa tana mutuwa. (Ezekiel 18:4, 20) Saboda haka, Littafi Mai Tsarki yake kiran wanda ya mutu “gawa.”—Leviticus 21:11.
AN GANO “RUHU”
Bari yanzu mu bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “ruhu.” Wasu mutane suna tsammani “ruhu” wata kalma ce mai nufin “kurwa.” Amma ba haka yake ba. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sarai cewa “ruhu” da “kurwa” suna nufin abubuwa biyu ne da suka bambanta. Ta yaya suka bambanta?
Marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar Ibrananci ruʹach ko kuma ta Helenanci pneuʹma sa’ad da suke rubutu game da “ruhu.” Nassosi kansu sun bayyana ma’anar waɗannan kalmomi. Alal misali, Zabura 104:29 ta ce: ‘Idan ka [Jehobah] swance numfashinsu [ruʹach], sun mutu, sun koma turɓayarsu.’ Yaƙub 2:26 ta ce “jiki ba tare da ruhu [ pneuʹma] matacce ce.” A waɗannan ayoyi, “ruhu” yana nufin abin da yake ba da rai ga jiki. In ba tare da ruhu ba jiki matacce ne. Saboda haka, a cikin Littafi Mai Tsarki an fassara kalmar nan ruʹach ba kawai ruhu ba amma kuma “rai.” Alal misali, game da Ambaliyar zamanin Nuhu, Allah ya ce: “Ina kawo ruwan tufana a bisa duniya, domin a hallaka dukan mai-rai, wanda ke da numfashin [ruʹach] rai a cikinsa, daga ƙarƙashin sama.” (Farawa 6:17; 7:15, 22) Saboda haka, “ruhu” yana nufin iko marar ganuwa da ke motsa dukan abubuwa masu rai.
Kurwa da kuma ruhu ba ɗaya ba ne. Menene bambancinsu? Jiki yana bukatar ruhu kamar yadda rediyo yake bukatar wutar lantarki—domin ya yi magana. Domin ƙarin misali, ka yi tunanin ɗan rediyo. Sa’ad da ka saka batir a cikin rediyo, wutar da take cikin batir ɗin za ta sa rediyon ta yi magana.
Amma idan babu batir sai rediyon ya mutu. Haka kuma rediyon da aka cire daga wutan lantarki. Hakazalika, ruhu shi ne iko da ke ba da rai ga jiki. Kuma kamar wutar lantarki ruhun ba shi da motsin zuciya ko tunani. Iko ne ba mutum ba. Amma idan ba tare da ruhun ba ko kuma rai, ‘jikinmu sai ya mutu ya koma turɓaya,’ kamar yadda mai zabura ya faɗa.Da yake magana game da mutuwar mutum, Mai-Wa’azi 12:7 ta ce: “Ƙura [na jikinsa] kuma ta sake koma cikin ƙasa kamar dā, ruhu kuma ya komo wurin Allah wanda ya bayar.” Sa’ad da ruhu, ko kuma rai, ya fita daga jiki, jiki sai ya mutu ya koma inda ya fito—ƙasa. Haka nan, rai yake komawa wurin wanda ya ba da shi—Allah. (Ayuba 34:14, 15; Zabura 36:9) Wannan ba ya nufin cewa rai ainihi yana tafiya zuwa sama. Maimakon haka, yana nufi ne cewa ga wanda ya mutu, dukan wani begen rayuwa a nan gaba ya dangana ne ga Jehobah Allah. Ransa yana hannun Allah. Sai ta wajen ikon Allah ne ko kuma ruhu, za a iya sake ba da rai saboda mutumin ya sake rayuwa.
Yana kwantar da hankali mu sani cewa haka Allah ya nufa ya yi ga dukan waɗanda suke hutu cikin “kabarbaru” da Allah ya yi niyyar tunawa da su! (Yohanna 5:28, 29) A lokacin tashin matattu, Jehobah zai sake ba da sabon jiki ga wanda yake barcin mutuwa kuma ya sake raya shi ta wajen ba shi ruhu, ko kuma rai. Wannan hakika zai kasance rana ta farin ciki!
Idan kana so ka ƙara fahimtar kalmomin nan “kurwa” da “ruhu” kamar yadda aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki, za ka sami bayani mai muhimmanci cikin mujallar nan Menene Yake Faruwa da mu Sa’ad da Muka Mutu? da kuma a shafuffuka na 375-384 na littafin nan Reasoning From the Scriptures, duka Shaidun Jehobah ne suka wallafa.