Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA UKU

Menene Allah ya Nufa ga Duniya?

Menene Allah ya Nufa ga Duniya?
  • Menene Allah ya nufa ga ’yan adam?

  • Ta yaya aka ƙalubalanci Allah?

  • Yaya rayuwa a duniya za ta kasance a nan gaba?

1. Menene Allah ya nufa ga duniya?

ABIN da Allah ya nufa ga duniya babu shakka abin sha’awa ne. Jehobah yana so duniya ta cika da mutane masu ƙoshin lafiya da farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “ya dasa gona . . . a cikin Adnin” kuma ya sa “kowane itacen da ke mai-sha’awan gani, masu-kyau kuwa domin ci.” Bayan da Allah ya halicci mata da miji na farko, Adamu da Hawa’u, ya sa su a gida mai ni’ima, ya kuma ce musu: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Farawa 1:28; 2:8, 9, 15) Saboda haka nufin Allah ne mutane su haifi ’ya’ya, su faɗaɗa aljanna ta cika dukan duniya, kuma su kula da dabbobi da ke cikinta.

2. (a) Ta yaya muka san cewa abin da Allah ya nufa ga duniya zai cika? (b) Wane irin mutane ne Littafi Mai Tsarki ya ce za su rayu har abada?

2 Kana tsammanin nufin nan na Jehobah Allah, mutane su rayu cikin aljanna a duniya zai taɓa yiwuwa kuwa? “Na faɗi,” Allah ya ce, “zan kuwa aika.” (Ishaya 46:9-11; 55:11) Babu shakka, Allah zai yi abin da ya nufa! Ya ce ya halicci duniya “ba wofi ba, ya kamanta ta domin wurin zama.” (Ishaya 45:18) Waɗanne irin mutane Allah yake so su zauna a cikin duniya? Kuma har tsawon wane lokaci yake so su zauna a cikinta? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: ‘Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.’Zabura 37:29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

3. Wane irin yanayi ne na taƙaici ya samu a duniya, kuma wace tambaya wannan ya jawo?

3 A bayyane yake cewa wannan bai faru ba tukuna. A yau mutane suna tsufa kuma suna mutuwa; suna faɗa suna kashe juna. Akwai abin da ya faru. Hakika, Allah bai nufi duniya ta kasance kamar yadda muke ganinta a yau ba! Menene ya kawo haka? Me ya sa nufin Allah bai cika ba? Babu wani littafi na tarihi da zai iya ba mu amsa, domin matsalar ta samo asali ne daga samaniya.

ASALIN MAGABCI

4, 5. (a) Waye ainihi ya yi wa Hauwa’u magana ta bakin maciji? (b) Ta yaya mutum adali mai gaskiya zai juya ya zama ɓarawo?

4 Littafin farko na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da abokin gaban Allah da ya bayyana a gonar Aidan. An kwatanta shi da “maciji,” amma ba dabba ba ne. Littafin ƙarshe na Littafi Mai Tsarki ya kira shi “Iblis da Shaiɗan, mai-ruɗin dukan duniya.” An kira shi ‘tsohon macijin.’ (Farawa 3:1; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Wannan mala’ika mai iko, ko kuma halittar ruhu, ya yi amfani da maciji ya yi wa Hauwa’u magana, kamar yadda mutane masu iyawa sai su yi magana, muryarsu ta kasance kamar ta fito ne daga ’yar tsana. Babu shakka cewa wannan ruhun yana wajen sa’ad da Allah ya shirya duniya domin mutane.—Ayuba 38:4, 7.

5 Tun da dukan halittun Jehobah kamiltattu ne, to, wa ya halicci wannan “Iblis” “Shaiɗan”? A taƙaice, ɗaya daga cikin mala’iku ’ya’yan Allah ne ya mai da kansa Iblis. Wannan zai yiwu kuwa? Hakika, a yau mutumin da ya kasance adali mai gaskiya zai iya juya ya zama ɓarawo. Ta yaya wannan zai faru? Idan mutumin ya ƙyale baƙin muradi ya cika zuciyarsa. Idan ya ci gaba da saƙa shi a zuciya, wannan muradin sai ya fi ƙarfinsa. Sa’ad da kuma ya sami zarafi, sai ya bi zuciyarsa.—Yaƙub 1:13-15.

6. Ta yaya ruhu ɗan Allah mai iko ya zama Shaiɗan Iblis?

6 Abin da ya faru ke nan da Shaiɗan Iblis. Hakika ya ji sa’ad da Allah ya faɗa wa Adamu da Hauwa’u su haifi ’ya’ya su cika duniya. (Farawa 1:27, 28) Wataƙila Shaiɗan sai ya yi tunani, ‘Ai, gara waɗannan mutane su bauta mini maimakon su bauta wa Allah!’ Baƙin muradi ya kahu a zuciyarsa. Sai, ya bi zuciya ya yaudari Hauwa’u, ya yi mata ƙarya game da Allah. (Farawa 3:1-5) Saboda haka ya zama “Iblis,” wanda yake nufin “Maƙaryaci.” Haka nan kuma ya zama “Shaiɗan,” wanda yake nufin “Abokin gaba.”

7. (a) Me ya sa Adamu da Hauwa’u suka mutu? (b) Me ya sa dukan zuriyar Adamu suke tsufa kuma suke mutuwa?

7 Ta wajen ƙarya da yaudara, Shaiɗan Iblis ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya. (Farawa 2:17; 3:6) Saboda haka, mutuwa ta same su, kamar yadda Allah ya ce za ta kasance a gare su idan suka yi rashin biyayya. (Farawa 3:17-19) Tun da Adamu ya zama ajizi domin zunubi, dukan zuriyarsa suka gāji zunubi daga wurinsa. (Romawa 5:12) Za a iya kwatanta wannan yanayin da gwangwanin gasa burodi. Idan gwangwanin ya lanƙwashe, mai zai sami burodin da za a gasa a cikinsa? Kowane burodi zai kasance da lanƙwasa, ko kuma ajizanci. Hakazalika, dukan ’yan adam suka gaji “lanƙwasa” ta ajizanci daga Adamu. Abin da ya sa ke nan dukan mutane suke tsufa kuma suke mutuwa.—Romawa 3:23.

8, 9. (a) Menene Shaiɗan yake nufi a ƙalubalantar da ya yi? (b) Me ya sa Allah bai halaka ’yan tawayen ba a take?

8 Sa’ad da Shaiɗan ya ja-goranci Adamu da Hauwa’u su yi zunubi ga Allah, yana ja-gorarsu ne wajen tawaye. Yana ƙalubalantar yadda Jehobah yake sarauta. Wato Shaiɗan cewa yake: ‘Allah mugun sarki ne. Maƙaryaci ne azzalumi kuma yana hana talakawansa abubuwa masu kyau. Mutane ba sa bukatar Allah ya mallake su. Za su iya kafa wa kansu abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. Kuma ya fi musu su kasance a ƙarƙashin mallakata.’ Ta yaya Allah zai yi maganin irin wannan tuhuma? Wasu sun ce da Allah ya kashe ’yan tawayen kawai. Amma da wannan zai mai da martani ga ƙalubalanci na Shaiɗan kuwa? Da wannan ya tabbatar da cewa yadda Allah yake sarauta daidai ne?

9 Kamiltaccen hukuncin Jehobah ba zai ƙyale shi ya kashe ’yan tawayen nan da nan ba. Ya yanke shawarar cewa ana bukatar lokaci domin a mai da martani ga ƙalubalanci na Shaiɗan a hanya mai gamsarwa da za ta tabbatar da cewa Iblis maƙaryaci ne. Saboda haka Allah ya ƙyale mutane su mallaki kansu na ɗan lokaci a ƙarƙashin rinjayar Shaiɗan. Za a tattauna abin da ya sa Jehobah ya ƙyale lokaci mai tsawo ya shige kafin ya magance wannan batu a Babi na 11 na wannan littafi. Amma a yanzu, yana da kyau mu yi tunani game da wannan: Shin Adamu da Hauwa’u suna da wani dalilin da ya sa za su yarda da abin da Shaiɗan ya ce ne, shi da bai taɓa yi musu wani abin kirki ba? Daidai ne su yarda cewa Jehobah, wanda ya ba su dukan abin da suka mallaka, mugun maƙaryaci ne? Da kai ne me za ka yi?

10. Ta yaya za ka goyi bayan Jehobah domin ka mai da martani ga ƙalubalanci na Shaiɗan?

10 Yana da kyau mu yi tunani a kan waɗannan tambayoyi domin kowannenmu yana fuskantar irin wannan batu a yau. Hakika, kana da damar ka goyi bayan Jehobah domin ka mai da martani ga ƙalubalanci na Shaiɗan. Kana iya yarda Jehobah ya Mallake ka, kuma ka taimaka ka tabbatar da Shaiɗan maƙaryaci ne. (Zabura 73:28; Misalai 27:11) Abin baƙin ciki, mutane kalilan ne kawai a tsakanin biliyoyin mutane da suke wannan duniya suka zaɓi su yi haka. Wannan ya kawo wata muhimmiyar tambaya, Shin Littafi Mai Tsarki ya koyar ne da cewa Shaiɗan ne yake mallakar wannan duniyar?

WAYE YAKE MULKIN WANNAN DUNIYAR?

Da Shaiɗan zai yi wa Yesu alkawarin dukan mulkokin duniya idan ba nasa ba ne?

11, 12. (a) Ta yaya jarabtar Yesu ta nuna cewa Shaiɗan shi ne mamallakin wannan duniya? (b) Menene kuma ya tabbatar da cewa Shaiɗan shi ne mamallakin wannan duniya?

11 Yesu bai taɓa yin shakkar cewa Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar ba. A wata hanya mai ban al’ajabi, Shaiɗan ya taɓa nuna wa Yesu “dukan mulkokin duniya, da ɗaukakarsu.” Sai Shaiɗan ya yi wa Yesu alkawari: “Duk waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mani sujada.” (Matta 4:8, 9; Luka 4:5, 6) Ka yi tunanin wannan. Da wannan alkawari zai kasance jarraba ga Yesu idan ba Shaiɗan ba ne yake mallakar dukan waɗannan mulkoki? Yesu bai yi musu ba cewa dukan waɗannan gwamnatoci na duniya na Shaiɗan ne. Babu shakka, da Yesu ya yi haka idan ba Shaiɗan ba ne yake da su.

12 Hakika, Jehobah shi ne Allah Maɗaukaki Sarki, Mahaliccin dukan abu. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Duk da haka, babu inda Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah Allah ko kuma Yesu Kristi ke mallakar wannan duniyar. Saboda haka, a darensa na ƙarshe a duniya, Yesu ya nuna cewa Shaiɗan shi ne “mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31; 14:30; 16:11) Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna mana cewa Shaiɗan Iblis shi ne “allah na wannan zamani.” (2 Korinthiyawa 4:3, 4) Game da wannan abokin gaba, ko kuma Shaiɗan, manzo Yohanna ya rubuta: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.”—1 Yohanna 5:19.

YADDA ZA A KAWAR DA DUNIYAR SHAIƊAN

13. Me ya sa ake bukatar sabuwar duniya?

13 Duk shekara, duniya tana ƙara zama wuri mai haɗari. Ta cika da sojoji da suke yaƙe-yaƙe, ’yan siyasa marasa gaskiya, miyagu masu taurin zuciya. Duniya gaba ɗayanta ta fi gaban a gyara. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa lokaci ya yi kusa da Allah zai kawar da duniyar nan ta mugunta a yaƙinsa na Armageddon. Wannan zai share fage ga sabuwar duniya ta adalci.—Ru’ya ta Yohanna 16:14-16.

14. Waye Allah ya zaɓa ya yi Sarauta a Mulkinsa, kuma ta yaya aka annabta wannan?

14 Jehobah Allah ya zaɓi Yesu Kristi ya zama Sarki a Mulkinsa na samaniya, ko gwamnati. Tun a dā can, Littafi Mai Tsarki ya annabta: “Gama an haifa mana yaro, a garemu an bada ɗa: mulkin za ya kasance a kafaɗarsa: za a ce da sunansa . . . Sarkin Salama. Ƙaruwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka.” (Ishaya 9:6, 7) Game da wannan mulkin, Yesu ya koya wa mabiyansa addu’a: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Kamar yadda za mu gani a nan gaba a wannan littafin, Mulkin Allah ba da daɗewa ba zai kawar da dukan gwamnatocin duniya, kuma shi kansa zai ɗauki matsayin dukansu. (Daniel 2:44) Sa’an nan Mulkin Allah zai kawo aljanna a duniya.

SABUWAR DUNIYA TA YI KUSA!

15. Mecece ce “sabuwar duniya”?

15 Littafi Mai Tsarki ya yi mana tabbaci: “Amma, bisa ga alkawalinsa, muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci ya ke zaune.” (2 Bitrus 3:13; Ishaya 65:17) Sau da yawa idan Littafi Mai Tsarki ya yi maganar “duniya” yana nufin mutane da suke raye a duniya. (Farawa 11:1) “Sabuwar duniya” ta adalci tana nufin mutane da suka sami yardar Allah.

16. Wace kyauta ce mai tamani waɗanda Allah ya yarda da su za su samu, kuma menene za mu yi domin mu same ta?

16 Yesu ya yi alkawari cewa a sabuwar duniya mai zuwa, waɗanda Allah ya yarda da su za su sami kyautar “rai na har abada.” (Markus 10:30) Don Allah ka buɗe Littafinka Mai Tsarki zuwa Yohanna 3:16 da kuma Yohanna 17:3, ka karanta abin da Yesu ya ce dole ne mu yi domin mu sami rai madawwami. Yanzu, ka yi la’akari daga Littafi Mai Tsarki albarkatai da waɗanda suka cancanta za su samu, kyauta mai ban sha’awa daga Allah a Aljanna ta duniya.

17, 18. Ta yaya muka sani cewa a ko’ina a cikin duniya za a sami salama da kwanciyar hankali?

17 Mugunta, yaƙe-yaƙe, yin laifi, da kuma nuna ƙarfi duka za su zama abin da suka shige. “Mai-mugunta ba shi. . . Amma masu-tawali’u za su gāji ƙasan.” (Zabura 37:10, 11) Za a sami zaman lumana domin Allah zai “sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.” (Zabura 46:9; Ishaya 2:4) Sa’an nan “mai-adilci za shi yalwata; da salama mai-yawa, har batun wata ya ƙare,” wato za a yi salama har abada!—Zabura 72:7.

18 Masu bauta wa Jehobah za su zauna cikin kwanciyar hankali. Duk sa’ad da Isra’ilawa na lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki suka yi wa Allah biyayya, suna zama cikin kwanciyar hankali. (Leviticus 25:18, 19) More irin wannan kwanciyar hankali a Aljanna zai kasance abin ban sha’awa.—Ishaya 32:18; Miƙah 4:4.

19. Ta yaya muka sani cewa za a sami yalwar abinci a sabuwar duniya ta Allah?

19 Ba za a yi ƙarancin abinci ba. Mai Zabura ya raira waƙa ya ce: “Za a yi albarkar hatsi a ƙasa a bisa ƙwanƙolin duwatsu.” (Zabura 72:16) Jehobah Allah zai albarkaci mutanensa masu adalci, kuma “ƙasa tā bada anfaninta.”—Zabura 67:6.

20. Me ya sa za mu tabbata cewa dukan duniya za ta zama aljanna?

20 Duniya duka za ta zama aljanna. Za a gina gidaje a kuma dasa lambuna a wuri da mutane masu zunubi suka lalata. (Ishaya 65:21-24; Ru’ya ta Yohanna 11:18) Da shigewar lokaci, ɓangarorin duniya da aka riga aka mallaka za a faɗaɗa shi har sai dukan duniya ta kyawanta ta zama mai amfani kamar gonar Aidan. Kuma Allah zai buɗe hannayensa ya “biya ma kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura 145:16.

21. Menene ya nuna cewa za a sami salama tsakanin mutane da dabbobi?

21 Za a sami salama tsakanin mutane da dabbobi. Dabbobin daji za su yi kiwo tare da na gida. Har jariri ma ba zai ji tsoron dabbobi ba da yanzu suke da haɗari.—Ishaya 11:6-9; 65:25.

22. Menene zai faru da cututtuka?

22 Cututtuka za su shuɗe. Sarkin Mulkin sama na Allah, Yesu zai warkar da mutane fiye da yadda ya warkar da su sa’ad da yake duniya. (Matta 9:35; Markus 1:40-42; Yohanna 5:5-9) Sa’an nan “wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, ina ciwo ba.”— Ishaya 33:24; 35:5, 6.

23. Me ya sa tashin matattu zai faranta mana rai?

23 Za a dawo da matattu zuwa rai kuma za su kasance da begen dawwama. Dukan waɗanda suka mutu da Allah yake tunawa da su zai tashe su zuwa rai. Hakika, “za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.”—Ayukan Manzanni 24:15; Yohanna 5:28, 29.

24. Yaya ka ji game da rayuwa a Aljanna ta duniya?

24 Waɗanda suka zaɓi su koyi game da Mahaliccinmu, Jehobah Allah, kuma su bauta masa, rayuwa mai ban sha’awa ta nan gaba na jiransu! Yesu yana maganar wannan Aljanna ta duniya da take zuwa ne sa’ad da ya yi alkawari ga mai laifi da ya mutu a gefensa: “Yau kana tare da ni a cikin [Aljanna].” (Luka 23:43) Yana da muhimmanci mu yi koyi game da Yesu Kristi, wanda dukan waɗannan albarkatai za su samu ta hannunsa.