RATAYE
Ya Kamata Ne Mu Kiyaye Ranaku Masu Tsarki?
BA LITTAFI MAI TSARKI ba ne tushen ranaku masu tsarki na addinai da na gwamnati da suka yi kaurin suna a yawancin ɓangarorin duniya a yau. Menene tushen wannan bukukuwa? Idan kana iya zuwa laburare, za ka yi farin ciki idan ka
duba abin da littattafai suka ce game da ranaku masu tsarki da suka yi fice a inda kake da zama. Ga wasu misali.Ista. “Babu alamar an kiyaye bikin Ista a Sabon Alkawari,” in ji The Encyclopædia Britannica. Ta yaya Ista ta samo asalinta? Tushenta daga bautar arna ne. Ko da yake an tuna da tashin Yesu daga matattu, ayyuka da ake yi a Ista ba na Kiristoci ba ne. Alal misali, game da fitaccen “ɗan zomo na Ista,” littafin nan The Catholic Encyclopedia ya ce: “Zomon alama ce ta arna, alamar haihuwa.”
Bikin Sabuwar Shekara. Lokaci da kuma yadda ake yin bikin Sabuwar Shekara ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Game da tushen wannan biki, littafin nan The World Book Encyclopedia ya ce: Barome Yuliyas Kaisar a shekara ta 46 K.Z., ya kafa 1 ga Janairu, a matsayin Ranar Sabuwar Shekara. Romawa suka keɓe wannan ranar ga Janus, allahn ƙofofi, da mafari. An samo sunan Janairu daga Janus, wanda yake da fuskoki biyu—ɗaya na duban gaba ɗayan kuma baya.” Saboda haka, bikin Sabuwar Shekara ya samo asalinsa ne daga al’adar arna.
Halloween. The Encyclopedia Americana ya ce: “Al’adun wannan bikin an samo su ne a lokacin [firistocin Seltikawa] kafin lokacin Kiristoci. Bikin na Seltikawa suna yin shi ne domin allolinsu biyu, ga rana da suke bauta da kuma allahn mutuwa . . . , wanda ake yin bikin dominsu a ranar 1 ga Nuwamba, a farkon Sabuwar Shekara ga Seltikawa. An saka biki ga matattu a cikin Kiristanci sanu a hankali.”
Wasu Ranaku Masu Tsarki. Ba zai yiwu a tattauna dukan bukukuwa da ake yi a duniya ba. Amma, dukan bikin da ake yi don a ɗaukaka mutane ko ƙungiyoyi, Jehobah Allah bai yarda da wannan ba. (Irmiya 17:5-7; Ayukan Manzanni 10:25, 26) Ka tuna cewa tushen biki na addini zai nuna ko Allah ya yarda da shi ko a’a. (Ishaya 52:11; Ru’ya ta Yohanna 18:4) Mizanan Littafi Mai Tsarki da aka ambata a Babi na 16 na wannan littafin za su taimake ka ka fahimci yadda Allah yake ɗaukan ranaku masu tsarki na gwamnati.