SASHE NA 7
Alkawuran Mulkin—Sabonta Dukan Abu
KA TSINKA wani babban nunannen mangwaro daga itace, ka tattaɓa shi, sa’an nan ka saka shi cikin kwando. Ka riga ka kwashi sa’o’i kana aiki amma ba ka gaji ba. Mahaifiyarka kuma tana wani itace da ke kusa, tana aiki da farin ciki yayin da take tattaunawa da wasu danginku da kuke girbin tare. Tana nan matashiya yadda ka san ta shekaru da yawa sa’ad da kake yaro. Ka tuna sa’ad da ta tsufa, ta yi ciwo, kuma ka riƙe hannunta sa’ad da ta mutu a tsohuwar duniya. Ka kuma tuna yadda ka yi kuka a lokacin jana’izarta. Amma yanzu, ga ta da rai da koshin lafiya tare da wasu!
Mun tabbata cewa waɗannan abubuwan za su faru. Mun san da haka domin Allah ba ya saɓa alkawuransa. A wannan sashen, za mu tattauna yadda za a cika wasu alkawura game da Mulkin Allah nan ba da daɗewa ba har zuwa lokacin yaƙin Armageddon. Za mu kuma tattauna wasu alkawura masu ban al’ajabi game da Mulkin da za su cika bayan yaƙin. Babu shakka, za mu yi matuƙar farin ciki sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta bisa dukan duniya kuma ya sa sabonta dukan abu!
A WANNAN SASHEN
BABI NA 22
Mulkin Ya Sa Ana Yin Nufin Allah a Duniya
Me ya sa ka tabbata cewa alkawuran Jehobah za su cika?