BABI NA 16
Yin Taro don Ibada
1. Wane taimako ne almajiran Yesu suka samu sa’ad da suka taru, kuma me ya sa suka bukaci wannan taimakon?
ALMAJIRAN Yesu sun taru don su ƙarfafa juna jim kaɗan bayan an ta da shi daga mutuwa. Kuma sun rurrufe ƙofofin ɗakin da suke yin taron domin suna tsoron magabtansu. Amma wannan tsoron da suke ji ya ɓace sa’ad da Yesu ya bayyana a tsakaninsu kuma ya ce: “Ku karɓi ruhu mai tsarki.” (Karanta Yohanna 20:19-22.) Bayan haka, almajiran sun sake yin taro kuma Jehobah ya cika su da ruhu mai tsarki. Hakan ya ba su ƙarfin ci gaba da yin wa’azi da gaba gaɗi!—A. M. 2:1-7.
2. (a) Ta yaya Jehobah yake mana tanadi, kuma me ya sa muke bukatar wannan taimakon? (b) Me ya sa Ibada ta Iyali yake da muhimmanci? (Ka duba ƙarin bayani da kuma akwatin nan “ Ibada ta Iyali,” shafi na 175.)
2 Muna fuskantar irin matsalolin da ’yan’uwanmu na ƙarni na farko suka fuskanta. (1 Bit. 5:9) A wasu lokatai, tsoron mutane yana iya kama wasu daga cikinmu. Muna bukatar taimakon Jehobah don mu ci gaba da yin wa’azi. (Afis. 6:10) Jehobah yana yi mana tanadin abin da muke bukata ta hanyar taron da muke yi. A yanzu haka, muna da damar halartan taro guda biyar a mako, wato Taro don Jama’a da Nazarin Hasumiyar Tsaro da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya da Makarantar Hidima ta Allah da kuma Taron Hidima. a Ƙari ga haka, muna more wasu manyan taro guda huɗu a shekara, wato, taron yanki da taron da’ira guda biyu da kuma taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci dukan taron nan? Ta yaya muka soma gudanar da taro a zamaninmu? Kuma mene ne ra’ayinmu game da taro zai nuna game da mu?
Me Ya Sa Muke Yin Taro?
3, 4. Mene ne Jehobah yake bukata daga bayinsa? Ka ba da misalai.
3 Tun da daɗewa Jehobah ya bukaci bayinsa su riƙa yin taro don su bauta masa. Alal misali, a Dokar da Allah ya ba wa al’ummar Isra’ila a shekara ta 1513 kafin zamaninmu, Jehobah ya umurce su su riƙa kiyaye ranar Assabaci don kowace iyali ta bauta wa Allah kuma ta san Dokarsa sosai. (K. Sha 5:12; 6:4-9) Sa’ad da Isra’ilawa suka bi wannan umurnin, iyalansu sun sami ƙarfafawa kuma al’ummar gaba ɗaya ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Amma, sa’ad da Isra’ilawa suka ƙi bin Doka, kamar wadda ta ce su riƙa yin taro don su bauta wa Jehobah, hakan ya sa sun rasa tagomashin Allah.—Lev. 10:11; 26:31-35; 2 Laba. 36:20, 21.
4 Ka yi la’akari kuma da misalin da Yesu ya kafa. Yana zuwa haikali a kowane mako a Assabaci. (Luk 4:16) Bayan mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu, almajiransa sun ci gaba da yin taro duk da cewa sun daina bin dokar Assabaci a lokacin. (A. M. 1:6, 12-14; 2:1-4; Rom. 14:5; Kol. 2:13, 14) A irin waɗannan taron, Kiristoci na ƙarni na farko suna samun koyarwa da ƙarfafawa, kuma suna yabon Allah da addu’o’insu da kalamansu da kuma waƙoƙinsu.—Kol. 3:16; Ibran. 13:15.
5. Me ya sa muke halartan taron mako-mako da kuma manyan taro? (Ka duba akwatin nan “ Taron Shekara-Shekara Suna Haɗa Kan Bayin Allah,” shafi na 176.)
5 Hakazalika, idan muka halarci taronmu na mako-mako da kuma manyan taro, muna nuna goyon baya ne ga Mulkin Allah, kuma za mu sami ƙarfi daga ruhu mai tsarki kuma mu ƙarfafa wasu da kalamanmu masu kyau. Abu mafi muhimmanci shi ne, muna da damar bauta wa Jehobah ta hanyar addu’o’inmu da kalamanmu da kuma waƙoƙinmu. Ko da yake yadda aka tsara taronmu a yau ya bambanta da na Isra’ilawa da kuma na Kiristoci a ƙarni na farko, amma taron suna da muhimmanci sosai. Ta yaya muka soma gudanar da taro a zamaninmu?
Taron Mako-Mako da ke Ƙarfafa “Ƙauna da Nagargarun Ayyuka”
6, 7. (a) Mece ce manufar taron da muke yi? (b) Ta yaya yadda ake gudanar da taro a dā ya bambanta daga rukuni zuwa rukuni?
6 A lokacin da Ɗan’uwa Charles Taze Russell ya soma yin bincike don samun gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah, ya ga cewa yin taro da waɗanda suke da irin maƙasudinsa yana da muhimmanci. A shekara ta 1879, Ɗan’uwa Russell ya rubuta cewa: “Ni da wasu a birnin Pittsburgh, mun kafa rukuni don bincika Nassosi, kuma muna yin taro a kowace Lahadi.” An ƙarfafa masu karanta Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) su riƙa yin taro. An soma yin taron a shekara ta 1881, sau biyu a mako, a ranar Lahadi da Laraba a birnin Pittsburgh, a Pennsylvania. Hasumiyar Tsaro ta Nuwamba 1895 ta ce manufar waɗannan taron da ake yi ita ce don mu riƙa yin “zumuntar Kirista kuma mu kasance da ƙauna da haɗin kai” kuma mu ba waɗanda suka halarta damar ƙarfafa juna.—Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.
7 A shekaru da yawa, yadda Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke gudanar da taro ya bambanta daga rukuni zuwa rukuni. Alal misali, wata wasiƙar da wani rukuni a Amirka ya rubuta kuma aka wallafa ta a shekara ta 1911 ta ce: “Muna yin taro aƙalla sau biyar a mako.” Suna yin waɗannan taron a ranar Litinin da Laraba da Jumma’a da kuma sau biyu a ranar Lahadi. Wata wasiƙar kuma da wani rukuni a Afirka ya rubuta, kuma aka wallafa ta a shekara ta 1914 ta ce: “Muna yin taro sau biyu a wata, muna somawa a ranar Jumma’a kuma mu kammala a ranar Lahadi.” Amma a kwana a tashi, sai aka kafa tsarin da muke bi a yau wajen gudanar da taronmu. Yanzu za mu ɗan tattauna tarihin kowane taro.
8. Mene ne jigon wasu jawabai ga jama’a da aka yi a dā?
8 Taro don Jama’a. A shekara ta 1880, bayan Ɗan’uwa Russell ya soma wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona, ya bi gurbin Yesu ta wajen soma yin wa’azi a wurare dabam-dabam. (Luk 4:43) Ana cikin hakan ne, Ɗan’uwa Russell ya kafa mana gurbin da muke bi a yau na yin Taro don Jama’a. Sa’ad da take sanar da tafiyarsa, Hasumiyar Tsaro ta ce Ɗan’uwa Russell “zai yi farin cikin yi wa jama’a jawabi a kan ‘Al’amuran mulkin Allah.’” A shekara ta 1911, bayan an kafa azuzuwa ko kuma ikilisiyoyi a ƙasashe da dama, an ƙarfafa kowane aji ya tura waɗanda suka iya jawabi zuwa yankunan da ke kewaye da su don su ba da jawabai guda shida da suka tattauna batutuwa kamar su shari’a da fansa da dai sauransu. A ƙarshen kowane jawabi, ana sanar da jigon jawabi na mako mai zuwa da kuma sunan wanda zai ba da jawabin.
9. Waɗanne canji ne aka yi a Taro don Jama’a, kuma ta yaya za ka iya goyon bayan wannan taron?
9 A shekara ta 1945, Hasumiyar Tsaro ta sanar da cewa za a soma gudanar da Taro don Jama’a a duk faɗin duniya, kuma za a ba da jawabai ne guda takwas da suka tattauna “matsaloli na gaggawa da ake fuskanta a lokacin.” A shekaru da dama, masu ba da jawabi suna tattauna jigon da bawan nan mai aminci ya bayar da kuma wanda su da kansu suka shirya. Amma a 1981, an umurci dukan masu ba da jawabi su yi amfani da awutlayin da ikilisiya ta ba su. b Har zuwa shekara ta 1990, wasu jawabai sun kunshi gwaji ko kuma wuraren da masu sauraro za su yi kalami. Amma a wannan shekarar ce aka canja hakan, kuma aka soma ba da jawabai zalla. An yi wani canjin a watan Janairu 2008, sa’ad da aka rage lokacin jawaban daga minti 45 zuwa 30. Ko da yake an canja tsarin wannan taron sau da sau, amma jawaban sun ci gaba da taimaka wa mutane su dogara ga Kalmar Allah kuma jawaban suna koyar da mu abubuwa dabam-dabam game da Mulkin Allah. (1 Tim. 4:13, 16) Shin kana gayyatar waɗanda kake tattauna Littafi Mai Tsarki da su da kuma sauran waɗanda ba Shaidu ba don su zo su saurari waɗannan jawabai masu muhimmanci da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki?
10-12. (a) Waɗanne canji ne aka yi a yadda ake gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro? (b) Waɗanne tambayoyi ne zai dace mu yi wa kanmu?
10 Nazarin Hasumiyar Tsaro. A shekara ta 1922, masu kula masu ziyara da Watch Tower Society ta tura zuwa ikilisiyoyi su ba da jawabai kuma su ja-gorance su a yin wa’azi sun ba da shawara cewa a soma gudanar da wani taro musamman don yin nazarin Hasumiyar Tsaro. An bi wannan shawarar kuma aka soma yin nazarin Hasumiyar Tsaro a tsakiyar mako ko kuma a ranar Lahadi.
11 Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni 1932 ta ba da umurni a kan yadda za a gudanar da taron. Talifin ya ce ɗan’uwa ne ya kamata ya gudanar da taron, kamar yadda ake yi a Bethel. ’Yan’uwa maza su uku za su iya zauna a gaba kuma su riƙa karanta sakin layin karɓa–karɓa. A lokacin, talifofin ba su da tambayoyi, saboda haka, mai gudanar da taron ne zai riƙa ba masu sauraro damar su ƙirƙiro tambayoyin a kan talifin da ake tattaunawa. Bayan haka, zai kira mutane daga cikin masu sauraron su amsa tambayoyin. Idan ana bukatar ƙarin bayani, mai gudanar da taron zai yi bayani “daidai-wa-daida.”
12 Da farko, an yarda kowace ikilisiya ta yi nazarin mujallar da yawancin ’yan’uwa suka zaɓa. Amma a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1933, an shawarci dukan ikilisiyoyi su riƙa nazarin sabbin talifofin da aka wallafa. A 1937, an ba da umurni cewa a riƙa yin wannan nazarin a ranar Lahadi. A cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 1942, an sake yin wasu gyaran da muke bi a yau. Da farko, wannan mujallar ta sanar da cewa za a wallafa tambayoyi a ƙarƙashin kowane shafin talifofin nazari, kuma tambayoyin ne za a yi amfani da su. Bayan haka, ta ambata cewa taron zai ɗauki awa ɗaya, kuma ta ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa yin kalamai “a nasu kalmomin” maimakon su karanta amsoshin daga sakin layin. Har wa yau, Nazarin Hasumiyar Tsaro ce hanya ta musamman da bawan nan mai aminci yake ci gaba da yi mana tanadi a kan kari don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. (Mat. 24:45) Zai dace kowannenmu ya yi wa kansa waɗannan tambayoyin: ‘Ina shirya nazarin Hasumiyar Tsaro a kowane mako kuwa? Ina ƙoƙarin yin kalami kuwa idan da hali?’
13, 14. Waɗanne canji ne aka yi a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, kuma mene ne yake burge ka game da wannan taron?
13 Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. A tsakanin shekara ta 1895 zuwa 1897, bayan an fitar da kundayen littafin nan Millennial Dawn, wani Ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai suna, H. N. Rahn da ke da zama a birnin Baltimore, Maryland a Amirka, ya ba da shawara cewa a kafa “Dawn Circles,” wato rukunin masu nazarin Millennial Dawn. Da farko, an gwada yin waɗannan taron a gidajen mutane. Amma a watan Satumba 1895, an yi nasarar kafa waɗannan rukunin a birane da dama a ƙasar Amirka. Hasumiyar Tsaro na watan Satumba ta shawarce dukan ɗaliban Littafi Mai Tsarki a ko’ina su riƙa yin waɗannan taron. Mujallar ta kuma ce ya kamata wanda zai gudanar da taron ya zama wanda ya iya karatu sosai. Zai riƙa karanta jimla kuma ya ba masu sauraro dama su yi kalami. Bayan ya karanta kowace jimlar da ke sakin layin kuma an tattauna ta, sai ya karanta nassosin da ke wurin. A ƙarshen babin, dukan waɗanda suka halarci taron za su yi taƙaitaccen bayani a kan abin da suka koya.
14 An canja sunan wannan taron sau da sau. An kira shi Rukunin Nazarin Littafi Mai Tsarki na Biriya, domin yadda mutanen Biriya a ƙarni na farko suka duƙufa a yin bincika Nassosi. (A. M. 17:11) A kwana a tashi, an canja sunan zuwa Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya. A yanzu ana kiransa Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, kuma dukan ’yan’uwa suna taruwa ne a Majami’ar Mulki maimakon rukunoni a gidajen mutane. A shekaru da dama, an yi amfani da littattafai da ƙasidu dabam-dabam, har da wasu talifofin Hasumiyar Tsaro a wannan taron. Tun daga farko, ana ƙarfafa dukan waɗanda suka halarci wannan taron su yi kalami. Wannan taron ya taimaka mana mu daɗa fahimtar Littafi Mai Tsarki. Shin kana shirya wannan taron sosai kuma kana iya ƙoƙarinka wajen yin kalami kuwa?
15. Mece ce manufar Makarantar Hidima ta Allah?
15 Makarantar Hidima ta Allah. Ɗan’uwa Carey Barber, wanda ya yi hidima a hedkwatarmu da ke Brooklyn a Amirka, ya ce: “A daren Litinin, 16 ga Fabrairu, 1942, an gaya wa dukan ’yan’uwa maza da ke hidima a Bethel na Brooklyn su shiga makaranta da yanzu ake kira Makarantar Hidima ta Allah.” Ɗan’uwa Barber ya zama ɗaya daga cikin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, kuma ya ce wannan makarantar “ɗaya ne daga cikin ci gaba na musamman da aka shaida a yadda Jehobah yake bi da mutanensa a zamaninmu.” Makarantar ta taimaka wa ’yan’uwa maza su zama ƙwararrun masu koyarwa da kuma wa’azi, shi ya sa daga shekara ta 1943, aka ba dukan ikilisiyoyi ƙasidar nan Course in Theocratic Ministry. A ranar 1 ga Yuni, 1943, Hasumiyar Tsaro ta ce an tsara Makarantar Hidima ta Allah ne don a taimaka wa bayin Allah su “horar da kansu don su iya yin wa’azin Mulkin da kyau.”—2 Tim. 2:15.
16, 17. Shin Makarantar Hidima ta Allah tana koya mana yin jawabi ne kawai? Ka bayyana.
16 Da farko, ’yan’uwa da yawa ba sa iya yin jawabi a gaban jama’a. Ɗan’uwa Clayton Woodworth Junior, wanda aka saka mahaifinsa da Ɗan’uwa Rutherford da kuma wasu a fursuna a shekara ta 1918 ya tuna da yadda ya ji a lokacin da ya shiga wannan makarantar a shekara ta 1943. Ya ce: “Ba da jawabi yana yi mini wuya sosai. Sai in ji kamar harshena yana daɗa tsawo, bakina kuma yana ta bushewa, sa’an nan muryata kuma ta zama kamar rurin zaki.” Amma yayin da Clayton ya daɗa ƙwarewa, sai ya sami gatan ba da jawabai da yawa. Makarantar ta koya masa yadda zai ba da jawabi. Ƙari ga haka, ta koya masa muhimmancin kasancewa da tawali’u da kuma dogara ga Jehobah. Ya ce: “Na fahimci cewa ƙwarewar mai ba da jawabi ba wani abu ba ne. Amma idan ya shirya da kyau kuma ya dogara ga Jehobah, masu sauraro za su ji daɗin jawabinsa kuma za su koyi darasi.”
17 A shekara ta 1959, ’yan’uwa mata sun sami shiga wannan makarantar. ’Yar’uwa Edna Bauer ta tuna lokacin da aka yi sanarwar a wani babban taron da ta halarta. Ta ce: “Na tuna irin farin cikin da ’yan’uwa mata suka yi. Yanzu sun daɗa samun zarafin koyo.” Ko da kai namiji ne ko kuma tamace, za ka amfana daga wannan damar idan ka zama ɗalibi a Makarantar Hidima ta Allah don Jehobah ya koyar da kai.—Karanta Ishaya 54:13.
18, 19. (a) Bisa wane tsari ne aka kafa Taron Hidima? (b) Me ya sa muke rera waƙa a taronmu? (Ka duba akwatin nan “ Sanar da Gaskiya ta Wajen Rera Waƙa.”)
18 Taron Hidima. Tun shekara ta 1919, ana yin taro don koyar da mutane game da yin wa’azi. A lokacin, waɗanda za su fita rarraba littattafai ne kawai suke halartar wannan taron. Daga shekara ta 1923, an soma Taron Hidima sau ɗaya a wata, wanda dukan masu shela a ikilisiya za su iya halarta. A shekara ta 1928, an ƙarfafa ikilisiyoyi su riƙa yin wannan taron kowane mako, sa’an nan a shekara ta 1935, Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa ikilisiyoyi su riƙa gudanar da Taron Hidima bisa ga bayanin da ke cikin Hidimarmu ta Mulki (wanda aka kira Director da kuma Informant a dā). Ba da daɗewa ba, wannan taron ya zama ɗaya daga cikin taron da kowace ikilisiya ke yi.
19 Har wa yau, ana gudanar da Taron Hidima bisa ga tsarin da Yesu ya kafa na koyar da mutane don su yi wa’azi da kyau. (Mat. 10:5-13) Idan kana cikin waɗanda ake ba Hidimarmu ta Mulki, shin kana yin nazarinsa kuma ka yi amfani da shawarwarin da ke ciki sa’ad da kake yin wa’azi?
Taro Mafi Muhimmanci a Shekara
20-22. (a) Me ya sa muke tunawa da mutuwar Yesu? (b) Ta yaya kake amfana daga halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu kowace shekara?
20 An gaya wa mabiyan Yesu su riƙa tuna da mutuwarsa har sai dawowarsa. Ana yin Taron Tuna da Mutuwar Yesu a kowace shekara, kamar yadda ake yin Idin Ƙetarewa. (1 Kor. 11:23-26) Miliyoyin mutane suna halartan wannan taron kowace shekara, kuma yana sa shafaffu su tuna da gatan da suke da shi na yin sarauta tare da Kristi. (Rom. 8:17) Ga wasu tumaki kuma, wannan taron yana sa su girmama Sarkin Mulkin Allah kuma su kasance da aminci a gare shi.—Yoh. 10:16.
21 Ɗan’uwa Russell da abokansa sun fahimci muhimmancin tunawa da mutuwar Yesu kuma sun san cewa ya kamata a yi hakan sau ɗaya a shekara. Hasumiyar Tsaro ta watan Afrilu 1880 ta ce: “Cikin shekaru da dama, ya zama al’adarmu a nan Pittsburgh mu riƙa tuna da Idin Ƙetarewa [Tunawa da Mutuwar Yesu] kuma mu ci gurasa mu sha ruwan inabin da ke wakiltar jiki da jinin Ubangijinmu.” Ba da daɗewa ba, an soma yin manyan taro a lokaci ɗaya da Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Taro na farko da aka adana rahotonsa shi ne wanda aka yi a shekara ta 1889, wanda mutane 225 suka halarta kuma 22 suka yi baftisma.
22 A yau, ba ma yin taron tunawa da mutuwar Yesu a babban taro. Duk da haka, muna gayyatar mutanen da ke yankinmu su halarci taron tunawa da mutuwar Yesu tare da mu a Majami’ar Mulki a yankinmu ko a wani wurin da aka yi haya. A shekara ta 2013, mutane fiye da miliyan 19 ne suka tuna da mutuwar Yesu. Hakika babban gata ne a gare mu mu halarta kuma mu gayyaci mutane su halarci taron tare da mu a wannan dare mafi muhimmanci! Shin kana ƙwazo sosai kowace shekara wajen gayyatar mutane da yawa zuwa Tunawa da Mutuwar Yesu?
Abin da Ra’ayinmu Yake Nunawa
23. Mene ne ra’ayinka game da taronmu?
23 Bayin Allah masu aminci ba sa ganin wuyan bin umurnin da aka ba mu cewa mu riƙa yin taro. (Ibran. 10:24, 25; 1 Yoh. 5:3) Alal misali, Sarki Dauda ya ji daɗin zuwa haikalin Jehobah don ya yi masa ibada. (Zab. 27:4) Ya so yin hakan musamman ma tare da mutanen da suke ƙaunar Allah. (Zab. 35:18) Ka kuma tuna da misalin da Yesu ya kafa. Tun yana yaro, ya yi sha’awar kasancewa a gidan Ubansa don ya yi ibada.—Luk 2:41-49.
Za mu nuna cewa mun gaskata da Mulkin Allah idan muna halartan taro a kai a kai
24. Mene ne muke samun damar yi sa’ad da muka halarci taro?
24 Idan muka halarci taro, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu ƙarfafa ’yan’uwanmu. Muna kuma nuna cewa muna ɗokin koyon yadda za mu yi rayuwa a matsayin talakawan Mulkin Allah domin a taron ikilisiya da manyan taro ne muke samun irin wannan koyarwar. Ƙari ga haka, taronmu suna horar da mu kuma suna ba mu ƙarfin ci gaba da yin aikin da ya fi muhimmanci, wato yin wa’azi da kuma koyar da mutane don su zama almajiran Sarki Yesu Kristi. (Karanta Matta 28:19, 20.) Babu shakka, za mu nuna cewa mun gaskata da Mulkin Allah idan muna halartan taro a kai a kai. Bari mu ci gaba da ɗaukan taronmu da muhimmanci sosai!