Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 15

Gwagwarmaya don Samun ’Yancin Yin Ibada

Gwagwarmaya don Samun ’Yancin Yin Ibada

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda Kristi ya taimaka wa mabiyansa su yi gwagwarmaya don hukuma ta yi musu rajista kuma su sami ’yancin yin biyayya ga dokokin Allah

1, 2. (a) Mene ne ya tabbatar da cewa kai ɗan Mulkin Allah ne? (b) Me ya sa a wasu lokatai Shaidun Jehobah suke gwagwarmaya don su sami ’yancin yin ibada?

 KAI ɗan Mulkin Allah ne? Hakika, a matsayin Mashaidin Jehobah, kai ɗan Mulkin Allah ne! Mene ne ke tabbatar da hakan? Ba fasfo ba ne ko wasu takardu daga gwamnati. Maimako hakan, tabbacin ya dangana ne ga yadda kake bauta wa Jehobah. Ibada ta gaskiya ta wuce batun imaninka kawai. Ta ƙunshi abin da kake yi, wato biyayyar da kake yi wa dokokin Mulkin Allah. Ga dukanmu, ibadarmu ta shafi dukan fasalolin rayuwarmu, har da yadda muke tarbiyyar da iyalanmu da kuma matakan da muke ɗauka game da lafiyar jikinmu.

2 Amma, duniyar da muke ciki takan tauye mana ’yancinmu na kasancewa ’yan Mulkin Allah ko kuma ta hana mu bin ƙa’idodin Mulkin. Wasu gwamnatoci sun yi yunƙurin rage mana ’yancin gudanar da ibada ko kuma hana mu yin ibada gaba ɗaya. A wasu lokatai, mabiyan Yesu sun yi gwagwarmaya don su sami ’yancin bin dokokin Sarki Almasihu. Hakan abin mamaki ne? A’a, domin mutanen Jehobah a zamanin dā ma sun yi gwagwarmaya don su sami ’yancin bauta wa Jehobah.

3. Wane yaƙi ne mutanen Allah suka yi a zamanin Sarauniya Esther?

3 Alal misali, a zamanin Sarauniya Esther, bayin Allah sun yi yaƙi don su ceci kansu. Me ya sa? Mugun Firayim Minista Haman ya shawarci Sarkin Farisa, Ahasuerus, ya sa a kashe dukan Yahudawan da ke ƙasar sarkin domin “shari’arsu kuwa dabam ce da ta dukan mutane.” (Esther 3:8, 9, 13) Jehobah ya bar hakan ya faru da bayinsa ne? A’a, ya albarkaci ƙoƙarin da Esther da Mordekai suka yi sa’ad da suka roƙi sarkin Farisa ya kāre bayin Allah.—Esther 9:20-22.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan babin?

4 A zamaninmu kuma fa? Kamar yadda muka gani a Babi na 14, a wasu lokatai, hukumomi sun yi hamayya da Shaidun Jehobah. A wannan babin, za mu tattauna wasu hanyoyin da irin waɗannan gwamnatocin suka yi ƙoƙarin hana mu yin ibada. Za mu tattauna muhimman fannoni uku: (1) ’yancinmu na kasancewa a matsayin ƙungiya da kuma yin ibada yadda muke so, (2) ’yancinmu na zaɓar jinyar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, da kuma (3) ’yancin da iyaye suke da shi su yi renon yaransu bisa ƙa’idodin da Jehobah ya shimfiɗa. A kowane fanni, za mu ga yadda ’yan Mulkin Almasihu masu aminci suka yi gwagwarmaya don su kāre ’yancinsu mai tamani da kuma yadda aka albarkace ƙoƙarinsu.

Gwagwarmayar Samun ’Yanci da Kuma Rajista Daga Hukuma

5. Ta yaya yin rajista da hukuma yake amfanar Kiristoci na gaskiya?

5 Shin sai mun yi rajista ne da gwamnatocin ’yan Adam ko kuma sun amince da aikinmu kafin mu bauta wa Jehobah? A’a, amma yin rajista da hukuma zai taimaka mana mu gudanar da ibadarmu cikin sauƙi. Alal misali, za mu iya yin taro a Majami’un Mulki da Majami’un Taro, za mu iya buga kuma mu shigo da littattafanmu da suka bayyana Littafi Mai Tsarki, kuma za mu iya yin wa’azi ga maƙwabtanmu babu hani. A ƙasashe da yawa, domin Shaidun Jehobah sun yi rajista, suna more ’yancin yin ibada kamar sauran addinan da aka yi wa rajista. Amma mene ne yake faruwa sa’ad da gwamnatoci suka ƙi yi mana rajista ko kuma suka yi ƙoƙarin danne mana ’yancinmu?

6. Wane ƙalubale ne Shaidun Jehobah suka fuskanta a Ostereliya a tsakanin shekara ta 1940 zuwa 1943?

6 Ostareliya. A tsakanin shekara ta 1940 zuwa 1943, gwamna-janar na Ostareliya ya ce imaninmu yana jawo “koma-baya” ga yaƙin da suke yi. Saboda haka, an sa takunkumi a ayyukanmu. Shaidu sun kasa yin taro da kuma wa’azi a fili, an rufe Bethel, kuma an ƙwace Majami’un Mulki. An hana mu ma mallakar littattafanmu da suka bayyana Littafi Mai Tsarki. Bayan sun yi shekaru suna gudanar da ayyukansu a ɓoye, sai Allah ya kawo ƙarshen matsalar da Shaidu a Ostareliya suke fuskanta. A ranar 14 ga Yuni, 1943, Babban Kotun Ostareliya ya cire takunkumin da aka sa wa Shaidun Jehobah.

7, 8. Ka ambata gwagwarmayar neman ’yancin ibada da ’yan’uwanmu a Rasha suka yi shekaru suna yi.

7 Rasha. A ƙarƙashin gwamnatin Kwaminisanci, an hana Shaidun Jehobah gudanar da ayyukansu na ibada har tsawon shekaru da yawa, amma a ƙarshe an yi musu rajista a shekara ta 1991. Bayan faɗuwar Soviet Union ta dā, Gwamnatin Tarayya ta Rasha ta amince da aikinmu a ƙarƙashin doka a shekara ta 1992. Amma ba da daɗewa ba, sai wasu ’yan hamayya, musamman waɗanda suke Cocin Orthodox ta Rasha suka fara jin tsoro saboda ƙaruwar da muke samu. ’Yan hamayyar sun shigar da ƙararraki guda biyar a kotu tsakanin shekara ta 1995 da 1998, suna tuhumar Shaidun Jehobah da laifi. A kowane zaman da suka yi a kotu, alƙalin bai sami Shaidun da laifi ba. Amma ’yan hamayyar ba su karaya ba, sai suka sake shigar da ƙara a shekara ta 1998. Da farko Shaidun sun yi nasara, amma ’yan hamayyar sun ƙi amincewa da hukuncin sai suka ɗaukaka ƙara, kuma sun ka da Shaidun Jehobah a hukuncin da aka yanke a watan Mayu ta 2001. An sake zaman shari’ar a watan Oktoba ta shekarar 2001, kuma a 2004, an yanke hukuncin ƙwace rajistar da aka yi wa Shaidun Jehobah a Moscow da kuma saka musu takunkumi.

Titos Manoussakis (Ka duba sakin layi na 9)

8 Hakan ya sa aka soma tsananta wa Shaidun Jehobah sosai. (Karanta 2 Timotawus 3:12.) An kai musu farmaki kuma sun fuskanci tsanantawa. An ƙwace littattafansu na addini, kuma an hana su yin haya ko gina gidajen yin ibada. Ka yi tunanin yadda ’yan’uwanmu maza da mata suka ji a lokacin da suke fuskantar waɗannan matsalolin! Shaidun sun kai ƙara Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam (European Court of Human Right) a shekara ta 2001 kuma sun aika ƙarin bayanai zuwa Kotun a 2004. Kotun ya yanke hukunci a shekara ta 2010. Kotun ya ce Rasha ta hana ayyukan Shaidun ne domin ba ta son addininsu kuma ya ce babu dalilin da zai sa ya amince da hukuncin waɗannan kotunan Rasha, tun da babu shaidar da ta nuna cewa Shaidun Jehobah sun aikata wani laifi. Kotun ya daɗa cewa an saka wannan takunkumi a kan ayyukan Shaidun Jehobah ne kawai don a cire musu kāriyar da suke da ita a ƙarƙashin doka. Hukuncin Kotun ya nuna cewa Shaidun suna da ’yancin gudanar da addininsu. Ko da yake hukumomi dabam-dabam a Rasha sun ƙi bin hukuncin Kotun Turai, bayin Allah a wannan ƙasar sun sami ƙarin ƙarfin gwiwa daga waɗannan nasarorin.

9-11. Ta yaya mutanen Jehobah suka yi gwagwarmayar neman ’yancin yin ibada a Girka, kuma mene ne sakamako?

9 Girka. A shekara ta 1983, Titos Manoussakis ya kama hayar ɗaki a birnin Heraklion, Crete, don wani ƙaramin rukunin Shaidun Jehobah su riƙa haɗuwa suna yin ibadarsu a ciki. (Ibran. 10:24, 25) Ba da daɗewa ba, wani limamin cocin Orthodox ya shigar da ƙara wajen ’yan sanda saboda ɗakin da ’yan’uwan suke amfani da shi don ibada. Me ya sa? Domin kawai imanin Shaidun ya bambanta da na Cocin Orthodox! Sai lauyan gwamnati ya shigar da ƙarar a gaban kotu kuma aka fara tuhumar Titos Manoussakis da kuma wasu Shaidun Jehobah guda uku. An ci su tara kuma aka yanke musu hukuncin wata biyu a kurkuku. A matsayin ’yan Mulkin Allah masu aminci, Shaidun sun ɗauki hukuncin da kotun ya yanke a matsayin ƙeta ’yancin da suke da shi na yin ibada, sai suka ɗaukaka ƙara zuwa kotunan ƙasar kuma a ƙarshe suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam.

10 A ƙarshe, wannan Kotun ya yanke hukuncin da ya jijjiga maƙiyan ibada ta gaskiya. Kotun ya ce: “Shaidun Jehobah ‘sanannen addini’ ne a ƙarƙashin dokar Girka” kuma hukuncin da kotunan Girka suka yanke ya “ƙeta ’yancin addinin waɗanda suka shigar da ƙarar.” Kotun Turai ya ce gwamnatin Girka “ba ta da izinin bincika imanin mutum ko kuma yadda mutumin yake gudanar da ibadarsa.” Kotun Turai ya yi watsi da hukunce-hukuncen da aka yanke wa Shaidun, kuma hakan ya sa Shaidun suka sake samun ’yancinsu na yin ibada!

11 Wannan nasarar ta kawo ƙarshen matsalar nan a Girka kuwa? Abin taƙaici shi ne, a’a. Bayan wannan nasarar, an yi shekaru 12 ana tabka irin wannan shari’ar a garin Kassandreia, a ƙasar Girka kafin kotu ya warware matsalar a shekara ta 2012. Wani limamin cocin Orthodox ne ya shigar da ƙarar. Majalisar Ƙasa, wato, The Council of State, wanda shi ne kotu mafi girma a Girka ne ya yanke hukuncin kuma bayin Allah ne suka yi nasara. Hukuncin ya yi nuni ga tsarin mulkin Girka wanda ya amince da ’yancin addini kuma kotun ya yi watsi da tuhumar da ake yi wa Shaidun Jehobah cewa addininsu ba sananne ba ne. Kotun ya ce: “Imanin ‘Shaidun Jehobah’ ba ɓoyayye ba ne, saboda haka, su ’yan sanannen addini ne.” Waɗanda suke ƙaramar ikilisiyar da ke birnin Kassandreia sun yi murna sosai domin yanzu suna iya yin ibada a Majami’ar Mulkinsu.

12, 13. Ta yaya ’yan hamayya a ƙasar Faransa suka yi ƙoƙarin kafa dokoki don su yi ‘hukunci na zalunci,’ kuma mene ne sakamakon hakan?

12 Faransa. Wasu da ke hamayya da bayin Allah sun yi ƙoƙarin kafa dokoki don su yi ‘hukunci na zalunci.’ (Karanta Ishaya 10:1.) Alal misali, a shekara ta 1995, hukumomin karɓan haraji a Faransa sun soma binciken sha’anin kuɗin Association Les Témoins de Jéhovah (ATJ), wato ɗaya daga cikin sunayen da Shaidun Jehobah suka yi rajista da shi a Faransa. Ministan kasafin kuɗi ya bayyana ainihin maƙasudinsu na yin wannan binciken, ya ce: “Binciken zai iya sa kotu ya ƙwace dukiyoyinsu ko kuma a tuhume su da laifi . . . , kuma hakan zai iya rikitar da ayyukan ƙungiyar ko ya tilasta mata ta daina gudanar da ayyukanta a ƙasarmu.” Ko da yake binciken kuɗin da aka yi ya nuna cewa kome yana tafiya sumul, hukumomin harajin sun ɗora wa ATJ haraji mai yawan gaske. Idan hukumar ta yi nasara, wannan dabarar za ta sa ’yan’uwanmu su rufe ofishin reshen da ke ƙasar kuma su sayar da gine-ginen don su biya harajin nan mai yawan gaske. Hakan ya girgiza ’yan’uwanmu sosai, amma ba su karaya ba. Shaidun sun ƙi amincewa da wannan hukuncin domin rashin adalci ne aka yi musu, sai suka ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam a 2005.

13 Kotun ya yanke hukunci a ranar 30 ga Yuni, 2011. Kotun ya ce idan babu wani abin da ya saɓa wa doka, ya kamata ’yancin addini ya hana gwamnati bincika cancantar imanin addini ko kuma yadda masu bin addinin suke gudanar da ibadarsu. Kotun ya daɗa da cewa: “Harajin . . . zai hana ƙungiyar samun kuɗin gudanar da ayyukanta, bayan haka, zai iya hana mabiyan addinin gudanar da ibadarsu bisa ga ’yancin da suke da shi.” Kotun ya yanke hukunci kuma Shaidun Jehoba ne suka yi nasara! Mutanen Jehobah sun yi farin ciki sa’ad da gwamnatin Faransa ta mai da harajin da ta karɓa daga ATJ har da ruwa a kai. Kamar yadda Kotun ya umurta, gwamnatin ta mai da musu ginin ofishin reshen da ta ƙwace.

Kana iya yin addu’a a kullum a madadin ’yan’uwanka masu bi, waɗanda suke shan wahala a yanzu saboda rashin adalcin da ake yi musu a kotu

14. Ta yaya za ka iya taimakawa a gwagwarmayar samun ’yancin yin ibada?

14 Kamar Esther da Mordekai a zamanin dā, mutanen Jehobah a yau suna gwagwarmaya don su sami ’yancin bauta wa Jehobah a hanyar da yake so. (Esther 4:13-16) Za ka iya taimakawa kuwa? Ƙwarai! Kana iya yin addu’a a kullum a madadin ’yan’uwanka masu bi, waɗanda suke shan wahala a yanzu saboda rashin adalcin da ake yi musu a kotu. Irin waɗannan addu’o’in za su iya ƙarfafa ’yan’uwanmu da suke shan wahala da kuma tsanantawa. (Karanta Yaƙub 5:16.) Jehobah yana jin addu’o’in nan kuwa? Nasarorin da muke samu a kotu sun nuna cewa yana ji!—Ibran. 13:18, 19.

’Yancin Zaɓan Jinyar da Ta Jitu da Imaninmu

15. Waɗanne abubuwa ne bayin Allah suke la’akari da shi game da yin amfani da jini?

15 Kamar yadda muka gani a Babi na 11, Littafi Mai Tsarki ya gaya wa ’yan Mulkin Allah su guji yin amfani da jini, abin da ya zama gama-gari a yau. (Far. 9:5, 6; Lev. 17:11; karanta Ayyukan Manzanni 15:28, 29.) Ko da yake ba ma karɓan ƙarin jini, muna son jinya mafi kyau wa mu da ƙaunatattunmu idan jinyar ba za ta saɓa wa dokokin Allah ba. Kotunan ƙoli na ƙasashe da yawa sun yarda cewa mutane suna da ’yancin zaɓa ko su ƙi jinya saboda lamirinsu da kuma imaninsu. Amma, a wasu ƙasashen, bayin Allah sun fuskanci matsaloli da yawa saboda wannan batun. Ga wasu misalai.

16, 17. Wace irin jinya ce aka yi wa wata ’yar’uwa a Japan da ya jijjiga ta sosai, kuma ta yaya Jehobah ya amsa addu’o’inta?

16 Japan. Misae Takeda, wata matar aure ce ’yar shekara 63 a Japan, kuma tana bukatar tiyata. A matsayinta na ’yar Mulkin Allah, ta bayyana wa likitanta dalla-dalla cewa ba ta son ƙarin jini. Duk da haka, bayan watanni, ta yi mamakin jin cewa an yi mata ƙarin jini a lokacin da ake yi mata tiyata. Domin cuci da kuma ruɗi da aka yi mata, ’yar’uwa Takeda ta kai ƙarar likitocin da kuma asibitin kotu a watan Yuni ta 1993. Wannan ’yar’uwar mai ladabi kuma mai magana a hankali tana da bangaskiya mai ƙarfi. Ta gaya wa kotun da ke cike da mutane abin da ya faru babu jin tsoro, kuma ta kasance a tsaye a wurin da ake saka shaidu a kotu fiye da awa ɗaya duk da rashin lafiyarta. Zuwanta kotu na ƙarshe shi ne wata ɗaya kafin mutuwarta. Gaba gaɗinta da bangaskiyarta sun burge mu, ko ba haka ba? ’Yar’uwa Takeda ta ce ta roƙi Jehobah a kullum ya albarkaci gwagwarmayar da take yi. Ta kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ji addu’o’inta. Hakan ya faru kuwa?

17 Shekaru uku bayan mutuwar ’Yar’uwa Takeda, Kotun Ƙoli na ƙasar Japan ya yanke hukunci kuma ta yi nasara, Kotun ya ce laifi ne a yi mata ƙarin jinin da ta ce ba ta so. Wannan hukuncin da aka yanke a ranar 29 ga Fabrairu, 2000, ya nuna cewa, idan ya zo ga “’yancin zaɓi” a irin wannan batu, “dole ne a daraja ’yancin da mutum yake da shi na yin zaɓi.” Saboda gwagwarmayar da ’Yar’uwa Takeda ta yi don samun ’yancinta na zaɓan jinyar da ta jitu da lamirinta da Littafi Mai Tsarki ya horar, a yau Shaidu a Japan suna iya yin jinya ba tare da jin tsoron za a tilasta musu su karɓi ƙarin jini ba.

Pablo Albarracini (Ka duba sakin layi na 18 to 20)

18-20. (a) Ta yaya kotun ɗaukaka ƙara a Ajantina ya amince da ’yancin ƙin karɓan ƙarin jini ta wajen amfani da takardar izinin jinya? (b) A batun ƙarin jini, ta yaya za mu nuna cewa mun ba da kanmu ga sarautar Kristi?

18 Ajantina. Ta yaya ’yan Mulkin za su iya kasancewa a shirye don irin jinyar da za a iya yi musu sa’ad da suke a sume? Muna iya kasancewa tare da takardarmu da ke bisa doka don ta yi magana a madadinmu kamar yadda Pablo Albarracini ya yi. A watan Mayu ta 2012, ɓarayi sun je fashi kuma ruwan harsashin da suka yi ya same Pablo. An kwantar da shi a asibiti a sume kuma hakan ya hana shi bayyana matsayinsa game da ƙarin jini. Amma, yana tare da katin da ke ɗauke da cikakken umurni game da irin jinyar da yake so, kuma shi da kansa ne ya saka hannu a takardar shekaru huɗu kafin wannan aukuwar. Ko da yake yanayinsa ya yi tsanani sosai kuma wasu likitoci suna ganin yana bukatar ƙarin jini don a ceci ransa, likitocin da ke jinyarsa sun yarda su yi abin da yake so. Amma, mahaifin Pablo, wanda ba Mashaidin Jehobah ba ne, ya je kotu ya karɓi izinin soke abin da ɗansa ya ce yake so.

19 Nan da nan sai lauyan da ke wakiltar matar Pablo ya ɗaukaka ƙara. Sa’o’i da yin hakan, sai kotun ɗaukaka ƙara ya yi watsi da umurnin da wancan kotun ya bayar kuma kotun ɗaukaka ƙarar ya ce dole ne a daraja abin da mai rashin lafiyar ya ce a cikin takardar da ke ɗauke da irin jinyar da yake so. Mahaifin Pablo ya ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Ajantina. Amma, Kotun Ƙolin ya ce bai ga “wani dalilin da zai sa ya yi shakkar cewa [Pablo ya cika takardar jinyar da ta nuna cewa ba ya son ƙarin jini] ne sa’ad da yake cikin hankalinsa, kuma ya yi hakan da manufa da kuma ’yanci.” Kotun ya ce: “Duk wani mutumin da ya balaga yana da ikon rubuta irin jinyar da yake so, kuma zai iya amincewa ko ya ƙi wata irin jinya. . . . Dole ne likita ya bi wannan umurnin.”

Ka cika takardar izinin kula da jinya?

20 Ɗan’uwa Albarracini ya daɗe da warkewa. Shi da matarsa suna godiya domin ya cika wannan umurni game da jinya tun kafin lokacin jinyar. Ta wajen ɗaukan wannan ƙaramin mataki mai muhimmanci, ɗan’uwa Albarracini ya nuna cewa ya miƙa wuya ga sarautar Kristi a ƙarƙashin Mulkin Allah. Kai da iyalinka kun ɗauki matakin nan kuwa?

April Cadoreth (Ka duba sakin layi na 21 to 24)

21-24. (a) Ta yaya ne Kotun Ƙoli na ƙasar Kanada ya yanke wani gagarumin hukunci game da ƙananan yara da kuma ƙarin jini? (b) Ta yaya ne wannan hukuncin zai iya ƙarfafa bayin Jehobah matasa?

21 Kanada. A wannan ƙasar, kotuna suna amince da ’yancin da iyaye suke da shi na zaɓa wa ’ya’yansu jinya mafi kyau. Akwai lokatan da ma kotunan suka yanke hukunci cewa ya kamata a daraja abin da matasan da ba su kai shekara 16 ba suka ce game da irin jinyar da suke so. Abin da ya faru da ’Yar’uwa April Cadoreth ke nan. Sa’ad da take ’yar shekara 14, an kwantar da April a asibiti saboda yoyon jini a cikin cikinta. ’Yan watanni kafin wannan aukuwar, ta cika takardar Izinin Kula da Jinya, wato DPA, da ya ƙunshi umurni cewa kada a yi mata ƙarin jini ko a lokacin gaggawa ma. Likitan da ke kula da ita ya yi watsi da umurnin da April ta bayar kuma ya nemi kotu ya ba shi izinin yi mata ƙarin jini. Sun yi mata ƙarin jini leda uku ƙarfi-da-yaji. Bayan haka, April ta ce tana ji kamar fyaɗe aka yi mata.

22 April da iyayenta sun shigar da ƙara kotu don a bi musu hakkinsu. Bayan shekaru biyu, an shigar da ƙarar a Kotun Ƙoli na ƙasar Kanada. Ko da yake Kotun bai canja dokar da April ta ƙalubalanta ba, amma ya ba ita da sauran matasan da ba su kai shekara 16 ba ’yancin tsai da shawara game da irin jinyar da suke so. Kotun ya ce: “A batun jinya, ya kamata a ƙyale matasan da ba su kai shekara 16 ba su nuna cewa sun isa tsai da shawara game da irin jinyar da suke so.”

23 Wannan muhimmiyar shari’a ce, domin Kotun Ƙoli ya nuna ’yancin da matasan da ba su kai shekara 16 ba suke da shi a ƙarƙashin doka. Kafin wannan hukuncin, kotu a Kanada suna iya ba da umurnin a yi wa matashin da bai kai shekara 16 ba duk wata irin jinyar da kotun yake ganin zai dace da matashin. Amma bayan wannan hukuncin, kotu ba zai iya tilasta a yi wa matashin da bai kai shekara 16 jinyar da ba ya so ba, ba tare da an ba shi damar tabbatar da cewa ya isa tsai da shawara da kansa ba.

“Sanin cewa na ɗan taimaka wajen ɗaukaka sunan Allah da kuma ƙaryata Shaiɗan ya faranta mini rai sosai”

24 Kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa a wannan gwagwarmayar da aka shafe shekaru uku ana yi? April ta ce, “E!” Yanzu ita majagaba ce mai ƙoshin lafiya kuma ta ce: “Sanin cewa na ɗan taimaka wajen ɗaukaka sunan Allah da kuma ƙaryata Shaiɗan ya faranta mini rai sosai.” Labarin April ya nuna cewa matasanmu za su iya tashi tsaye kuma su nuna cewa su ’yan Mulkin Allah ne da gaske.—Mat. 21:16.

’Yancin Yi wa Yara Tarbiyya Bisa Mizanan Jehobah

25, 26. Wane yanayi ne yakan taso wani lokaci sa’ad da aka kashe aure?

25 Jehobah ya danƙa wa iyaye hakkin yi wa ’ya’yansu tarbiyya bisa mizanansa. (K. Sha 6:6-8; Afis. 6:4) Hakan yana iya zama jan aiki musamman bayan iyaye sun kashe aurensu. Ra’ayin iyaye yana iya bambanta game da yadda za su yi wa ’ya’yansu tarbiyya. Alal misali, iyayen da Mashaidi ne yana iya nacewa a yi wa yaro tarbiyya bisa mizanan Kirista, yayin da wanda ba Mashaidi ba zai iya ƙin amincewa da hakan. Hakika, ya kamata iyayen da Mashaidi ne ya fahimci cewa mutuwar aure za ta iya raba mata da miji, amma ba za ta iya raba dangantakar da ke tsakanin iyaye da yaransu ba.

26 Iyayen da ba Mashaidi ba ne zai iya shigar da ƙara kotu don a ba shi riƙon ɗansu ko kuma ’ya’yansu domin ita ko shi ya yi musu tarbiyya bisa tafarkin addininsa. Wasu sun yi da’awa cewa yi wa yaro tarbiyya a matsayin Mashaidin Jehobah yana da haɗari. Suna iya cewa za a hana yaran yin bikin tuna ranar haihuwarsu da sauran bukukuwa, har da ƙin “ceto ran” yaran da ƙarin jini idan suna bukatar jinya da gaggawa. Abin farin ciki shi ne, yawancin kotuna suna duba abin da ya fi wa yaron alheri ne, maimakon su yanke hukunci a kan ko addinin ɗaya daga cikin iyayen yana da haɗari. Bari mu duba wasu misalai.

27, 28. Wane hukunci ne Kotun Ƙoli na jihar Ohio ya yanke a batun da aka shigar a gabanta cewa yi wa yaro tarbiyyar Shaidun Jehobah yana da haɗari?

27 Amirka. A shekara ta 1992, Kotun Ƙolin Ohio, ya saurari wata ƙarar da aka ɗaukaka zuwa gabanta inda wani mahaifin da ba Mashaidi ba ne yake da’awar cewa za a jefa ɗansa matashi cikin haɗari idan aka yi masa tarbiyya a matsayin Mashaidin Jehobah. Kotun da aka fara shigar da ƙarar ya amince da abin da mahaifin ya ce kuma ya ba shi riƙon ɗan. An ba mahaifiyar yaron, Jennifer Pater, damar ziyartar sa, amma an umurce ta kada ta “koya wa yaron imanin Shaidun Jehobah ta kowace hanya.” Wannan umurnin da ƙaramin kotun ya bayar yana nufin cewa ’Yar’uwa Pater ba za ta iya tattauna Littafi Mai Tsarki ko mizanansa na ɗabi’a da ɗanta, Bobby ba! Ka yi tunanin yadda ta ji game da hakan. Abin ya baƙanta ran Jennifer sosai, amma ta ce ta yi haƙuri kuma ta miƙa al’amarin ga Jehobah. Ta tuna abin da ya faru kuma ta ce: “Jehobah ya kasance tare da ni kullum.” Tare da taimakon ƙungiyar Jehobah, lauyanta ya ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ƙolin Ohio.

28 Kotun Ƙolin ya yi watsi da hukuncin wancan kotun, kuma ya ce “iyaye suna da cikakken ’yancin yi wa ’ya’yansu tarbiyya bisa ƙa’idodin addininsu.” Kotun ya ce ba shi da izinin hana iyaye riƙon ’ya’yansu saboda addininsu, sai dai idan akwai ƙwaƙƙwarar shaidar da ta nuna cewa imanin Shaidun Jehobah zai jefa yaron cikin haɗari. Kotun Ƙolin bai ga shaidar da ta nuna cewa imanin Shaidun zai jefa lafiyar yaron cikin haɗari ba.

Kotuna da yawa sun yanke hukuncin da ya ba iyaye Kiristoci ikon rainon ’ya’yansu

29-31. Me ya sa aka hana wata ’yar’uwa a ƙasar Denmark rainon ’yarta, kuma wane hukunci ne Kotun Ƙoli na ƙasar Denmark ya yanke a wannan batun?

29 Denmark. Anita Hansen ta fuskanci irin wannan matsalar sa’ad da tsohon mijinta ya kai ƙara kotu don a ba shi ’yancin rainon ’yarsu ’yar shekara bakwai mai suna Amanda. Ko da yake a shekara ta 2000 kotun gunduma (district court) ya ba ’Yar’uwa Hansen rainon ’yarsu, amma mijinta, wato mahaifin Amanda ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli na tarayya (high court), kotun ya yi watsi da hukuncin kotun gunduma kuma ya ba mahaifin ’yancin rainon ’yarsa. Kotun ƙolin ya ce tun da addinan iyayen ba ɗaya ba kuma hakan ya haifar da bambancin ra’ayi tsakaninsu, mahaifin ne kaɗai zai iya tsai da shawara a kan addinin da yarinyar za ta bi. Saboda haka, kotun ya ƙwace Amanda daga hannun ’yar’uwa Hansen domin ita Mashaidiyar Jehobah ce!

30 A lokacin da take cikin wannan matsalar, ’yar’uwa Hansen takan rasa abin da za ta ce a addu’a. Amma ta ce: “Abin da ke Romawa 8:26 da 27 sun ƙarfafa ni sosai. Na san cewa Jehobah ya fahimci nufina. Idanunsa suna kaina kuma yana tare da ni a kullum.”—Karanta Zabura 32:8; Ishaya 41:10.

31 ’Yar’uwa Hansen ta ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Ƙoli na ƙasar Denmark. A hukuncinsa, Kotun ya ce: “Ana yanke hukuncin wanda zai riƙe ’ya ne bayan an duba abin da zai fi wa ’yar alheri.” Kotun ya kuma ce ana yanke hukunci ne na wanda zai riƙe ’ya bisa ga yadda kowane iyaye yake warware matsaloli, ba bisa “imani da kuma matsayin” Shaidun Jehobah ba. ’Yar’uwa Hansen ta yi murna sosai sa’ad da Kotun ya ba ta ’yancin rainon ’yarta Amanda.

32. Ta yaya ne Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam ya kāre iyaye Shaidun Jehobah daga bambancin da ake nuna musu?

32 Ƙasashe dabam-dabam a Turai. A wasu yanayin, jayayyar da ake samu game da hukuncin da aka yanke na wanda zai riƙe yara tana kai wa har Kotun Turai na Kāre ’Yancin ’Yan Adam. Sau biyu, Kotun Turai ya ce yadda kotunan ƙasashe suke bi da iyayen da Shaidu ne ya bambanta da waɗanda ba Shaidu ba saboda addininsu. Kotun Turai ya kira hakan nuna bambanci, kuma a hukuncin da ya yanke, ya ce “bai amince da nuna fifiko saboda bambancin addini ba.” Wata mahaifiya Mashaidiya da ta amfana daga wannan hukunci na Kotun Turai ta yi murna sosai kuma ta ce, “Na yi baƙin ciki sosai saboda zargi na da aka yi cewa zan cutar da ’ya’yana, domin ina ƙoƙarin yi musu tarbiyyar Kirista wadda na san za ta amfane su.”

33. Ta yaya ne iyaye Shaidu za su iya yin amfani da ƙa’idodin da ke Filibiyawa 4:5?

33 Hakika, ya kamata iyaye Shaidu da ake shari’a da su a kotu saboda ’yancin da suke da shi na koya wa yaransu mizanan Littafi Mai Tsarki su ƙoƙarta wajen nuna sanin yakamata. (Karanta Filibiyawa 4:5.) Kamar yadda suka fahimci cewa suna da ’yancin yi wa ’ya’yansu tarbiyya yadda Allah yake so, hakazalika sun yarda cewa, iyayen da ba Mashaidi ko Mashaidiya ba tana iya ba da nata gudummawar wajen kula da yaran idan tana so. Yaya iyaye Shaidu suke ɗaukan hakkin yi wa yara tarbiyya?

34. Ta yaya ne iyaye Kiristoci a yau za su iya amfana daga misalin Yahudawan zamanin Nehemiya?

34 Wani misali a zamanin Nehemiya ya bayyana hakan. Yahudawa sun yi aiki tuƙuru don su gyara kuma su sake gina bangon Urushalima. Sun san cewa yin hakan zai kāre su da iyalansu daga ƙasashe maƙiya da ke kewaye da su. Saboda wannan dalilin, Nehemiya ya umurce su: “Ku yi yaƙi domin ’yan’uwanku, da ’ya’yanku, maza da mata, da matayenku, da gidajenku.” (Neh. 4:14) Wannan yaƙin yana da muhimmanci sosai ga waɗannan Yahudawan. A yau ma, iyayen da Shaidun Jehobah ne suna aiki tuƙuru don su yi wa ’ya’yansu tarbiyya cikin gaskiya. Sun san cewa ’ya’yansu suna fuskantar tasiri marar kyau a makaranta da kuma a yankin da suke da zama. Irin waɗannan tasirin suna iya shiga gida ta kafofin yaɗa labarai. Iyaye, kada ku manta cewa kwalliya za ta biya kuɗin sabulu a duk wani yaƙin da kuke yi saboda ’ya’yanku maza da mata su girma a hanyar da za su ci gaba da inganta dangantakarsu da Jehobah.

Ku Sani Cewa Jehobah Zai Tallafa wa Ibada ta Gaskiya

35, 36. Ta yaya Shaidun Jehobah suka amfana daga gwagwarmayar da aka yi don samun ’yanci, kuma mene ne ƙudurinka?

35 Babu shakka, Jehobah ya albarkaci ƙungiyarsa ta zamaninmu a gwagwarmayar da take yi na samun ’yancin yin ibada. A gwagwarmayar da suke yi na samun ’yancinsu bisa doka, bayin Allah sun ba da shaida mai kyau a kotu da kuma a gaban mutane. (Rom. 1:8) Wani sakamako mai kyau na nasarorin da suka samu a kotu shi ne sun sake ƙarfafa ’yancin mutane da yawa da ba Shaidu ba. Amma, a matsayin bayin Allah, mu ba ’yan neman canji ba ne kuma ba ma ɗaukaka kanmu. Abu mafi muhimmanci shi ne, Shaidun Jehobah sun nemi ’yancinsu ne bisa doka a kotuna don su kafa kuma su yaɗa ibada ta gaskiya.—Karanta Filibiyawa 1:7.

36 Kada mu yi sakaci da darussa na bangaskiya da muka koya daga waɗanda suka yi gwagwarmayar neman ’yancin bauta wa Jehobah! Bari mu ci gaba da kasancewa da aminci, kuma mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana goyon bayan aikinmu kuma zai ci gaba da ba mu ƙarfin yin nufinsa.—Isha. 54:17.