SASHE NA 6
Tallafa wa Mulki—Yin Gini Domin Ibada da Kuma Ba da Agaji
A CE ka shiga Majami’ar Mulkin da kuke yin taro a cikin kuma ka ga kamar ba ita ba ce. Ka daɗe kana alfahari da ginin. Wataƙila ka tuna yadda ka taimaka sa’ad da ake ginin shekarun da suka wuce. Amma yanzu kana murna sosai domin an mai da Majami’ar Mulkin wajen ba da agaji na ɗan lokaci. Bayan wani ambaliyar da ta yi ɓarna a yankinku, sai Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Reshe ya yi shiri nan da nan don a kai abinci, sutura, ruwan sha, da sauran taimako ga waɗanda bala’in ya shafa. An tsara kayan agajin sosai. ’Yan’uwa maza da mata suna shiga suna samun abin da suke so, kuma a yawancin lokatai, suna hawaye don murna.
Yesu ya ce babban abin da za a san mutanensa da shi shi ne ƙaunar da suke yi wa juna. (Yoh. 13:34, 35) A wannan sashen, za mu ga yadda Shaidun Jehobah suka nuna ƙauna ta Kirista ta wajen aikin gine-gine da kuma aikin agaji. Irin wannan ƙaunar tabbaci ne mai girma da ya nuna cewa muna ƙarƙashin sarautar Mulkin Yesu.
A WANNAN SASHEN
BABI NA 19
Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah
Wuraren ibada suna ɗaukaka Allah, amma akwai abin da ya fi ɗaukawa da tamani sosai.