BABI NA 18
Yadda Ake Tallafa wa Ayyukan Mulkin
1, 2. (a) Wace amsa ce Ɗan’uwa Russell ya ba wani fasto da yake so ya san yadda Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke samun kuɗin gudanar da ayyukansu? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan babin?
AKWAI lokacin da wani faston Reformed Church (Cocin Mujaddadi) ya je wurin Ɗan’uwa Charles T. Russell don ya san yadda Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke samun kuɗin gudanar da ayyukansu.
Ɗan’uwa Russell ya ce: “Ba ma yawo da tire don karɓan kuɗi.”
Faston ya tambaye shi: “To, yaya kuke samun kuɗi?”
Russell ya ba da amsa cewa: “Idan na gaya maka gaskiya ba za ka yarda ba.” Ya daɗa da cewa: “Sa’ad da mutane suka halarci taronmu, ba ma miƙa musu kwando don su saka kuɗi. Sun san cewa muna kashe kuɗi. Suna gaya wa kansu, ‘An kashe kuɗi a majami’ar nan . . . Ta yaya ni ma zan iya ba da gudummawar kuɗi?’”
Faston ya kalli Ɗan’uwa Russell cike da mamaki.
Russell ya ci gaba da cewa, “Gaskiya tsantsa nake gaya maka. Sukan tambaye ni, ‘Ta yaya zan tallafa wa aikin nan da gudummawar kuɗi?’ Sa’ad da mutum ya sami albarka kuma yana da kuɗi, zai so ya ba Ubangiji kuɗin. Idan kuma ba shi da kuɗi fa, me ya sa za mu tilasta masa ya yi hakan?” a
2 “Gaskiya tsantsa” ce Ɗan’uwa Russell ya faɗa. Mutanen Allah sun daɗe suna ba da gudummawa da son rai don tallafa wa ibada ta gaskiya. A wannan babin, za mu duba wasu misalai da ke cikin Nassi da kuma na zamani game da ba da gudummawa. Yayin da muke duba yadda ake samun kuɗin tallafa wa ayyukan Mulki a yau, zai dace kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Ta yaya zan iya tallafa wa Mulkin?’
Duk Wanda Ya Yi Niyya Ya Kawo Gudummawa
3, 4. (a) Mene ne Jehobah ya sani game da bayinsa? (b) Ta yaya Isra’ilawa suka tallafa wajen gina mazauni?
3 Jehobah ya amince da bayinsa na gaske. Ya san cewa idan aka ba su dama, za su nuna ibadarsu cike da farin ciki ta wajen ba da gudummawa da son rai. Ka yi la’akari da misalai biyu daga tarihin Isra’ila.
4 Bayan Jehobah ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, ya gaya musu su gina mazauni madaidaici don yin ibada. Yin ginin da kuma kayayyakin da za a saka a ciki zai bukaci abubuwa da dama. Jehobah ya umurci Musa ya ba mutanen dama su tallafa wa aikin ginin, ya ce: “Duk wanda ya yi niyya, bari ya kawo wa Ubangiji sadaka [gudummawa].” (Fit. 35:5, Littafi Mai Tsarki) Yaya mutanen da ba su daɗe da rabuwa da “bauta mai-wuya” ba suka amsa wannan kiran? (Fit. 1:14) Sun tallafa sosai, da son rai, ta wajen ba da zinariya da azurfa da kuma abubuwa masu tamani. Wataƙila sun karɓi yawancin waɗannan abubuwan daga iyayen gidansu na dā, wato Masarawa. (Fit. 12:35, 36) Isra’ilawan sun ba da gudummawa fiye da wadda ake bukata har aka ‘hana su kawowa.’—Fit. 36:4-7.
5. Mene ne Isra’ilawa suka yi sa’ad da Dauda ya ba su damar ba da gudummawa don gina haikali?
5 Wajen shekaru 475 bayan haka, Dauda ya ba da gudummawa daga ‘dukiyarsa’ don a gina haikali, wato tabbatacciyar cibiyar ibada ta gaskiya a duniya. Sai ya ba ’yan’uwansa Isra’ilawa damar ba da gudummawa, yana cewa: “Wanene fa za ya bayas da yardan rai, shi cika hannunsa yau ga Ubangiji?” A sakamakon hakan, mutanen sun ‘bayar da yardan ransu, da sahihiyar zuciya suka yi baiko ga Ubangiji.’ (1 Laba. 29:3-9) Domin ya san ainihin tushen waɗannan gudummawar, Dauda ya yi addu’a ga Jehobah cewa: “Dukan abu daga gareka yake, daga cikin naka kuma muka bayas a gareka.”—1 Laba. 29:14.
6. Me ya sa ake bukatar kuɗi don yin aikin Mulki a yau, kuma waɗanne tambayoyi ne suka taso?
6 Musa da Dauda ba su tilasta wa bayin Allah su ba da gudummawa ba. Maimakon haka, mutanen sun yi hakan ne da zuciya ɗaya. A yau kuma fa? Mun san cewa aikin da Mulkin Allah yake yi yana bukatar kuɗi. Ba ƙaramin kuɗi ake kashewa ba wajen buga da rarraba Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, gina da kuma kula wuraren taro da ofisoshin reshe, da kuma ba da agaji ga ’yan’uwanmu masu bi a lokacin da masifa ta auku. Saboda haka, muhimman tambayoyin da suka taso su ne: Ta yaya ake samun kuɗaɗen nan? Ana bukatar tunzura mabiyan Sarkin don su ba da gudummawa ne?
“Ba Za Ta Taɓa Roƙo ko Ta Nemi Tallafi Daga Mutane Ba”
7, 8. Me ya sa mutanen Jehobah ba sa roƙo ko neman tallafin kuɗi daga mutane?
7 Ɗan’uwa Russell da waɗanda suke aiki tare sun ƙi su yi koyi da hanyoyin neman kuɗi da suka zama gama-gari a cocin Kiristendom. A bayanin da ya yi mai jigon nan “Do You Want ‘Zion Watch Tower’?” (Kana Son ‘Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona’?), a fitowa ta biyu ta Hasumiyar Tsaro, Russell ya ce: “Mun yi imani cewa muna da goyon bayan JEHOBAH wajen wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona, saboda haka, ba za ta taɓa roƙo ko ta nemi tallafi daga mutane ba. Idan [Jehobah] wanda ya ce: ‘Dukan azurfa da zinariya tawa ce,’ ya daina tanadar da kuɗin da muke bukata, za mu san cewa lokaci ya yi na daina wallafa mujallar.” (Hag. 2:7-9) Fiye da shekaru 130 bayan ya yi wannan furucin, Hasumiyar Tsaro da kuma ƙungiyar da ke wallafa ta sai samun ci gaba suke yi!
8 Mutanen Jehobah ba sa roƙon kuɗi. Ba sa yawo da faranti a gaban mutane don su karɓi kuɗi ko kuma su aika wasiƙun neman tallafi. Kuma ba sa bikin gabatar da sababbin littattafai ko su yi baza da makamantansu don su tara kuɗi. Suna bin abin da Hasumiyar Tsaro ta ce tun da daɗewa: “Mun san cewa bai dace mu nemi tallafin kuɗi kamar yadda sauran coci suke yi don gudanar da aikin Ubangiji ba . . . A ra’ayinmu, duk wani kuɗin da aka samu ta hanyoyin roƙo da sunan Ubangijinmu haramun ne a gare shi, kuma ba zai albarkaci waɗanda suka ba da kuɗin ko kuma aikin da aka yi da shi ba.” b
Kowane Mutum Ya Bayar Yadda Ya Yi Niyya a Zuciyarsa
9, 10. Mene ne dalili na farko da ya sa muke ba da gudummawa da son rai?
9 A matsayin talakawan Mulkin a yau, ba sai an tilasta mana mu ba da gudummawa ba. Akasin haka, muna jin daɗin yin amfani da kuɗaɗenmu da wasu dukiyoyinmu don tallafa wa ayyukan Mulki. Me ya sa muke yin hakan da son rai? Bari mu tattauna dalilai uku.
10 Na ɗaya, muna ba da gudummawa da son rai domin muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu yi ‘abubuwan da suke gamshe shi.’ (1 Yoh. 3:22) Hakika, Jehobah yana murna da mai bauta masa da ya ba da gudummawa da zuciya ɗaya. Bari mu duba kalmomin manzo Bulus game da bayarwa ta Kirista. (Karanta 2 Korintiyawa 9:7.) Kirista na gaskiya ba ya sanyin jiki wajen ba da gudummawa ko kuma ya yi hakan don an tilasta masa. Amma, yana bayarwa ne domin ‘ya yi niyya a zuciyarsa’ ya yi hakan. c Wato, yana ba da gudummawar ne bayan ya ga cewa akwai bukata kuma zai iya taimakawa. Jehobah yana ƙaunar irin wannan mutumin, domin “Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” Wata fassarar ta ce: “Allah yana son mutanen da ke son bayarwa.”
11. Mene ne ke motsa mu mu ba Jehobah kyauta mafi tamani?
11 Na biyu, gudummawar da muke yi hanya ce ta miƙa godiya ga Jehobah domin albarka mai yawa da ya yi mana. Ka yi la’akari da wata ƙa’ida mai muhimmanci a Dokar da aka ba da ta hannun Musa. (Karanta Kubawar Shari’a 16:16, 17.) Sa’ad da suke halartar idi guda uku da suke yi kowace shekara, kowane Ba’isra’ile yakan ba da kyauta “gwargwadon albarkar” da Jehobah ya yi masa. Shi ya sa, kafin ya halarci idin, kowane mutumi yana bukatar ya tuna yawan albarka da Allah ya yi masa kuma ya bincika zuciyarsa, kafin ya tsai da shawara game da kyauta mafi kyau da zai kawo. Hakazalika, idan muka duba yadda Jehobah ya albarkace mu a hanyoyi masu yawa, hakan na motsa mu mu ba shi kyauta da ta dace. Kyautar da muka bayar da zuciya ɗaya, wadda ta haɗa da dukiyoyinmu, ta nuna cewa muna godiya domin albarka mai yawa da Jehobah ya yi mana.—2 Kor. 8:12-15.
12, 13. Ta yaya gudummawar da muke bayarwa da son rai take nuna cewa muna ƙaunar Sarki Yesu, kuma nawa ne kowannenmu yake bayarwa?
12 Na uku, muna nuna ƙaunarmu ga Sarki Yesu Kristi ta gudummawar da muke yi. Ta yaya? Ka yi la’akari da abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa a darensa na ƙarshe kafin a kashe shi. (Karanta Yohanna 14:23.) Yesu ya ce: ‘Idan mutum yana ƙaunata, zai kiyaye maganata.’ ‘Maganar’ Yesu ta haɗa da umurninsa na yin bisharar Mulki a faɗin duniya. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Muna kiyaye ‘maganar’ ta wajen yin amfani da lokacinmu, kuzarinmu, da dukiyoyinmu wajen faɗaɗa bisharar Mulki. Ta haka, muna nuna ƙaunarmu ga Sarki Almasihu.
13 Hakika, a matsayin mabiyan Mulki masu aminci, muna so mu nuna goyon bayanmu ga Mulkin da dukan zuciyarmu ta wajen ba da gudummawar kuɗi. Nawa ne kowannenmu yake bayarwa? Wannan shawararmu ce. Kowa zai ba da gudummawa ne gwargwadon ƙarfinsa. Yawancin ’yan’uwanmu masu bi ba masu arziki ba ne. (Mat. 19:23, 24; Yaƙ. 2:5) Amma wani abin da zai iya ƙarfafa irin ’yan’uwan nan shi ne sanin cewa Jehobah da Ɗansa suna ɗaukan gudummawar da suka bayar da zuciya ɗaya da tamani.—Mar. 12:41-44.
Ta Yaya Ake Samun Kuɗi?
14. A shekarun da suka shige, yaya Shaidun Jehobah suke ba da littattafansu?
14 A shekarun da suka shige, Shaidun Jehobah suna ba da littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki kuma su karɓi gudummawa. Ba sa karɓan gudummawa mai yawa don suna so waɗanda ba su da kuɗi sosai ma su iya samun littattafan. Hakika, ko da mutum bai da gudummawar da zai bayar amma yana son littafin, masu shelar Mulki suna marmarin ba shi littafin. Muradinsu shi ne littafin ya shiga hannun mutanen da suke son gaskiya, su karanta shi kuma su amfana.
15, 16. (a) Wane gyara ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yi a hanyar da muke ba da littattafanmu daga 1990? (b) Ta yaya ake ba da gudummawar da son rai? (Ka kuma duba akwatin nan “ Me Ake Yi da Gudummawar da Muke Bayarwa?”)
15 A shekara ta 1990, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yi gyara a yadda muke ba da littattafanmu. Daga wannan shekarar a Amirka, an soma ba wa mutane littattafai ne ba tare da gaya musu kuɗin da za su bayar ba. Wasiƙar da aka rubuta wa dukan ikilisiyoyi a wannan ƙasar ta ce: “Za a ba masu shela da kuma mutanen waje mujallu da littattafai ba tare da an gaya musu yawan gudummawar da za su yi don littafin ko mujallar ba. . . . Duk wanda yake so ya ba da gudummawa don kuɗin da muke kashewa a aikinmu na ilimantarwa zai iya yin hakan, amma za su iya karɓan littattafanmu ko sun ba da gudummawa ko ba su ba da ba.” Wannan shirin ya taimaka wajen bayyana cewa aikinmu na addini ne da ake tallafawa da gudummawa da son rai, kuma ya nuna dalla-dalla cewa “ba ma ɓata [‘tallar,’ NW] maganar Allah.” (2 Kor. 2:17) Daga baya, an soma amfani da wannan shirin na ba da gudummawa da son rai a dukan ofisoshin reshe a faɗin duniya.
16 Ta yaya ake ba da gudummawa da son rai? Akwai akwatunan gudummawa a Majami’un Mulki na Shaidun Jehobah. Mutane suna iya saka gudummawarsu a ciki ko kuma su aika kai tsaye zuwa ofishin reshen Shaidun Jehobah da ke ƙasar. A kowace shekara, akwai talifi a cikin Hasumiyar Tsaro da ke bayyana yadda za a iya ba da gudummawa.
Yaya Ake Amfani da Kuɗin?
17-19. Ka bayyana yadda ake amfani da gudummawar kuɗi a (a) aiki na dukan duniya, (b) gina Majami’ar Mulki a faɗin duniya, da kuma (c) kuɗin da ikilisiya take kashewa.
17 Aiki na dukan duniya. Ana amfani ne da kuɗi don biyan kuɗaɗen da aka kashe wajen yaɗa bishara a faɗin duniya. Kuɗaɗen nan sun haɗa da kuɗin da ake kashewa wajen buga littattafan da ake rarrabawa a faɗin duniya da gina da kuma gyara ofisoshin reshe da gidajen Bethel, da kuma gudanar da makarantu da dama na ƙungiyar Jehobah. Ƙari ga haka, ana amfani da kuɗaɗe wajen kula da masu wa’azi a ƙasashen waje da masu kula masu ziyara da kuma majagaba na musamman. Ana kuma yin amfani da gudummawar da muka bayar wajen ba da agaji na gaggawa ga ’yan’uwanmu masu bi sa’ad da bala’i ya addabe su. d
18 Aikin gina Majami’un Mulki a faɗin duniya. Ana amfani da kuɗaɗe don taimaka wa ikilisiyoyi su gina ko canja fasalin Majami’ar Mulki. Yayin da ake karɓan gudummawa, za a iya ba da ƙarin kuɗi don taimaka wa wasu ikilisiyoyi. e
19 Kuɗin da ikilisiya take kashewa. Ana amfani da kuɗaɗe wajen gudanar da ayyuka da kuma kula da Majami’ar Mulki. Dattawa suna iya cewa a aika wasu kuɗaɗe zuwa ofishin reshe don ci gaban aikin da ake yi a faɗin duniya. A irin wannan yanayin, dattawan za su sanar da ikilisiya game da batun. Idan ikilisiya ta yarda, sai a tura wa ofishin reshe kuɗin. A kowane wata, ɗan’uwan da ke ajiye kuɗin ikilisiya yakan rubuta rahoton kuɗi da za a karanta wa ikilisiya.
20. Ta yaya za ka girmama Jehobah da “wadatarka”?
20 Idan muka yi la’akari da dukan abubuwan da yin bisharar Mulki da kuma almajirantarwa a faɗin duniya ya ƙunsa, hakan yana sa mu ‘girmama Ubangiji da wadatarmu.’ (Mis. 3:9, 10) Wadatarmu ta haɗa da ƙarfinmu, hankalinmu, da kuma abubuwan da muka koya a ibadarmu ga Jehobah. Muna so mu yi amfani da su sosai a aikin Mulki. Amma, mu tuna cewa wadatarmu ta kuma haɗa da dukiyoyinmu. Bari mu ƙuduri niyyar ba da abin da za mu iya bayarwa, a lokacin da za mu iya. Gudummawar da muke bayarwa da son rai tana ɗaukaka Jehobah kuma tana nuna cewa muna goyon bayan Mulkin Almasihu.
a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 1915, shafuffuka na 218-219.
b Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 1899, shafi na 201.
c Wani masani ya ce kalmar Helenanci da aka fassara “yi niyya” “tana nuna abin da mutum ya riga ya yi tunani a kai.” Ya daɗa da cewa: “Ko da yake bayarwa tana sa farin ciki, hakan na bukatar shiri.”—1 Kor. 16:2.
d Ka duba Babi na 20 don ƙarin bayani game da hidimar agaji.
e Ka duba Babi na 19 don ka sami cikakken bayani game da gina Majami’ar Mulki.