Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA SHA BIYAR

Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah

Yadda Ya Dace a Bauta wa Allah

1. Waye ne kaɗai zai iya gaya mana yadda za mu bauta wa Allah?

YAWANCIN addinai suna zato cewa suna koya wa mutane gaskiya game da Allah. Amma hakan ba gaskiya ba ne, domin addinai da yawa suna koyar da ƙarya game da Allah da kuma yadda ya kamata mu bauta masa. Yaya za mu gane hanya mafi kyau na bauta wa Allah? Jehobah ne kaɗai zai iya gaya mana yadda za mu bauta masa.

2. Ta yaya za mu koyi yadda ya kamata mu bauta wa Allah?

2 Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki don mu koyi yadda ya kamata mu bauta masa. Saboda haka, idan ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki, Jehobah zai taimaka maka ka amfana daga koyarwarsa don ya damu da kai sosai.—Ishaya 48:17.

3. Mene ne Allah yake bukata a gare mu?

3 Wasu suna cewa Allah yana amincewa da dukan addinai, amma ba hakan Yesu ya koya mana ba. Ya ce: “Ba dukan mai-ce mani, Ubangiji, Ubangiji, za ya shiga cikin mulkin sama ba; sai wanda ke aikata nufin Ubana.” Saboda haka, muna bukatar mu koyi nufin Allah kuma mu yi shi. Wannan ba abin wasa ba ne don Yesu ya ce waɗanda ba sa yin biyayya ga Allah suna “aikata mugunta.”—Matta 7:21-23.

4. Mene ne Yesu ya ce game da yin nufin Allah?

4 Yesu ya ce za mu fuskanci ƙalubale idan muna so mu yi nufin Allah. Ya ce: “Ku shiga ta matsatsiyar ƙofa: gama ƙofa da fāɗi take, hanya kuwa mai fāɗi, wadda ta nufa wajen hallaka, mutane da yawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙarama ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:13, 14) Matsatsiyar hanya ko kuma bauta ta gaskiya tana kai ga rai na har abada. Hanya mai fāɗi ko kuma bauta ta ƙarya tana kai ga mutuwa. Amma Jehobah ba ya son mutane su mutu. Shi ya sa ya ba kowa damar koyan gaskiya game da shi.—2 Bitrus 3:9.

YADDA YA DACE A BAUTA WA ALLAH

5. Ta yaya za mu gane masu bauta wa Allah yadda ya dace?

5 Yesu ya ce za mu iya gane waɗanda suke bauta ta gaskiya. Za mu iya yin hakan ne ta wurin bincika imaninsu da kuma ayyukansu. Ya ce: ‘Bisa ga ’ya’yansu za ku san su.’ Ya daɗa da cewa: “Kowane itacen kirki yakan fitar da ’ya’yan kirki.” (Matta 7:16, 17) Hakan ba ya nufin cewa bayin Allah ba sa laifi. Amma suna ƙoƙarin yin abin da ya dace. Bari mu ga abubuwan da za su taimaka mana mu gane yadda ya kamata mu bauta wa Allah.

6, 7. Me ya sa masu bauta ta gaskiya suke koyar da Littafi Mai Tsarki? Wane darasi ne misalin Yesu ya koya mana?

6 Ya kamata mu ɗauko koyarwarmu daga Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timotawus 3:16, 17) Manzo Bulus ya ce wa Kiristoci: “Sa’ad da kuka karɓi maganar jawabi daga gare mu, wato maganar Allah ke nan, kuka karɓe ta, ba kamar maganar mutane ba, amma, yadda take hakika, maganar Allah.” (1 Tasalonikawa 2:13) Masu bauta ta gaskiya suna koyar da Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki. Ba sa koyar da ra’ayoyin mutane, ko al’adu ko kuma wani abu.

7 Duk abin da Yesu ya koyar daga Littafi Mai Tsarki ne. (Karanta Yohanna 17:17.) Yana yawan ambata abin da Nassosi suka ce. (Matta 4:4, 7, 10) Masu bauta ta gaskiya ma suna bin misali Yesu ta wurin koyar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

8. Mene ne Yesu ya koya mana game da bauta wa Jehobah?

8 Ya kamata mu bauta wa Jehobah kaɗai. Zabura 83:18 ta ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Yesu ya so mutane su san Allah na gaskiya kuma ya koya musu sunan Allah. (Karanta Yohanna 17:6.) Yesu ya ce: “Ka yi sujada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta wa.” (Matta 4:10) Saboda haka, a matsayinmu na bayin Allah, muna bin misalin Yesu. Muna bauta wa Jehobah kaɗai, muna yin amfani da sunansa kuma muna koya wa wasu sunan da kuma abubuwan da Allah zai yi mana a nan gaba.

9, 10. Ta yaya za mu nuna ƙauna ga mutane?

9 Muna bukatar mu ƙaunaci mutane da gaske. Yesu ya koya wa bayinsa cewa su ƙaunaci mutane. (Karanta Yohanna 13:35.) Ya kamata mu ƙaunaci mutane kome launin fatarsu da al’adarsu da kuma wadatarsu. Ya kamata ƙaunar da muke wa juna ta sa mu kasance da haɗin kai. (Kolosiyawa 3:14) Saboda haka, ba ma zuwa yaƙi kuma ba ma kashe-kashe. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba.” Ya kuma daɗa da cewa: “Mu yi ƙaunar junanmu: ba kamar Kayinu wanda shi ke na Shaiɗan, ya kashe ɗan’uwansa” ba.—1 Yohanna 3:10-12; 4:20, 21.

10 Muna yin amfani da lokacinmu da ƙarfinmu da kuma dukiyarmu wajen taimaka da kuma ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Muna “aika nagarta zuwa ga dukan mutane.”—Galatiyawa 6:10.

11. Me ya sa muka yarda cewa ta wajen Yesu ne kaɗai za mu sami ceto?

11 Muna bukatar mu yi imani cewa ta wajen Yesu ne kaɗai za mu sami ceto. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu ceto ga waninsa: gama babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (Ayyukan Manzanni 4:12) A Babi na 5 na wannan littafin, mun koyi cewa Jehobah ya aiko da Yesu zuwa duniya don ya fanshi mutane masu biyayya. (Matta 20:28) Jehobah ya zaɓi Yesu ya yi sarauta bisa dukan duniya. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce wajibi ne mu yi biyayya ga Yesu idan muna son mu sami rai na har abada.—Karanta Yohanna 3:36.

12. Me ya sa ba ma saka hannu a siyasa?

12 Bai kamata mu saka hannu a siyasa ba. Yesu bai yi siyasa ba. Sa’ad da Yesu yake gaban sarkin ƙasar Roma, Bilatus, ya ce masa: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne.” (Karanta Yohanna 18:36.) Muna yin koyi da Yesu ta wajen goyon bayan Mulkin Allah da ke sama. Hakan ne ya sa ba ma saka hannu a siyasa ko da a wace ƙasa muke da zama. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce mu yi biyayya ga “ikon masu-mulki,” wato gwamnatoci. (Romawa 13:1) Muna yin biyayya ga dokokin ƙasar da muke. Amma idan dokokin gwamnati sun saɓa wa na Allah, muna yin koyi da manzannin Yesu waɗanda suka ce: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”—Ayyukan Manzanni 5:29, Littafi Mai Tsarki; Markus 12:17.

13. Wane irin wa’azi muke yi game da Mulkin Allah?

13 Mun yi imani cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai cire matsalolin duniya. Yesu ya ce za a yi wa’azin ‘wannan bishara ta mulki’ a dukan duniya. (Karanta Matta 24:14.) Babu gwamnatin ɗan Adam da zai iya cim ma abin da Mulkin Allah zai yi. (Zabura 146:3) Yesu ya koya mana cewa mu riƙa yin addu’a game da Mulkin Allah. Ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah zai halaka dukan gwamnatocin ’yan Adam kuma shi kaɗai “za ya tsaya har abada.”—Daniyel 2:44.

14. Su waye ne ka yi imani cewa suna bauta wa Allah a hanyar da ta dace?

14 Bayan ka yi nazarin waɗannan batutuwan, ka tambayi kanka: ‘Su waye ne suke yin amfani da Littafi Mai Tsarki a dukan koyarwarsu? Su waye ne suke koya wa mutane sunan Allah? Su waye ne suke nuna ƙauna ga junansu sosai kuma suka yi imani cewa Allah ya aiko da Yesu don ya cece mu? Su waye ne ba sa saka hannu a siyasa? Su waye ne suke yin wa’azi cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai cire matsalolinmu?’ Babu shakka, Shaidun Jehobah ne kaɗai.—Ishaya 43:10-12.

WANE MATAKI NE ZA KA ƊAUKA?

15. Me ya kamata mu yi idan muna so Allah ya amince da bautarmu?

15 Yana da kyau mu yi imani cewa Allah yana wanzuwa da gaske, amma ba shi ke nan ba. Me ya sa? Domin har aljanu ma sun yi imani cewa Allah yana wanzuwa, amma ba sa masa biyayya. (Yaƙub 2:19) Idan muna so Allah ya amince da bautarmu, dole ne mu yi imani cewa yana wanzuwa kuma mu bi umurninsa.

16. Me ya sa ya kamata mu nisanta kanmu daga addinin ƙarya?

16 Idan muna son Allah ya amince da bautarmu, dole ne mu nisanta kanmu daga addinin ƙarya. Annabi Ishaya ya ce: “Ku fita daga cikin tsakiyarta; ku tsarkaka.” (Ishaya 52:11; 2 Korintiyawa 6:17) Shi ya sa muke bukatar mu nisanta kanmu daga bauta ta ƙarya.

17, 18. Mece ce “Babila Babba,” kuma me ya sa ya kamata mu fita daga cikinta da gaggawa?

17 Mene ne addinin ƙarya? Addinin ƙarya duk wani addini ne da ke koya wa mutane su riƙa bauta wa Allah a hanyar da ta saɓa wa Kalmarsa. Littafi Mai Tsarki yana kiran dukan addinan ƙarya “Babila Babba.” (Ru’ya ta Yohanna 17:5) Me ya sa? Domin bayan da aka yi Ambaliyar Ruwa a zamanin Nuhu, addinan ƙarya da yawa sun taso a birnin Babila. Da sannu-sannu, sai waɗannan addinan suka yaɗu a dukan duniya. Alal misali, mutanen Babila suna bauta wa alloli uku cikin ɗaya. A yau ma, mutane da yawa suna koyar da cewa Allah uku ne cikin ɗaya. Amma Littafi Mai Tsarki ya koyar sarai cewa akwai Allah na gaskiya ɗaya tak, wato Jehobah kuma Yesu Ɗansa ne. (Yohanna 17:3) Mutanen da suke zama a Babila sun kuma gaskata cewa akwai wani abu a cikin jikin mutum da ke ci gaba da wanzuwa bayan mutuwa kuma wai wannan abin zai iya shan azaba a wuta. Amma hakan ƙarya ce.—Ka duba Ƙarin bayani na 14, 17 da 18.

18 Allah ya annabta cewa nan ba da daɗewa ba, zai halaka dukan addinan ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 18:8) Shin ka fahimci dalilin da ya sa ya kamata mu fita daga addinin ƙarya da gaggawa? Jehobah Allah yana son ka yi hakan kafin lokaci ya kure.—Ru’ya ta Yohanna 18:4.

Idan ka bauta wa Jehobah tare da bayinsa, za ka kasance cikin iyali na dukan duniya

19. Ta yaya Jehobah zai taimaka maka idan ka tsai da shawarar bauta masa?

19 Idan ka tsai da shawarar fita daga addinin ƙarya kuma ka bauta wa Jehobah, wasu cikin abokanka ko ’yan’uwanka za su iya yin fushi kuma su soma tsananta maka. Amma Jehobah ba zai yatsar da kai ba. Za ka kasance cikin miliyoyin mutanen da ke ƙaunar juna da gaske kuma suke kamar iyali guda. Ƙari ga haka, za ka kasance da begen yin rayuwa har abada a Aljanna da Allah ya yi alkawarinta. (Markus 10:28-30) Wasu cikin abokanka ko kuma ’yan’uwanka da suke tsananta maka za su iya soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki.

20. Me ya sa yake da kyau mu bauta wa Allah a hanyar da ta dace?

20 Nan ba da daɗewa ba, Allah zai cire dukan mugunta kuma Mulkinsa zai mamaye dukan duniya. (2 Bitrus 3:9, 13) Wannan lokacin zai yi daɗi sosai! Kowa zai bauta wa Jehobah yadda ya dace. Saboda haka, ya kamata ka ɗauki mataki yanzu don ka bauta wa Allah a hanyar da ta dace.